← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 39

Sashe 36

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***********
Bacci b'arawo shine yae awon gaba da Huraira a wannan daren, bashi ya farkaba se asuba cikin tsanani firgici da rud'un mafarkin da yae, da ambaton Allah ya farka yae saurin kai dubansa zuwaga d'an uwansa da har lokacin yake unconcious, da sauri ya kunna fitilar d'akin ya nufi gadon, ga mamakinsa mafarkin dai dayayi shine, gashi yana kallo jini yana malala daga bakin d'an uwan sa wai wani bak'in halittane yazo ya kwashe masa 'ya'yan hanji shine yaketa zubar da jini, rungumarsa yae cikin tausayi

"Nashiga uku sufyan meya sameka haka?" Bazeko iya magana ba, haka ya dinga kwarara aman jini, ba shiri Abu hurairah yaje kiran likita bayan ya tashi Dawood daga kwanciyar da yake ta bacci......

Iya bincike anyi amma babu komai a tattare dashi daya shafi dalilin aman jinin, hankula sun tashi ainun har yanzu be farfad'o ba amma jinin yanzu abun ma ya k'ara yawa ta hanci data baki, ga yanka a cinya ga buguwa da yae kai komai ma damun sufyan yake gwanin tausayi.......

"Yaya Huraira ni dama nacene ko zaku gwada yin masa adu'a ne asanya malamai daku kanku kukeyi, al'amarin nan yafi k'arfin accident gaskia, ya dace kusan me ake ciki" kallonta yae cikin damuwa

"Zan gayawa Dad inji mezece, Zuhrah nimafa banida lafiya wlhy tsaye kurin nake" kallon sa tae kafin tae magana ya soma tari, da gudu ya wuce toilet jikinsa har b'ari yake haka ya dinga kwarara aman jini bako k'akk'autawa, hankalinta ya mugun tashi ganin hakan

"Nashiga uku Al-hassan kaima irin na d'an uwanka kakeyi, mekenan yake shirin faruwa da rayuwar ku haka? Innalillahi wa inna ilahiraji'un" se kuka take wiwi ganin aman yak'i tsayawa ta juya da gudu tana k'wallahwa hanifer kira, tare suka dawo d'akin zuwa ban d'akin, yafi 10mns kafin abun ya tsagaita, kallon sa sukeyi dukkansu cikin tausayi se kuka sukeyi

"Yaa Hurairah muje asibiti dan Allah" hanifer tace bayan sun tayashi gyaran jikinsa ya dawo d'akin kan gado

"Base munje ko inaba hanny, karki damu kusan kwanaki 5 inayi ai, idan kuma ya dena shikena ai" waro idanta tae waje

"Kwanaki 5 yaa Hurairah ban saniba, mekenan kake shirin aikatawa rayuwar ka, menene matsalar ka wai?" zuhra ta furta tana ta kuka, sunyi sunyi ya kafe akan bazashi asibiti ba, ganin haka ya sanya hanifer ta kira Dad a waya take sanar masa.

Lawuri dai malam ya ciwo kanta ta hanyar mata adu'a da kuma sanya karatun alk'urani agaba, koma menene yasan mugun abu ake turo mata tunda ta musulunta, yanzu sunan ta Naja'atu sunan da ita da kanta ta zab'a abunta dan kanta, sedai har yau takanyi borin nan tamkar wata zautacciya.
********
*Bayan sati uku*

Dukda Abu sufyan ya farfad'o hakan baze hanashi yin aman ba, likitoci da kansu sun tabbatar wa mahaifinsu basuda wata matsala b'angaren lafiyar su daze sanya su dinga wannan uban aman jinin, sabida ko pcv nasu duk sanda za'ayi toko ze nuna kusan 40% ne koma fi, dukkkaninsu sunyi fari run rame sunyi wani fayau, yanzu abinda yafi komai ban tsoro shine yanda sumar kansu da girar idansu dana saman kai harma da gashin gabansu ke komawa fari kamar na tsofaffi kuma ayau an tashi da tashin hankakin gashin yana cirewa da kanshi...... Matsalar datafi kowacce tashin hankalin iyayen su itace wacce basa magana sam, sedai yake bak'i ya tafi, mom kam ta dakatar da ciwon ta ta dawo gunsu susu biyu tana jinya.

