← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 39

Sashe 24

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nagode" A tak'aice

"Mesane kai kullum sedai ka zauna kayi shiru anan, bafa zasu hanamu yin magana da junaba, sedai idan mun keb'e inda ba kowane" kallon ta yae

"Yanzu ba magana muke ba?" Itama kallon sa tae

"Amma senayi magana so goma bazakamun biyu ba, bansaniba ko ina damun kane, nikuwa banida abokin hira anan sekai dole sedai kake kulani mukeyin hirar" D'age girarsa d'aya yae had'e da tab'e bakin sa

"Kinsan me?" Ya tambayeta cikin rashin walwala, cikin mutuwar jiki tace

"Seka fad'a"

"Banason surutu ne ni, ya kamata ki huta da magana kema sekace ba mace ba, kin dinga zabga surutu kenan cacacaca, ni banason hayaniya" harga Allah nataso ya ansata hakaba amma seta kalli rana taga lokacin sallan magrib yayi ma, wannan ya sanya kurin ta tashi batace masa komai ba ta nufi hanyar neman ruwan alwala.

***********
Har wannan lokacin sam ko kad'an Lawuri bata dawo hayyacinta ba, ba abinda ta tuna daya shafi raguwarta ta baya, mutanen data sani kuwa daga Abu sufyan se Ayusher se kuwa me kulawa da ita yanxu Asabe da Barbo data fahimci ita kad'ai kejin yare iri d'aya da nata, bata san ma'anar rayuwarta ba amma tasan shak'uwa da sufyan, batasan komai ba sedai tabbas tasan Sufyan sun shak'u da har bataso ta waiga bata ganshi ba, dukda basajin yaren juna amma suna fahimtar juna koda da idone, tarasa mesa duk sanda ta kalli fuskar sa setakejin wani al'amari game dashi kamar dacen tayi wata rayuwar data gagara tunano ko meye.......

So takeyi ta tambayeshi menene ke damunsa amma sam batasan ya zata saka hausar ba bakuma taso tayi masa da yaransu

"Mene?" Ta furta cikin hausarta wacce bata daidaita ba, murmushin yak'e yae cikin takaici yace

"Me kika ganine Lawuri?" Bata fahimci komai ba sedai ta masa murmushi itama ta girgiza masa kanta, hirar bazata iya tsawo ba haka dai suke jefowa juna kalamai kad'an kad'an ko wanne yana fahimtar yaren d'an uwansa tunda sunajin yaren juna kad'an, ta fahimci rashin zuwan Ayusher gunta inda har take masa k'orafi hak'uri ya bata akan zatazo ne.......

A hanyar sa na barin gidan yae karo da Aysher kawar da kanta tae tamkar bata ko ganshi ba, dan yanzu so take ta koyar da kanta fitar harkar sa kwata kwata, shan gabanta yae yana murmishi

"My Ayush ni kuma? Yau ni ake d'aukewa kai har haka, ni narasa fushin na meye wlhy, inzo gunki bazaki fitoba, in kira waya bazaki d'aga ba, haba mana my Ayush, pure heart d'inki ne fa" K'wallan dataketa k'ok'arin tarewa ne ya silalo mata ta sanya wani farin qyalle dake hannunta ta d'auke shi batare data tab'a makeup nata ba, ta kalleshi sosai

"Ka tab'a zuwa nan gidan dominni ne hala? Waccen bamaguzar kake zuwa gunta kuma naji labarin yayanka agarin nemanta ya b'ata, kai kuma kasan inda take sabida tsabar sonkai irin naka ka barshi ya komawa hallaka yanzu ni meya saura dazaka gayamun? Ka cutar da jininka ma bare ni, duk sona dakai ina tsananin k'yamatar halayenka Yaa Sufyan sabida haka dan Allah nika hassaramun inaso zam sarara, zuciyata dai tawace zan rarrashi abuta" Ta qare maganar lokaci d'aya tana k'ok'arin bud'e motarta ta shige, mamakin ta sosai ya hanashi koda motsi mesashi bame tausayin halin dashi yake cikine wai? Tayaya ze dakatar da Hurairah tunda seda ya yafi tukunna ma ya sani, sumar kansa ya shafa sannan ya taka a hamkali zuwa gun motarsa tare da furzar da iska me zafin gaske daga bakinsa..

