← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 39

Sashe 12

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sosai kau, sabida ai sunsan a wannan ranar kad'ai mota ke wucewa se kuma bayan sati biyu irin ranar, kuma kayan abunci suke karb'ewa sedai kuma sukan tafi da motar ne, wani zubin ma sekaga sun ajiye motar abakin titin nanda en kwanaki, kuma idan akai gaddama sukanyi harbi gaskia" Shiru General yae kanshi ya k'ulle, duk abinda ya faru da yaran nan laifin sane, besan mesa ya kafe akan sesunyi tafiyar nan ba, mahaifiyar suma tace hankalinta be kwanta da tafiyar ba, shi har yanzu mamakin kanshi yake wlhy, yanda ya dage yanzu wa gari ya waya?

"Amm yanzu mintuna nawa zasu kaimu cikin garin?" Kallonsa yae

"Ai munzo, mintuna ashirin zuwa ashirin da biyar sun wadatar, an kusa zuwa cikin garin ai" bece komai ba ya koma mota sukai d'auki hanyar cikin garin, bayan da duka isa yace da General

"Yanzu tashar mu zamuje semuji meya faru awurin direban" jinjina ka shi yae yana mamakin yanda gabaki d'aya kanshi ya dena aiki, har suka k'arisa bece komai ba.

Sunyi sa'ar ganin direban kuwa inda suke basu labarin meya faru, har abinda ya faru da en bunnin nan, hankalin General ya tashi matuk'a dajin wannan zancen

"Yanzu wane asibitin sukaje?" Rike baki Direban ya

"Sunce su bak'ine basu tab'a zuwa nan garin ba, nima kuma ban tab'a sanin wani asibiti ba anan, amma dai gabas sukayi danko kud'in dazasu hau adaidaita basuda shi" Godiya General ya musu sannan ya nemi gidan soji na nan garin ya karb'i mota da direban su, kana ya soma yawon asibito cin garin kaf neman yaranshi.

***********
"Koyaya naso nai tunani sena gagarayi, zuciyata tana mun tserereniya akan abinda ze faru ga d'an uwana Dawood, ina cikin tashin hankali mara misaltuwa bansan waze taimakemu ba, asibitin nan basuda imani suna ganin mutum helpless su taikeshi bashi bane a ransu se zancen kud'i?" Kallonshi Dawood yae cikin damuwa yace

"Ga bamuda waya, gabansan number kowa aka ba" cikin zaquwa yace

"Nasan number mom aka, muje gun kiran waya na kud'i kokuma ma mu ari wayar likita anan ko wani staff"

"Hakan yayi muje" hakan sukaje suka samu wata mace a reception suka ari wayanta suka kira mom, haka sukayi ta kiranta a waya bata d'agawa har kusan so ba adadi, cikeda damuwa ya wurgawa dawood idanshi

"Bata d'auka ba wlhy" ya fad'a cikeda damuwa

"Ita kad'aice number dakake da itane?" Shiru yae nad'an lokaci kanyace

"Se Number Ayusher, barin gwada neman ta muji" kiranta yae ringin biyu ta d'aga kuwa, cikin muryanta me dad'i tace

"Hello" guntun tsaki yaja

"Badai zaki dena ba kenan ko?" Tashi zaune tayi cikin mamaki

"Father sword da gaske kaine, where have you been? Hav bn trying ur number all this while but its not going through" dafa goshin sa yae cikin qosawa da zancen nata yace

"Ayusher saurareni mana" shiru tae dan tasan seya datse kiran yanzu

"Ina cikin problem and bayaga number mommy banida number kowa aka bayan naki, so zanje wurin first mony agent zan qara kiranki a waya, u transfer 150k in to their acc inyaso sesu taimaka su bani cash" Nisawa tae

"Meya faru dakai hakane Farher sword?" Haushinta ya somaji

"Look Ayusher banida time na dogon bayani, just do as i say, u makesure that kin ajiye wayanki a kusa dake, zn kiraki da wani layin daba wannan ba yanzun nan ba jimawa, sena tura miki acc details d'in" murmushi tae

"Alright Pure hrt bye" ta kashe wayan, neman gun first money agent sukai, sunsh fama dasu kafin su yarda, sabida acewar su sedai ka bada kud'i a tura ma waninka, koka basu ATM su cira da kansu su baka, da qyar gashi weekends ne suka yarda da wannan shawarar, suka taimaka yashirata ta turo mai kud'in aka bashi sannan suka koma asibiti.