Zuhrah tana zaune ta k'urawa Abu Huraira ido banda kuka babu abinda takeyi, lokaci zuwa lokaci takan share k'wallan dake malalo mata cikin bak'in cikin ganin yanda mijinta ya koma, hannunta taji ya rik'o ta mayar da dubanta zuwaga hannunsu dake tsark'e kafin ta kuma kallon sa, murmushi ya sakar mata yana girgiza mata kansa alamar ta dena kuka hakanan, wani yawu me d'acin gaske ta had'iya kafin cikin tausayi tace

"Yaa Huraira yanzu naga baka magana, abincin nan baka iya ci, baka iya tashi fa, bansan meya same kaba, na sanar dasu abin nan iskane, amma basu kulani ba" Sauke k'wayar idanshi yae a k'asa shiya tabbatar cewar mutuwa zeyi bashida sauran shan ruwa agaba, yana so ya rayu da yaranshi, yanaso ya rayu da matarshi yana son zuhra, dukda a k'ark'ashin zuciyar sa yana son Lawuri har gobe amma shikam bayaso ya rayu babu zuhran sa, so yakeyi ya bata hak'uri ya rarrasheta soma yakeyi ya rungumeta ya bata baki amma besan meke hanashi yunk'urawa ba, gashi kuma babu abinda yake masa ciwo yarasa gane kan shi shi kanshi..... Ganin haka ya sanya kukanta ya tsananta shi kuwa se matse hannunta yake yana nodding kanshi alamun ta dena dan Allah amma ina kukan yaci k'arfinta sosai....

***********
Abu sufyan ma hakan take a gunshi domin kullum Ayusher sedai ta tasashi agaba tana kuka, dad yaukam abubuwan sunfin komai rikice masa musamman da akace tun daren jiya Abu Sufyan yake faman aman ba k'akk'autawa... Abu sufyan yana matuk'ar mamakin yanda sam baya iya adu'a ga abun aranshi amma baya iyayi, sedai ya dinga zuba gurnani yana ihu aduk sanda yake bacci domin kuwa har bayason wani abu me kamada bacci a yaud'eshi ya dinga mugayen mafarkai kenan kaman babu gobe....

Gado kusa da juna aka ajiye dukkansu sedai su kalli juna babu bakin magana maganar wannan matsalar tasu kuwa tagama zaga duniya kaf!!! Kowa da abinda yake cewa yana damunsu, mom ganin surukanta mata sunata kuka ya sanya itama tashiga yin nata, sabida yau jikin yafi ko yaushe rikicewa

"Seda na rok'i mahaifin yaran nan akan ya barmun yarana ya dage ya turasu wannan *Doguwar hanyar* yanzu gashi sanadin ratsa wannan jejin komai ya dagule mana, sanadin bin Doguwar hanya be amfanemu da komai ba yanzu ma kafiya irin nashi nace abin nan na addini ne akomawa malamai islama yaqi ya yarda jifa ne, ina kallo kenan yarana zasu mutu kalli yanda duk suka dawo, susu kad'ai suka san me sukeji,surukan nata duka rungumeta sukai sunata zuba uban gunjin kuka babu k'ak'autawa........gurnani sukajiyo daya sanyasu nausar dukkansu da sauri, tarar wa sukai dukansu ciwon ya tashi sun had'e hannayensu gu d'aya sunata gurnani da aman jinin yau hadda sare jinin me uban yawa, iyakar tashin hankalin sun shigeshi ko wannen su yanaso yae adu'a amma babu baki a zuci ma sunaso suyi amma sun gagara tunano komai acikin adu'a....

