← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 39

Sashe 21

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan akayi hakan zamu samu sassauci kaga tana samun difficulties wurin magana so dole semun d'auki mataki wannan ciwon maya buk'atar magani sedai ayita kulawa dasu ana koyar dasu abubuwa masu yawa" Sosai sufyan yae godiya kafin su rabu.

***********
   Murna awurin sufyan ba'a magana yana fatar karma memory d'in nata ya dawo sabida yanaso tasoshi shishi kad'ai batare da wani ba, yanaso ta manta da wani Abu Hurairah tun a wancen garin ya kula cewar tanason huraira shikuma baya fatan taso waninsa.

   Zama yae da kanshi yake bata abinci abaki, se murmushi yake zuba mata yana mata magana da hannu, kallonsa kurin takeyi bata fahim tarsa sam, language data iya shibawai ya iya bane ba ruwa ya bata tasha sannan yace

"Lawuri?" Kallonsa takeyi sam bata gane ko waye bama tunaninta ya tsaya cak ta gagara tunanin komai ita kam

"Sannu" shine abinda ya furta yana murmushi, ta gane kalmar tasan ta amma bata tunano komai ba, TV ya kunna ya zauna yana kallo yana nazarin kalmomin yarbanci daya soma koya a wurin Dawood da takarda da biro a hannun sa, so yake yariqa yin magana da ita shishi kad'ai, ya iya yaren su sabida kota kwana idan ma memory d'inta ya dawo shine abu huraira shi takejin yarensa kawai.....

     "Al-Hussain ina cikin tashin hankali, yaran nanfa hakk'in su yana kanmu, mune fa mukazo dasu wannan Doguwar hanyar batare da munyi wani dogon tunaniba, yanzu kana ganin daidai ne ace mu k'yalesu? Kana ganin daidaine mu fita sha'anin su bamusan hannun wa suka fad'a ba? Bamusan inda suke ba bayan ni dakai munada tabbacin cewar yaran nan basusan hanyar garin suba, ni inaga bamuwa kanmu adalci ba bakuma mu musuba" Nisawa yae yana me kallon yayan nasa

"Twin ya kakeso muyi? Neman mutum a fad'in Nigeria nan ba abu bane daze mana sauk'i, munyi iyakar yinmu mesa newai kake k'ok'arin  jefa rayuwar ka a hallaka akan wad'annan yaran? Kaga yanda ka rame kuwa? Dan Allah bro ka dena maganar yaran nan" kallonsa kawai Hurairah yake cikeda mamaki

"Al-hussain yaushe ka dena damuwa da damuwar d'an uwanka? Yaushe ka soma sauyawa haka? Har yaushe ka soma manta wa da abinda nakeso? Ka manta soyayyar danakewa yarin yar nan kuwa?" Kallonsa shima yake cikin jin zafin jin wai yanason Lawuri har haka

"Amma Al-hassan Hannifer kuma fa? Tun yaushe take dakon sonka?  Tun yaushe take bibiyar ka, banji tausayinta ba  matsayinta na mace sekai zanji tausayin ka, idan har akasan abinda kakeji game da ita babba ne ya kamata ka dubawa wannan yarinyar itama, ka ajiye son watacen dabaka masan inda take ba kaso k'anwarka ta jini" Gabaki d'aya ya gama rikitar dashi be saba yi masa magana haka ba, rana d'aya sukazo duniya amma yana matuk'ar girmamashi kasancewar shine yazo kafinshi

"Al-hussain meke dmunka ne? Meya sameka hakane baka kallon damuwata seta wata hanifer?" Mik'ewa yae

"Hanifer fa ce wata? Nifa bro damuwata d'aya wannan damuwar daka sanya kanka aciki, ka musu adu'a kurin shine abinda suka fi buk'ata a yanzu dai daga gunka" bece masa komai ba ya d'auki towel ya shiga wanka ya fito ya kimtsa se feshe feshen turaruka yake yana gyara sumar kansa yayi kyau matuk'a, kallon sa huraira yae sanda yake k'ok'arin barin d'akin

"Twin ina cikin damuwar ne zaka fita ka barni ko kamun yanda ka saba kace nazo muje gun friends namu indan sake haka muka saba dakai?" Kallon agogon hannunsa yae

"Bro da akwai inda zan biya ne gashi kaga ko wanka bakai ba, idn ka kimtsa kamun waya zan dawo na d'aukeka kaji" Bece komai se kishingida da yae

"Twin ya canja sosai, ya fita harkarsa ya dena fita tare dashi ya dena damuwa da damuwar sa meya sameshi?" Da wannan shima ya kimtsa ya fice.