***********
Tunda wannan abun ya faru Zuhrah bata k'ara yiwa Abu Hurairah koda gaisuwa ba, kusan kwanaki 4 yanzu ko inda yake bata zama, idan yazo inda suke ma tashi takeyi, dayasan ko ita wacece dabe wulaqantata ba, dan kawai ta nemi ya taimaketa seya mata izgilanci, tundama cen ita ba mace bace me d'aukar wulak'anci akan maza, tasan darajar kanta sosai dan Allah ya qaddare da zama nan bashi ze bata damar zubar da qimar taba.

Abun kuma seya dami Hurairah, yaudai da kanshi yaje gunta amma ko kallonsa batayi ba harya zauna

"Musulunci dai ya hana gaba ko?" Batako kalle saba ya qara cewa

"Assalamu Alaikum" shareshi tae

"Amincin Allah ya tabbata agareki ya bint" waigowa tae suka kalli juna cikin takaici ta amsa

"Amin wa Alaikassalam"

"Nazone yau mui maganar mafita, yau da dare nakeso mu tsere amma ke me kika gani, naga ke kinsan hanyoyin da suke bi, naga kuma suna shan burkutu duk dare kuma ni sun dena d'aure ni yanzu" kallon sa yanzu kam tae sosai

"Idan kuma suka kama mufa? Kasan hukuncin wanda ya gudu da mace anan gun?" Kallonta yake shima ido cikin ya girgiza mata kai alamr aa, taci gaba

"Kashesa akeyi idan an kamashi, ni kuma bnso maka mutuwa yanzu ba" haka dai ya kafe akan se sun tafi dole ta amince masa, cikin dare kuwa suka had'e inda yace suka nemi sulalewa....

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

*Book nawa na siyar wane, please karkui sharing wasu groups kuma karki karantamun idan baki biyaba,meso ya siya ya nemi wannan lambar 07084161619*

22

Tafiya me nisan gaske sukai dan kuwa basu suka sararawa tafiya ba se kusan asuba, seda sukai sallah sannan suka kalli juna, zuhrah tace

"Nagaji wlhi" cikin hasken dabe gama wadata gun ba ya furta

"Aikuma baki isaba Zuhra, yaya zakice
Kin gaji, karaya da wuri haka?" B'ata fuska tayi

"Ni gudun damukene ya ishen, bakaga ba har bayana ya soma mun ciwo" murmushin takaici yae

"Mutanen cen fa kinsan sunsan kan jejin, zama su fimun sanin shortcut daze iya had'asu damu batare da wani b'ata lokaci ba, bama wannan ba aiba su kad'ai bane mutanen wannan jejin macuta akwai dubun dubatar su miliyoyinsu ma suna nan, bamuda wani makami se adu'a idan zaki tashi muje ki tashi muje" mik'ewa tae cikin takaici da gasken ta gaji, istigfari yae Allah yaga zuciyar sa sannan ya damk'o hannunta suka soma gudu baji ba gani.

************
Abu sufyan kuwa duk wata damuwa damuke tsammanin yana cikinta tawuce hakan ma, sabida kwata kwata mom batada lafiya gashi bata kulashi akan ya bata kunya ya cutar da d'an uwansa, yauma kamar kullum durk'ushe yake agabanta yana xubar hawaye

"Mom dan Allah kiyi hak'uri ki tallafeni ki gafartamun, wlhy sharin shaid'anne" kawar da kanta tae daga dubanshi, tana fushi dashine kurun amma dukkanin laifin general ta d'audawa shi kacokam, sabida koba komai shine ya kafe akan yin tafiyar tun farko, dabe tura subin wannan doguwar hanyar ba dababu abinda ze rarraba kan yaranta har haka, seda ta share k'walla sannan tace