************
Alhamdulillah anyi masa aiki an cire bullet d'in lokaci bullet ne ma, na irin bundigar nan ta farauta, alamun dai qauyawa ne, aka saku damar gayar k'afar kuma anyi sa'a da aikin dan kuwa zuwa dare harya farfad'o, shi kuwa General beyi tsammanin zasuce asibiti ta garin babba ba, sedabya gama karad'e asbitocin garin kaf da clinics be samesu ba sannan ya nemi makwanci badan yaso ba, se washe gari ya soma neman Su a teaching hospital ta garin.

Besha wahala ba gun gano har d'akin dasuke, koda Abu sufyan ya ganshi a d'akin kasa koda k'wak'waran motsi yae ya k'ura masa na mujiya kawai yana kallon sa!, a hankali ya taka gun gadon na Abu huraira ya kalleshi yana bacci tausayin yaron ya sanyashi kuka, gashi kuma duk Abu sufyan yafita hayyacin sa, banda wahala babu abinda kake hangowa a fuskokin su, seda Abu Sufyan ya rungumeshi suka sha kukansu kafin su zauna baiwa juna labarin abinda ya faru, shirin tafiya gida yae musu ba b'ata lokaci sabida mahaifiyar su dake cikin halin ciwo ba qaqqautawa.

*Ban saniba ko iyakar tsawon hanyar kenan, ban saniba ko sun gama shan wahalar rayuwa kokuma da saura, bana tunanin nasan mezai faru agaba, abu d'aya na sani shine yanxu aka soma wasan, wasan na manya ne, wasan me wahala ne, dani daku semun daurewa bin Doguwar hanyar nan atare kozamu samu madafar b'ullewa*

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

*Littafina na siyarwa ne, idan kanso ka biya ka karanta idan ka tsinta a waje ka karanta baka biyaba kaida Allah... Me buqatar siya ya nemeni ta wannan number .
07084161619.

      11

"Menene yanzu yake damunta?" General ya wurgawa Cyama wannan tambayar acikin waya

"Batacin abinci jininnkuma har yanxu be sauka ba inji Dr." Nisawa yae yace

"Kibata wayar tam zan mata magana ne" mik'a mata tae tace

"Mom, dad ne ze miki magana" karb'a tae ta kara a kunnen ta

"Adaman General ya jikin ki?" Murmushi tae jin abinda yace

"Naji sauk'i Daddyn Twins" ta fad'a tana me k'ok'arin nuna masa bata cikin wani ciwo

"Na samo miki yaranki, ki gayawa jinin nan ya sauka da sauri, ga Abu sufyan ma ze miki magana" Da sauri ta tashi zaune tana dafe kanta

"Da gaske kake?"  Amaimakon taji muryan General setaji muryan Abu sufyan

"Mom sannu da jiki ya jikinki?" Mayar da numfarfashi tasomayi sauri da sauri kantace cikeda farin ciki

"Sannu Sufyan, ina kuka shiga haka kuka nemi d'agamun hankali mahaifiyar Dawood ma tashiga damuwa me tsanani" murmushi yae

"Mom ki kula da kanki kawai da lafiyanki mufa muna nan lafiya lau, wayoyin mune kurun aka sace mana duka, amma dukanmu muna cikin qoshin lafiyax harma tare da dad zamu dawo, please kiji sauqi kinji?" Ya k'arashe maganar cikin shagwab'a, tabbas ko wannan halin ya isa ya nuna cewan Abu sufyan d'intane, murna awurinta ba'a magana haka sukaita hira daga bisani sukai sallama bayan ya sanar mata Hurairah yana wanka gudun karta gano bashida lafiyane.

