← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 39

Sashe 34

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Maza kici abinci kinajina ko?" Shiru tayi ta janyo plate d'in agabanta se hawaye, haka tasoma cin kazar tamkar tanacin magani, hankalinta a matuk'ar tashe batako jin dad'in abincin ta soma ci, shikuwa cikin dakiya ya kasa ya tsare, seda taci sosai sannan tasha lemon

"Ki tashi zan miki wanka ki huta" da sauri ta kalleshi

"Wanka kuma Al-hassan, dan Allah zanyi da kaina" kawar da kanshi yae daga dubanta

"Ea min gaji, kuma kaman jikin ya soma miki nauyi kinata bak'i alamar bakya wankan k'warai" narai narai tayi da ido

"Amma Al-hassan ni...

"Danla Zuhra banason gadddama, and kinemi sunan daya dace kike kirana dashi,ke bakya majin kunya kaman sa'anki kina kiran sunana gatsai, ina k'annena fa na tabbatar Cya sedai kui sa'a da ita"

"Kayi hakuri zanna rik'a cewa yaya" shiru yae kurin be kula taba, nan ta zauna har wani lokaci me tsayi be tanka mata ba sam!

***********

Yaudai Abu sufyan gashi ga Ayusher amma da alama dukkaninsu kunyan juna sukeyi, sabida da k'yar suka iya cin kazar atare, sallan ma dai da k'yar ya furta suyita, bayan nan kuma akazo shirin bacci amarya ta gagara sauya kaya

"Ki rage nauyin kayan jikin ki mana Ayusher, sekiji dad'in baccin ko kuwa"

Saukar da kanta tae a k'asa cikeda kunya

"Kozaka bani wuri to" murmushin
yae yabar d'akin zuwa d'akin dayake mallakin sa, acen ya watsa ruwa yakuma sauya kayan jikinsa zuwa gajeran wando kawai, kwantaccen gargarsan k'irjinsa ya bayyana, cikar halittarsa ta zakin namiji, kai tsaye d'akin ya mufa ya tarar tana zaune akan tsakiyar gadon sanye da hijab ajikinta da alama adu'ae bacci takeyi, da murmushi ya d'are tsakiyar gadon

"Nima amum adu'a" ya furta cikeda zolaya

"Kaima idan kaje kwanciya kayi da kanka" kallonta yae

"Tunda anan zamu kwana atare mezesa bazaki minba ba" batace komai ba se murmushin datayi, haka ta idar ta matsa nesa dashi ta takure a hijabi, gagara yae tab'ata sabida shi yama rasa menene yakeji, badai kunya ba sekace ba namiji ba? Ya tambayi kansa, a hankali ya matsa kusa da ita bayan ya kashe fitilar d'akin ya rungumota jikinsa, sedai gogan ya kasa aikata mata komai, babu abinda kakeji se nausawar qirjinsu su duka, ita kanta a tsorace take.

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

32
Da k'yar ta iya saka towel ajikinta se kakkauda kai gefe takeyi cikin tsananin kunya da bak'ik cikin abinda Abu Hurairah yake mata, seda ya had'a ruwan da kanshi sannan ya zare towel d'in jikinta duk inda kunya take ta gama kamata, ta gagara d'aga idanta ta kalleshi, wani kukane yazo mata me matuk'ar ciwo ta gagara rik'ewa kurun seta saka kuka, beko kalleta ba, soso ya saka kurin ya sab'eta tamkar yanda akewa jinjiraye, seda ya kammala mata sannan ya d'aura mata towel d'in, hannayensa biyu ya saka ya d'auketa gaba d'aya zuwa cikin bedroom d'in, a saman gadon ya direta ya koma ban d'akin shima yae wanka ya d'auro towel a k'ugun sa, ya fito da d'aya a hannunsa yana tsane ruwan kansa dana jikin sa, kusa da ita ya zauna, ya waigo ya kalleta

"Yadai, zaki iya saka kayanne kona tayaki?" Bata dube shiba tace

"Cikinane ya k'ullemun amma idan ya sake zan tashi na saka" mik'ewa yae ya duba acikin wardrobe d'inta ya lalubo riga silk material me tsantsi me fad'i sosai da gajeran wandon rigar ya kawo mata, zaune ya zaunar da ita da kanshi ya saka mata riga ya bata wandon ta saka, sannan yace

"Bakida hula ne, ya kamata ki saka ki rufe kanki ko a haka zaki kwana?" Wucewa tae ta shiga duddubawa dan batasan ina aka ajiye mata kayan ba da k'yar ta samo wata hula tazo ta zauna a bakin gadon, fitilar d'akin ya kashe ya d'are kan gadon

"Kizo nan" ya furta cikin dakiya ita batasan meke sanya take tsoron saba, kwanciya sosai tayi amma a nesa dashi

"Ki matso zanwa yarana adu'a ne" batada zab'in daya wuce ta matsa d'in, tunaninda duk yana gun kalaman yaa Faruk, bataso take karya alk'awari ko kad'an, amma yazatayi da tsoron Abu hurairah gaba d'aya ya rikid'e ya dawo wani masifaffe, matsawan tayi sosai kusa dashi yakai hannunsa akan cikinta ya soma adu'a, yafi 10mms yanayi kafin ya juya mata baya ya soma adu'arshi bayan daya idar se shiru taji, lokacin awa d'aya ya wuce ma ta kira sunansa kusam so biyu beko motsa ba, da sauri ta sakko daga kan gadon ta janyo jakarta, wayarta ta zaro ta soma k'ok'arin kira.

