← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 39

Sashe 26

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kuma inbanda zurfin ciki irin na Adda labour bata fa taba fadar irin zaman da sukeyi ba bare tafadi cewar yana dukanta..." Hindu tafada tana kokarin zama agefen gadon,

"Ni dama tun jimawa wallahi na fuskanci akwai matsala kugafa irin ramar da tayi har iyallo ke cewa ciki ne..." Meenah itama dake tsaye kusa da amma ta tofa nata,

"Ai Dr yace babu wani ciki yanzu... Yace bata da komai, gara ma da Allah bai bata ba domin hada zuri'a da irinsu wannan hamood din hatsarine... Allah yabata masu albarka nan gaba" maama tafada tana kokarin mayar da kwallar da take kokarin cikowa idanunta, ammah dai har akayi aka gama bata tofa tata ba suna nan zaune sunata yimata sannu har Abba yazo yadubata yatafi hakama mazajensu duk sunzo sun dubata, khulsum amarya itama daren ranar sai gata, kowa yaga bilkisu sai yaji tausayinta sakamakon kumburar da fuskarta tayi tsabar duka. Lokacin da dare yayi meenah ce tace zata kwana da ita amma ammah tace a'a kowa yatafi gidansa inyaso Rabi mai aikinta sai tazauna su kwana tare hakan kuwa akayi, ita dai bilkisu kasa baccinma tayi sakamakon suyar da zuciyarta keyi motsi kadan zata furta,

"Allah ya isa..." Acikin zuciyarta kokuma afili. Saida tayi kwana uku agadon asibiti sannan tafara tashi har ta zauna kuma an danyi sa'a kumburin fuskar tata ya dan ragu, har ranar babu wanda yayi mata maganar hamood may be suna son abar asibitinne tukunna sai asanar mata abinda yafaru, aranar tana zaune maama na kusa da ita agefen gadon tana bare mata ayaba tana ci sai ga hajiya iyallo ita da yakumbo mai gado, tunda iyallo tashiga dakin take tsinewa hamood,

"Ni dama wallahi wannan yaron ban yarda dashiba... Yaro sai kace dan dambe wani murgujeje dashi... Wallahi tsohon mijinki shine miji mai gado... Yaro mai kunya ko gaisheka yakeyi idanuwansa akasa bazai taba yarda ya hada ido dakaiba amma shi wannan idonsa atsakar ka yake sai yasaka idonsa cikin naka sannan zaiyi maka magana....Allah yasawwake,Allah ya kwashe masa albarka macuci"

Tun abun na bawa su maama haushi har yadawo yana sakasu dariya, iyallo nata faman hamuki ya mudan yashigo wanda dama shine yakawo su,yana yiwa bilkisu yajiki iyallo tahau cewa,

"Ai shikenan yanzu sai acika min burina ayi hadin nan.. Ni dama tun farko mudansiru naso abawa aka ki..."

"Dan Allah iyallo mu ki kyalemu muji da abinda muke ji..." Maama tafada tana hararar gefe,

"To fitsararriya dadinta ma dai bake naceba balle kiyimin rashin arziki... Fitsararriya kawai.."

Shi dai ya mudan ficewa yayi daga dakin da alama shima baiji dadin maganar iyallo ba ko meye dalili? Bilkisu kuwa jin iyallo ta ambaci fahad har tana yabonsa yasata dulmiya kogin tunani.....