***********
   Shirinsa tsaf yae shida Dad da dawood sannan aka kwashesu zuwa airport dan da jirgi zasu koma abuja, tafiyar dabata wuce 40 mns ba ta sadasu da Abujan, Rahama wacce basu tab'a shiga acikintaba suka tsinc8 kansu aciki ganinsu a babban birnin tarayya, da wheelchair aka d'auki Abu Huraira, su Lawuri se zare ido suke, dama haka duniyar take da ababen kallo iri iri, kalli motoci kaman ba gobe dama haka rayuwar take suke cikin mugun jejin cen basu masan abinda ake ciki ba, kodai wai mafarki ne takeyi? Kokuma shin aa Aljanaine suka sato ta? Tama rasa me zatai tunani akai a haka har aka umarcesu da shiga motar suka d'unguma dukkansu zuwa gida.

************

     Abu Huraira kam asibiti aka wuce dashi inda suka k'ara duba k'afar alhamdulillah aiki yayi kyau, sedai fatan samun lafiya, Abu sufyan kuwa shida sauran dukansu gida suka wuce, kai tsaye d'akin su ya wuce ya shiga toilet yafi 2 hours yana dirxar jikinsa, yasha mamakin yanda gashi ya masa yawa sekace wanda ya shekara baya cikin al'umma, koda gake ba abin mamaki bane tunda yaga yanda gaba d'aya Abu Huraira yazama sekace wani tsohon zaki jikinsa duk gashi, bashida nutsuwar daze wani b'ata lokacin gun kwalliya dukda haka  ya shirya tsafi acikin k'ananun kayan sa shirt blue da wando fari qal, hannunsa ya wurgawa kallo bemasan dunuyar da agogon sa ya shiga ba kuma dashine ake ganeshi, zoben dai yana nan, murmushi yae ya fito daga d'akin nasa bayan ya feshe jikinsa da turaruka masu tashin k'amshi me sanyi da sanyaya zuciya.

A k'asa yaci karo da Hanifer bayan daya sakko, zuwa tae tana masa murmushi yabkalleta cikeda kulawa

"Hanny Baby, kina lafiya?"

"Ka rikitar dani yaa Sufyan nasan kaine ma, gashinan kanamun wannan kallon" murmushi yae

"Naji nine ya akayi?"

"Duk ka canja fa, kwata kwata kaman ba kaiba" gemun daya masa tsawo ya shafa yana murmushi bece komai ba

"Yaa Huraira fa?"

Kallonta yake har yanzu

"Huraira zazzab'i yake yana asibiti ma, daga zaran nayi aski gunshi zanje, ku da dare sekuje yanzu wannan bak'in ki nuna musu sui wanka ki basu abinci da lemo me sanyi sannan ki wadata su da suturu wannan kayan jikinsu ai destroying nasu ki baiwa gate man ya qonasu" Jikinta duk yae sanyi

"Yaa Sufan kace ina gayar da yaya huraira plss" Ta qarashe maganar wane zatai kuka jinjina kanshi yae ya juya kawai.

Kai tsaye shagon aski yaje yae askin san sannan ya wuce gun mom, murna awurinta ba'a ma magana, bayan sun gama gaisawa take tambayar sa Huraira yace ciki zolaya

"Lallai mom inaji dake, toba zagwad'in ganinki ya sanya gaba d'aya na manta ban sanar dake ba, kinsa halin Brother zazzab'i ya kamashi fa yanzu haka yana kwance agidan amma yace a gaisheki, idan naje gida zan kira kui magana danki tabbatar yana lafiya, yamaso yazo nace kasan Mom bazataji dad'i ba idan har ta ganka kana layi kuma kazo dubata" Murmushi tae

"Allah ya bashi lafiya, waime ya faru dakune Kyautar Allah nashiga damuwa fiyeda tunaninka, sekuma naganka fes fes amma karame sosai fa" kallon ta yae cikin murmushi
Chapter 12 · 0% Book details