← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 39

Sashe 4

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*********
Duk yanda taso tayi bacci abun ya gagareta, bazata iya hak'ura da rashin jin yayyun nataba, shak'uwace me tsanani a tsakaninsu, Fuskar wayarta ta kalla da sunayen su a k'alla ko wanne ta kira wayanshi yafi so hamsin amma baya tafiya, duk iyakan k'ok'arinta not reachable ake cewa da ita to ina suka shiga? Wannan itace tambayar da takewa kanta amma bata samu amsaba har wannan lokacin.

***********
Wayanshi ya danna gefen key haske ya bayyana, agogon wayan ya nuna k'arfe goma da rabi hadda mintuna uku na dare gumi ya sharce dan a zahirin gaskia a tsorace sosai yake, yawun bakinsa ma ya k'afe sam bayada wani abu dayae saura daze had'iya a bakin

"Abu Sufyan nashiga dana sani fa, dana sanin hanyar nan damuka d'akko cikin wannan daren damun sani damun kwana a k'auyen, gwara zazzab'in cizon sauro da wannan tashi hankalin damuke ciki, idan dai har daidai muka biyo hanyarnan tokuwa da tuni munzo wurin lakar damuka fad'a ciki d'azu, amma gashi yanzu shiru kusan sa'o'i biyu da matasan mintuna sun shud'e amma shiru kakeji, ina fatan ba wata hanyar muka k'ara cafka ba mara b'ullewa" Cikin damuwa Dawud yace

"Wannan kam tabbas wata *Doguwar hanya* ce muka d'akko me matuk'ar wahalar b'ullewa"

"Tuk'in nan danake tafiya ne kurun nakeyi amma wlhy bana gane kan hanyoyin nan, ban magana bane dankar na tsoratar daku amma hanyar seta rik'amun iri d'aya duk inda zanbi, ya dace musan abinyi gaskia" Yawun wahala Dawud ya had'iya ya tuna maganar mahaifuyarshi sanda ze fito gida

"Yanzu kai me zaka cewa kabeer? Kaine babban abokinsa amma akan ka tsaya hidimarsa kafiso kaje gantale, su sunada hujja dan ubansu ne ya aikesu kai kuma kanada wata hujjar ne, haba Dawud? Ya dace kawa kanka fad'a gaskia" Nisawa yae tunawa da ansan daya bata

"Umma ki gane tafiyan nan tunda Twins zasuyita nima dolene inje, bazan ganewa komai ba idan basa nan bikin ba wani dad'i zemu mn ba, nidai kimun kurun ita nake buk'ata" Adu'ar tamasa ya juya abunsa kuwa yabar gidan.

"Afu sufyan kasan me, Nemi wuri med'an fili kayi parkin motar nan kurun, mu kasheta mu sauke glass ko yayane, ka kunna mana karatun alqurani me girma, idan gari ya soma wayewa semu kama hanya, dan kar mui nisa inda bazamu ganeba koda akwai yalwar haske" Kallon juna sukai shida twin d'inshi ya kad'a masa kanshi akan hakan shawarace me kyau, cikin sanyin jiki yaja gefe yae parking adaidai wata bishiyar tare da janyo wayarshi ya kunna karatun alk'urani me girma a hankaki ya zuge glass na gaba duka biyu na baya d'aya kawai kwanciya yae jikin sit na kujerar ya lumshe idanshi tare da soma rero duk wata adu'ar datazo bakin sa ta tsari, haka suma sukeyi a hankali....

***********

Hasken Rana shine abinda ya farkar da Abu Sufyan dayan daga nannauyan baccin daya d'auke dukansu batare dasun shirya zuwan saba, wayarsa kuwa har cahrge ya d'auke sabida ya da take kunne, karon sa na farko kenan tun bayan daya girma da wani abu me kamada yin salla asuba ba'a cikin lokaci ba ya same shi, kallon Dawud yae dake gefenshi,baccin sa shima yake cikin nutsuwa sedai badan dad'i ba kod'an da yake a zaune yakene oho, ko shakka ba yayi sun kai nisa 5 kafin baccin ya sacesu dabadan hakan ba ba abinda ze hanawa d'ayansu farkawa adaidai lokacin daya saba tashi sallan asuba, hannu yakai yad'an bubbugi kafad'ar Dawud inda a hankali ya bud'e idanshi d'auke da salatin annabi a bakin sa, Abu Huraira ma farkawa yae suka kalli juna cikin mamakin baccin dasukayi, kan su sakko daga motar dukkansu su soma shirin d'aura alwala da d'an ruwan dasuka zo dashi na Faro.... Se bayan da suka sallaci sallolin dabasu samu sunyiba data asuba sannan suka yi addu'ar neman yafiya kan daga bisani su mik'e suna ninke carpet dake hannun su wanda dama anxo dashi, Abu Huraira ne yawa wurin kallon tsafta sosai kan daga bisani ya nisa yace

"Ko kunsan cewan kwata kwata ba alamun sawun mutane nabi nan hanyar ko zancen wata mota kaiko babur da keke banaji suna bi"  Jikin motar Abu Sufyan ya jingine cikeda damuwa yace

"Abinda ya kamacemu shine mu qarawa motar nan mai mu kama gabanmu yanzu Alhamdulillah safiyane inshaa Allah zamu gano hanyar" kallon tausayin kansu Abu huraira ya mai kanyace

"Abu Sufyan kasan Allah, wlhy a madifar tsorace nake, dabadan da Hilux mukazo ba da ba abinda ze hanamu shan bak'ar wahala tun daren jiya, yanzu kuma tsorona Allah banga inda zamu biba, ko ina yakoma mun iri d'aya" Mamaki ne sosainya bayyana a idon Dawud