*Wannan littafin na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

23

"Oga munshiga uku mun kawo kanmu gidan aljanai" kanma ya rufe baki dukansu sun runtuma aguje bako waiwaye, anan suka bar bindigogin su dama jakar kud'in baki d'aya, Suna nan a lab'e kan bishiyar su kuwa har sa'o'i biyu suka shud'e kana suka sakko, Abu Huraira ya bud'e jakar yaga kud'i me tarin yawa gashi bashida wurin zubasu bayaso ya d'auki jakar dukanta amma yasan kud'in zasu masa amfani nan gaba kad'an dan a wannan hanyar besan ina zasu fad'a ba shikam, ba wata suturar kirki ajikin sa, fatane kurun a kunkurunsa ita kanta Zuhra fatar ce a kunkurinta se a k'irjinta

"So kake ka d'auki kud'inne?" Kallonta yae had'e da sauke ajiyar zuciya

"Banaso na d'auke musu kud'in duka, so nake mu d'eba kud'in koda munje inda semun hau mota da kuma abinci, hanyar dasuka biyo tanan nakeso muma mubi, sabida tunda kikaga sunbi hanyar tokuwa inshaa Allah zata b'ulle ne"
Cikin damuwa ta kalleshi sosai tana gyaran tsayuwarta

"Nasani,gasu d'auke da yare irin namu ma, amma ni ba wannan ganin mugwayen mutane sun fito daga hanyar se jikina yae sanyi, banso mu bi hanyar hankalina be kwanta da itaba kuma" Yama rasa tayaya ze rarrasheta, ganin ya tsaya yana kallonta kurun ya sanya tace tana tara ruwan hawaye a idanta

"Kaji fa me suke cewa akan mace, idan kuma muka k'ara had'uwa dasu fa?"

"Kiyi adu'a yanda kikaga Allah ya korar mana su cikin sauqi hakan ko yanzu da k'afarsu zasuyi ta kansu ko k'ara ganinmu sukayi Allah ne ze kawo mana mafita" Raurau tae da ido tamkar zatayi kuka

"Dan Allah ka kula dani kaji?" Murmushi ya d'anyi

"Karki samu damuwa zuhra" haka suka ebi kud'i suka d'aura akunkurunsu jikin fatar shikamma zagayewa yae gaba d'aya, harsun kama hanyar ya waigo, bundiga k'arama k'waya biyu ya d'auka da adda d'aya yace

"Muje" ba musu tabi bayanshi suka kama hanya..

***********
Seda ya iso wannan k'auyen sannan suka tsallak ruwa zuwa k'auye na farko, suka k'ara wuce na biyu seda suka isa na ukun sannan seya isar da umarnin mom haka ya samu samari se shewa suke su kusan 10.sukace zasu rakasu har gida acikin kwana 6, da wannan ya kwana agarin seyaji meya faru tukunna.

************
Sunyi tafiyar data basu mamaki, kusan kwanaki 2 amma basu ga alamar wani garin ba kusa ko nesa dasu, hankulansu atashe yake ga ynuwa da uwar qishiruwa suna ji kamar me, zuwa yanzu Zuhrah tasoma kasawa sabida acen akwai abinci koba komai ana cin nama da sauran abubuwa

"Kace Al-hassan sunan ko?" Kallonta yar cikeda tausayi shi kanshi ya gaji sosai

"Ea sunana kenan" jinjina kanta tae

"Wlh na gaji Al-hassan, a mugun gajiye nake kuma yunwa nakeji ga uwar qishin ruwa danake ji" Dafe goshinsa yae

"Kiyi hakuri zuhra, inshaa Allah zakiga mun qarisa wani garin" batace komai ba suka ci gaba da tafiyar cikin gajiya, wani k'auye suka ci karo dashi mara hayaniya kuma kaman bashida yawa ma k'auyen, ganin da mutane sukai musu kurun se suka fara gudu yara da manya suna magana da harshen fulatanci akan ga yaran songai nan, sarai Zuhrah taji me suke cewa, da wannan tayi k'arfin halin soma tunka rarsu amma kowa se gudunta yakeyi......

**********
Bayan kwanaki hud'u ma sega wannan mutanen akan sunkai su Lawuri har gida sedai basu isa cikin garin ba suka juyo amma tabbas har hayewar garin sunyi dan har suna hango mutan smgarin suna sha'anin su da wannan dai suka dawo abunsu, godiya yae ya saka da abinda ya alqawarta ya juyo zuciyarsa babu dad'i ko kad'an.