**********
   "Dawood mesa kaida sufyan bakwa tausayi nane wai? Kafi kowa sanin cewar ban tab'a samun yarinyar danace ma inaso ba idan ba Lawuri ba, amma sam ta b'ata kun wofintar da ita kun manta haqqin kulawa dasu yana rataye ne a wuyanmu" kallon nutsuwa Dawood ya masa

"Nifa Abu Hurairah inaga adu'ar neman tsari ya kamata mu nema da wad'an nan mutane, bawai kai kad'ai ba nida kaina seda na fad'a tarkon ta, da momy ta kula ta dinga mun adu'a aka saka malamai ma sunayi sannan na samu lafiya akanta, abu na gaba kuma idan ka kula da kyau zakaga cewar bamune muka koresu ba da kansu suka bar gidan kuma Allah ya gani munyiniyakar yinmu, yanzu me kakeso muyi" Nisawa yae cikeda damuwa

"Amma dukda haka baka ganin ya dace mu koma garinsu mu bincika kosun dawo, ka tabbatar fa cewar bawai sunsan hanya bane ba, bakuma wai sunajin yarukan garin bane, yarbawa kuma bawai lallai su taimaka musu ba" kallon tuhuma dawood yake masa cikeda mamaki da tunanin anya hankalinka d'aya kuwa

"Kana haukane Abu Hurairah, yanzu kai Allah ya tsamoka daga hallaka sannan kace zaka koma, kasani irin azabar damukasha da *Doguwar hanyar* damuka bi Allah ne kad'ai yasa munada sauran shan ruwa agaba, kuma banda Allah babu me iya mana wannan, bari kaji idan harkai so ya rufe maka ido ni badaniba bazan tab'a komawa wannan hanyar ba, dan inada hankali na, ko dama nifa kurun ina sha'awar mukai musulunci agarin dababushi ne amma ban shirya hallakar da kaina akan mace ba"

"Haba mana Dawood mesa bakwa tausayi nane wai? Mesa kakemun haka? Wlhy rashin ganin wannan yarinyar tamkar rasa wani b'angare ne ajikina, ka taimakeni"

"Tausayinka nakeji wlhy d'an uwana, dole zanwa mommy magana ma anema maka magani kaima dan wannan abun tashin hankali ne, ace dai duk uquba da azabar damuk sha a wannan *DOGUWAR HANYAR* har kake iqirarin zaka koma?" Ai wannan kasan bawai aikine na hankali ba" Shiru kurun ya masa harya mik'e yabar masa d'akin gaba d'aya.

************
Tunda yake maganar general kallonsa kurin yakeyi, mamaki yake yanda yaron ya k'wallafa ransa akan yarinyar ya sani uwarsa koze mutu bazata yardaba, kuma yasani tabbas idan be masa abinda yake soba akwai matsala

"Amma kai Huraira dolene sekaje da kanka? Idan neman yaran kakeso ayi kabari da kaina zan tura manyan soji suje garin amma bazan bari kai kaje ba" langwab'ar da kanshi yae ya marairaice fuska

"Dad ka taimakeni aje dani, dan Allah na roqeka, kuma ni base ka gayawa mom ba kurun dai nika barni i promise u zan tsaya bayan sir shamsu akoma meye" Shiru yae yana nazarin maganar sa secen yace

"Idan kun tashi kubi ta wannan ruwan, ta garin wannan fulanin wannan jejin yanada matuk'ar hatsri, zan maka adu'a kakuma tabbatar hadda yad'uwar musulunci ya sanya kakeso kaje da wannan Allah ze dafa maka" haka yae godiya ya tashi murna fal aranshi.