"Kaima ka kula kenan? Na zata d'emuwane ya kamani ai" Hannunsa ya zura a lajihunsa d'aya jal

"Nikaina ban fahimci komai ba, kasan me dana farka senaga kaman jiya banan na ajiye kan motar ba" shiru ne ya ratsa wurin na wuccin gadi kafin daga bisani Abu sufyan yace

"Allah ya gani iyayen mu mukewa biyayya mukazo wanan jejin, da yardar Allah da qarfin adu'ar su bazamu tab'e ba, kuzo mui lalube inshaa Allah zamu b'ulle" cikin damuwa suka d'akko man fetur suka zube ajikin motar sannan suka koma ciki suna tashe  tax wannan karon Dawud ne ya karb'i Tuk'in, Abu sufyan yana baya ya kwanta yana me lumshe idansa, yunwa yakeji ma sosai dan haka ya janyo musu cake da drinks ya baiwa kowa yanka suna tafi sunaci badan dad'i ba, gabaki d'ayansu hankulansu a tashe suke kasancewar basu tab'a tsintar kansu a jeji ba se wannan karon........

********

  Yajima tsaye a kanta yana nazarin yanayinta, samsamsam ya kasa gane kan Haj Adama,tunda aka gagara samun lambobin wayoyin yaran nan jiya ko abinci tak'i taci, zama yae kusa da ita ya rik'o hannun ta

"Haba hajiyar general mesa kike hakane?  Ai duk yayinda kikaji shiru tokuwa da yardar lillahi lafiya ce take kawo hakan, nifa inaga yarannan dan kurin sunyi tafiyar nan ne basaso suka kama suka rufe wayoyinsu, suna kan fushi har yanzu, amma zasu bud'e ne" d'ago idanta tae dasu kae ja ta kalleshi, cikin takaici tace

"Bana tunanin na d'aura kyautar Allah akan wata turba masiffanciyar wannan, da kansu bazasuyi fushi da iyayen suba akan abinda yafi wanan ma bare wannan abin dabe taka kara ya karya ba, girman nak'uda yawane dashi koda bazaka yarda dani ba kasani koyaya matsala take kad'an tokuwa tabbas itace ta hanasu bud'e wayoyinsu kokuma a samesu" Sauke nannauyar ajiyan zuciya yae

"Bamuda wani zab'i daya wuce mu musu adu'a arayuwa, da damuwar nan tana maganin wani abu data miki Haj, ina baki shawara kurun ki musu adu'a zatafi saurin isa garesu akan wannan damuwar dakika sanyawa kanki, kici abinci ki miqawa Allah lamuranki inshaa Allah zakiga haske" Batace masa komai ba harya mik'e yabar mata d'akin.

*********
Duk yanda sukaso su gano kan hanyar abun yaci tura, sunyi zagaye sunyi kwana har sun gaji amma sam basu gano komai ba, zuwa yanzu man motar tasuma yayi qasa sosai ga yamma tayi cake kurin sukeci se sallah dasuke idan time yayi, alwala ma se sun riqe sabida ruwan su saura roba bakwai kurin, kansu ya kunce ainun.

Tunda magrib tae musu a wannan jejin suka sare da fita aciki a wannan ranar, to save there remaining fuel kurin sukae parking sukai sallah skaci cake se dabino suka sha lemo sa ruwa suka hau karatun alqur'ani me girma, sun jima sunayi har suka kintaci lokacin sallan isha suka tashi sukayi sannan suka shinfid'a qatuwar dadduma ajikin bayan motar su, suka koma suka kwanta acen cikin budadd'en booth d'in dasuka shinfid'a dandumar, sama dukkansu ke kallo bayan sunyi pillow da trow pillows dake cikin motar farin wata ya haske sararin samaniya bakajin sautin komai se bugawar zuciyoyin su dakuma sautin kukan tsuntsayen dake tashi lokaci zuwa lokaci, Abu sufyan ne ya kai hannunshi ya rik'o hannun Abu Huraira cikin muryan damuwa ya furta

"Brother am really scared please pray for us" Matse hannun nashi danashi cikin tausayi yace

"Keep reciting Ayatul kursiy brother, everything will be alright ok?" Yafad'a yana me duban face d'inshi acikin d'an hasken na farin wata, dawud ma a hankali ya soma adu'a ba k'akk'autawa........ Kuka suka soma jiyo tamkar na zaki, a tare suka miqe a zaune dukansu, se zare ido sukeyi yayinda kukan ke qara kusan tar inda suke, da gudu suka sakko suka bud'e motar, amma ina kafin sukai ga shigewa har abun ya qarado inda suke.....

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

       04

Sojojin basu isa garin nasu Baba ladi ba se bayan 2 days,haka suka wuni a garin bayan an tabbatar musu sun juya, amma wannan karon tare da Baba ladi suka juyo, sabida ta kaisu wannan Hotel dasuka sauka aji kosun koma, ga mamakin su basu koma ba tun ranar, ga kayansu ma dasuka bari anan kuma kud'in sati suka biya gashi yanzu kusan 6days babusu babu labarin su sam, sojojin hankalinsu ya tashi, anan sukawa kansu masauki washe gari suka juya k'auyen nasu Baba ladi da guzurin man fetur me yawa kaman yanda sukeyi idan zasuje jeji aiki.

K'anin Baba Ladi yae gyaran murya yace da Oga Shamsu
Chapter 4 · 0% Book details