Kafin kace meye wannan har an zagaye su kaf, ana zuba musu ihu akai da ababen makamai a hannu, da k'yar Zuhrah ta samu wani ya saurareta tamai bayani sosai akai abinda ya fito dasu daga wancen rundunar ta songai harta fulatancin dasuke ya sanya aka yarda da ita tayi bayani akan Hurairah sam baya jin fulatanci sabida shid'in mutumin k'abilar hausa zalla ne, ita kua mahaifiyrta en mutan fulanice kuma bata musu magana ta hausa, gun sarki aka kaisu ta qara koromai bayani, yace shisam be yarda dasu ba se idan zasu amince a d'aura musu auren dasukace shiya fito dasu, nan tamai bayanin cewa dama kosun d'aura babu auren nasu tunda maguzawa ne basusan Allah ba, su kuwa musulmai ne kuma basusan juna ba se agun, cikin harshen fulatanci ya furta

"Kinga yarinya dole fa semun d'aura muku auren nan zamu yarda daku, idan kuma ku masu lek'en asiri ne fa? Indai har hakane menene zesa ku gudu kuku biyu mace da namiji ba muharamman juna ba, so ake amana wayau, aini inada ilimi na, shekara nawa jama'ar songai suke hallaka mana en uwanmu da dukiyoyin mu? Basuda mafaka d'aya sedai su cutar damu su gudu, ko yanzu wlhy kasheku zamuyi annuyarku ta biyu" murya na rawa tace

"Kayi hakuri ka yarda damu sarki me adalci, yaya za'a samu fulani a jama'ar songai? Wlhy kamamu sukayi suka riqemu bamusan manufarsu tayin hakan ba" Kallon shek'ek'e ya mata

"Yarinya kasheku fa zanyi" Durk'ushewa tae agun

"Na yarda ka d'aura mana aure, na yarda zamu zauna harna tsawon lokacin daka ambata tare daku lokacin daya maka a matsayin miji da mata,idan har kaga wani abu a tattare damu na rashin gaskia ka kashe mu, amma yanzu kamun rai ka bamu wannan damar" seda yae magana da en fadawansa sannan yace zasu d'aura aurensu zakuma su basu wurin zama su zauna dasu na watanni biyu, idan songai da jama'ar sa suka kawo musu wata ziyarar to suma sesun kashe su har lahira, a garin su kuma baliga girmanta da baligi seda aure bazasu lamunta ya lalata musu yara mata ba, dan Haka dole sesun d'aura musu auren koyayane" Shiru tae tana kallon Al-hassan dankuwa tasani besan me ake cewa ba sam

"Ranka ya dad'e sadaki nafa" kallon kunkurunsu yae yace

"Kamar ba'a nigeria muke ba? Ai ga kud'inan a hannun ku?" Kallon Al-hassan take

"Muma ba damu bane ba kud'in" tsaki yaja

"Kuyita rik'ewa nine zan biya sadakin amma ko bakwaso yanzu zan had'a shaidu a d'aura muku aure" haka ta zauna ta baiwa Alhassan labari duk hankalinsa ya tashi babu yanda ya iya dole ya amince, sunaji suna gani tsohon nan ya biya sadakin su suka kuma d'aura musu aure!!!!.

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

******

"A tunninki zaki iya ne? Kina ganin hakan daidaine ya dace kenan wannan auren?" Kallon sa take cikin wani yanayi me matuk'ar wuyar fassara

"Kayi Hakuri kaji, bamuda zab'in daya wuce hakan, kuma ai dakai nayi maganar seda muka yanke shawarar atare idan ba dan ka bada bakin yin hakan ba babu kalar k'aud'in daze kaini in fad'a hakan kona zartar da hukunci kaina tsaye" Shiru yae
Chapter 26 · 0% Book details