**********
Tunda yaje gunta suke magana da 'yan kalmomin daya iya na yarbanci, komai shine yake shige mata gaba tanayi, sunyi shak'uwa me yawa, a hakan kuma yake mata hausa, lokuta da dama tare suke kulawa da ita shida Ayusher ko yanzu atare suke suna hausa suna yarbancin dasuma tsinta gwanin dariya, danma tanada kan kamawa sabida acikin 3 weeks harta soma iya mayarwa da hausar, ita kuwa Ayusher baiwar Allah har ita ake koyon yarbancin sabida tanaso taga Abu sufyan acikin farin ciki, kuma zaman yarinyar agidansu ya k'ara janyo kusanci a tsakanin su sabida kusan kullum yana gidan..

Mik'ewa yae ze tafi ya soma sallama dasu, kurun se Lawuri ta soma kuka akan zata bishi, hannunta ya rik'o duka biyu

"Má binó Lawuri (kiyi hak'uri Lawuri)" Langwab'ar da kanta tayi cikin shagwab'a tace

Igbawo lóma dé ? (Yaushe zaka dawo)

Murmushi yae yaji me tace amma besan meze ce mataba da
yarbancin se cewa

"Da sassafe gobe" sarai ta fahimce shi setayi murmushi tace tana zare hannayenta

"Odaró (seda safe)

Ta furta tana me juyar da kanta alamun btaso ya tafi, takaici duk se ya kama Ayusher amma seta had'iye kurin itama ta soma rarrsahinta da hausa.

Abu sufyan yabar wurin cikeda begen Lawuri yanaji aduniya baze tab'a iya yafewa waninsa itaba har abada.

**********
Shirin tafiya sukayi akan shi Huraira zashi tafiyar aikine sokoto, adu'a sosai mahaifiyar sa ta masa sannan yabar gidan, inda akayi zasu had'u da sojojin anan suka had'u general ma yayi adu'a sannan suka kama *Doguwar hanyar* dasuke fatan binta a wannan karon ya zamar musu alkhairi.

Niko nace Allah ya fitar ga A'i ga cinikin rogon ta kodai ta fad'i ko taci riba.

*********

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

*Littafina  na kud'i ne, dan Allah idan baki siyaba karki karantamun, kokimun ki tura wani gurin, bana Allah ya isa bane amma dai haqqina yana wuyan wanda ya aikata d'aya daga ciki, kuma koda ban fad'a ba duniya shaidace akan Allah isashene. Idan har kina buqatar karantawa ki nemeni ta wannan lambar 07084161619*

       19
Zaro wayrsa yae daga aljihunsa cikin takaici dan sosai ta dameshi da ringing, ganin Al hussain da yae yana kiranshi yasa ya d'aga cikin mamaki

"Mekenan haka kayi bro? Mesa zakamun haka?" Kishingida yae ajikin kujerar  motar yana lumshe ido

"Me kuma nayi maka?" Ya furta cikin mamakin kalaman d'an uwan sa

"Dad ya gayamun komai, Amma na sanar dakai yaran nan basa garinsu fa mesa zaka nace akan sekaje?" Sumar kansa ya shafo zuwa sajensa har zuwa gemunsa yad'anja a hankali

"Wane yaqini ne dakai nacewar basa garin su? Hakan yana nuni ne da cewar kasan inda suke kenan?" Se a sannan ya gano wowtar da yae na furta hakan

"Da nasan inda suke yaya zan barka ka tafi a banza? Kurin dai ni nasan basu san hanyar bane ba ko alama, kuma naga k'afarka har yanzu kana d'ingisawa ai"

"Wannan ba damuwa bane kaidai bakaso ka joining hand dani mu taimaki musulunci, baka kuma so in smu abinda nakeso so kayi abinda ya shafela plss ni zanyi nawa"  mamaki sosai kalaman sa suka baiwa sufyan

"Bro abin yakaimu haka mesa zakamun wannan maganar" tsaki Huraira yae
Chapter 21 · 0% Book details