"Zan hak'ura amma da sharad'i" Da sauri yace

"Na amince mom, duk girman sharad'in dazaki gindayamun zan jura zan d'auka inshaa Allah namiki alqawarin komai girman sharad'in zanbi shi batare da wani tunani ba" Gyaran kwanciyar ta tae

"Ka tabbatar nanda kwana biyu yarinyar nan ka d'aurata akan wannan k'auyen na fulanin garin dakuka b'ulla bayan da kuka baro muguwar hanyar nan, akwai garada da OGA shamsu yae sun rakasu ka basu kud'i Maira dubu d'ari biyar su d'auki yarinyr nan da kuyangarta su kaisu garinsu, ka kuma manta da ita har abada wannan shine sharad'in nawa, sabida Abu Hurairah bamuda tabbacin qara sanyashi a idanmu har abada" Jikinsa har rawa yakeyi tsabar firgici yana cikin tsananin rud'u da tashin hankali, har ya mik'e ya qara durk'ushewa

"Mom Dan Allah ki duba lam......"

"Wlhy kaji na rantse ka sanya wannan yarinyar akan hanya tayi garinsu nanda gobe ma na dawo sa abun baya" Yama rasa meyake masa dad'i haka ya kasa ya tsare ta da ido cikin rud'ani bashida bakin magana haka yabar d'akin jikin sa babu k'wari ko kad'an.....

Kallonta yakeyi bayako k'iftawa harta tsargu da kallon dayake mata, cikin bak'in ciki da takaici yace

"Lawuri zan sanyakai a hanya ki koma gida badan raina yana buk'ata koson hakan ba sedan yin biyayya wa mahaifiyata nasani ba dole bane ki fahimci yarena amma ko ba yanzu ki sani kina raina har abada ina miki sonso bana wasa ba banida wani zab'in dai daya wuce in hak'ura in barki ki tafi" bata gane sosai ba amma ta fahimci maganar ya shafi shi da ita kuma maganar tafiya yake mata, kuka ta saka dan batasan mekenan yake nufi ba, ya hau aikin rarrashi, washe gari tunda safe yazo gidan kai tsaye Ayusher ya nema ba musu tazo suka gaisa yace

"Zanyi tafiyane, zanje OGUN STATE" kallon mamaki tae masa ganin sam baya walwala

"Wurin me kuma Yaa Sufyan?" Ta tambayeshi cikin kulawa

"Lawuri zan sanya a hanyar garinsu, kuma daga OGUN STATE D'in ake dauke hanya zuwa garin, ga tafiyar da nisan gaske ina barar adu'ar ki" Sadda kanta tae a qasa cikin tausayin sa

"Mesa zaka mayar da ita?" Kawar da kanshi yae daga dubanta

"Hakan shine daidai dear, so karki damu fatana kimun adu'a kinsan yanda hanyar nan take" jinjina kanta tae

"Allah ya tsare hanya ya kaika lfiya yakuma dawo dakai lafiya" godiya yae mata sannan ya shiga se mamaki Lawuri keyi ya gama tattare musu kayansu yace su fito, haka suka kama hanya bata fahimtar komai sabida batare kai, se Barbi ce me gane inda aka dosa....

**********
Tunda mutanen songai suka gano guduwa sukai se suka shiga nemansu, koda suka fahimci hanyar dasukabi bame b'ullewa bace sesuka dawo suna
Dariya sun tabbatar bazasu yau ba sesun juyo dan kuwa akwai makasansu a hanyar bila'adadin, idan ma sun samu sun dawo kenan kafin a kashesu acen ba.

Kallon tausayi ya sake mata sanda suka iso hanyar data rabu kashi uku abun mamaki acikin jejin nan

"Zuhrah menene?" Duqar da kanta tae

"Yunwa nakeji" Ta bashi amsa a tak'aice, shida kanshi daurewa yake amma yunwa yakeji
Chapter 24 · 0% Book details