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:02 PM] Maamah twins💕❤: 35*** "Duk abinda kace ayi shi akayi, sedai ga hoto nan bata juyo ba, wani abu suke fad'a da bakinsu dan baji nake ba amma gasunan kallesu a ruwa, narasa menene a hannunta kullum shine yake hana mata zuwa kwata kwata....yanzu haka abunda muka mata na duk wanda ya kalli cikin idanta ya soma santa ya karye nayi nayi yak'i yaje, daso nayi wannan dasukaxo suka saceta su kashe juna ma akan soyayyarta, d'ayan har janyoshi nayi ya kamo hanya bansan meya hanashi k'arasowa ba, wani abu suke ambata dayake yawan k'onamun tsafi na" kallon sa K'uru da k'uruwa keyi kaman zasuyi kuka suce wayyo Allah

"Amma ai ya kamata kasan menene suke cewa, yanzu ace anan nahiyar akwai abinda ze gagari tsafin ka?" Shu'umun murmushi yae
"Ada babu amma yanzu akwai!!!! An samu a wata duniyar da damu bamusan dashiba me burgewa kalli yanzu suke rayuwa ma, dolene sena hallak'ar da yaran nan biyu saura musu kwana uku duk aljanan jikinsu su gama cinye musu hanji su gama tsiyayar musu da jini inyaso duk su mutu!!" Murnushin mugunta k'uru yae

"To Lawuri fa zata dawo?"

"Zata dawo dole ma, tunda farko kaine ka turata baka gayamun ba ai" cikin takaici ya kalleshi

"Ainasan kanada k'arfin ikon dawo da ita koda ta mutune, sabida haka nace taje danaga ta damu yanzu kuma suka dawo da ita, kuma ka kafeta anan bata sha'awar k'ara zuwa wani wurin su kuma a kashesu dukansu uku har wannan dasuke cewa Dawood" Wak'a da hauka ya somayi take hoton dawood ya bayyana yana zaune yana shan tea a hannun shi, wata k'ara ya k'walla ya nunashi da bindin dokin dake hannunshi yae wasu hauka sekuma ya kalli k'uru

"Su mutu a rana d'aya?" Da sauri k'uru ya d'aga kanshi alamar e, wani shirme ya somayi take agun Dawood ya soma tari tamkar tea d'in ya sark'eshi daga haka se aman jini bako k'akk'autawa, momyn sa dake zaune kusa dashi tana shan tea a take ta rik'eshi ta soma tambayar sa menene, ganin abun ya wuce wuri ya sanya ta soma kiran k'anwar sa, da gudu tazo, alk'ur'ani me girma ta d'akko ta soma karatun sa da k'arfij sauti, bata gushe agunba seda ta tabbatar ya dena, duk wannan abun dasukeyi Boka dasu k'uru suna kallonsu acikin k'warya, ihu suka k'walla ganin k'waryar ta boka ta koma koriya shar, wannan abu shine na farko daya faru a garin tun bayan samuwar mafarin al'ummar su, haka ya dinga gunji cikin k'araji da surutai bako k'akk'autawa bashiba hatta su k'uru sun rud'e da wannan al'ajabin.

*******
Babu shakka su twins suna cikin tashin hankali, abun ya soma wuce tunanin general ido ya k'ura musu yana tunanin mafita yanzu kam, sabida ba shakka akwai damuwa a wannan hatkar duba da yanayin su a wannan lokacin idanuwan su sun kad'a sunyi jajir tamkar an zuba musu jini ajiki ga fatar jikinsu ta soma tamurewa tanayin fari sekace wanda ya shekara be sgafa mai ba a lokacin da ake kwarara uban sanyi!!!!

Wayar sa ya zaro ya kira malam, bayan sun gaisa yake snar masa yazo asibiti, shisam yama manta da wata Lawuri ya kula kamr wannan damuwar da yae da ita soyayyace yanzu kuwa ya dena ji mezai damesa?.

Koda malam yazo yashiga rud'u sosai, umarni ya bayar akan a mayar dasu gidansa, wannan abun koba menene iskane kuma a haka yakeso ya kashe su, da wannan shi kanshi malamin seda ya kira mahaifin sa sabida yana ganin abun yafi k'arfin sa.......

Dawood kuwa sedaga baya abun ya k'ara tashi masa, inda atake mommynsa ta tuna da zancen su Twins,kai tsaye mom twins ta kira suka tabbtr mata ga inda aka wuce dasu, ita kanta alfarma ta nema na wucewa da Dawood shima a tallafeta a dubashi san gaskia baida lafiya.
Chapter 36 · 0% Book details