Faruk yana zaune wayan shi yae k'ara , yana cikin tsananin damuwa gashi har k'arfe d'ayan dare ya gota, ganin sunan me kiranshi ya sanya yae saurin d'aukar waya muryanshi har rawa yake wurin fad'an

"Bintu!" Cikin dashewar murya tace

"Kayi hak'uri yaa Faruk, wlhy komai rintsi bazanci amanar kaba har abada" zufa ya sharce sannan yace

"Amma dukda haka kike k'in d'aukar wayana dan kuna tare" kallon gefen da Abu huraira yake tae

"Yaa Faruk wayan yana silent ne fa"

"Kina nufin ke bakimayi tunanin ki kirani ba?" Shiru tae

"Seda nace dake karkiyi wannan tariyar ta yaudara, kince abinda ya had'aku da farko tsautsayi ne da kuma rabo, wannan karon bazan d'auka hakan ba, dolene ki rik'emun adalci, karki mana tsawon shekaru hud'u ina jirank8 ki gama jami'a, bayan nan na shud'e shekaru uku dama wasu dakon watanni ina jiran dawowar ki bayan kowane mahaluki ciki kuwa hadda iyayenki sun cire rai akan dawowar ki, kowa yace bazaki dawo ba na kafe, yanzu kin dawo da auren wani hadda ciki, still dai na kafe ya kamata ki tausayamun"

"Yaa Faruk wlhy na sani, namaka alk'awarin har inbar gidan nan bazan bari wani abu ya shiga tsakanina dashi ba" jinjina kansa yae

"Ok!! To na aminta dake, kullum dare zamu rik'a raba dare muna waya kamar sanda kike gida sabida kinga ai batare kuke kwana ba ko" muryarta har sark'ewa yake sanda tace

"Ea hakane amma yanzu bacci nakeji sosai kasan nagaji, sedai gobe ko?" Jinjina kai yae

"Tose goben zan kiraki da safe inji ya kika kwana, and a rik'e alqawari plss, kike yawo da hijab ma" gyad'a kanta tae tamkar yana kallonta kafin ta kashe wayar cikin jin zuciyarta babu dad'i, yaya zata rik'a waya da aure a kanta? Mesa zuciyarta sam bata ke mata adalci ace se mugun k'ulli take mata akan Faruk, taji zata kaso wannan auren ta aureshi kodan halaccin daya mata amma hakan bayana nufin wai tayita keta haddin wannan auren ba, ganibtake tamkar taci amanar faruk dayawa shisa ta kasa dena yin wayar dashi........

***********
*Washe gari*

Mamaki sufyan keyi ace duk gayu da rashin kunyan da ayusher ke mai ada yanzu kurun sabida sun kwana a tare ta wani kama ta zama kurma ko kallon sa ma batayi, bakuma abin da ya mata illah rungumar kawai

"Abincin ma bazakici a gabana ba, nashiga ajanna ni Al-hussain, kina shirin rikitar dani Aisha, menene na wannan abun haka wai? Ko fushin ne har yanzu?" Ci gaba tai da wasa da cokalin datake cin abinci dashi tana murmushi

"Ba gashi ina ciba?" Ta bashi amsa da tambaya

"Banga abinda kikeci ba nikam,har abincin ya gama sandarewa bakici komai ba, barin koma d'akin kawai" batace msa komai ba harya bar gun...

********
Tunda general yazo Lawuri ke kuka tana ce masa zataje gun Abu Huraira da Abu sufyan, yarasa ima ze dafe sabida harga Allah baya fatan abinda ze juyar msa da farin cikin yaran sa,ba kuma hakance fatansa ba akan su, yakuma sani wannan karon koda mom tayi rigima batada aifi konan da cen, da wannan ya sanya aka bata hak'uri dukda ya kula tana gane yaren hausa daga ita har barbo ma, sedai mayarwanne bako wanne suka iya ba, amma rigimar data saka ya wuce tunanin sa dan haka ya mata alk'awarin inshaa Allah jibi ze kaita inda suke......

Ran Abu Hurairah yakai mak'ura gun b'aci dajin wannan rainin wayon da Zuhra keyi, tama gama raina sa, wato shi zatawa rainin wayau har haka, da wani ma take magana a waya, har tana masa alk'awarin baze tab'a taba!!! Lallai seya nuna mata iyakar ta seya tabbatar mata da cewar shayi ma ruwa ne, seya nuna mata shid'in cikakken namiji ne.

Tunda ya tashi kuwa hatta gaisuwar ta ciki ciki ya amsa mata se wani shan magani yakeyi, duk setasha jinin jikinta, shi kuwa bayaso ta gane yaji sanda take wayar da wani gardi, dan haka beko nunar mata ya gane ba, abinci ma beci agidan ba ta kansa yae abinshi, dare yayi ya dawo d'akinta kwamciya, dukseta takura ba haka taso ba, kallonshi tayi cikin tsoro tace

"Yaa Huraira dama cewa nayi ni banajin tsoron kwana ni kad'ai a d'aki, daka koma d'akinka kawai" Wani mugun kallo ya wurga mata daya haddasa mata shiga taitayin ta,da sauri ta kawar da idanta daga dubansa

"Kizo ki kwanta" ya furta cikin tsare gida, mik'ewa tae daga zaman da tai tace

"Ina zuwa zan jona wayana charge a parlor" gyaran kwanciyar sa yae

"Na gashe wayar na jona miki charging, banaso ake barin waya bud'e da dare" shiru tae bata masan ya d'auki wayar ba itakam yanzu ya zatayi da faruk?
Chapter 34 · 0% Book details