← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 39

Sashe 37

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******
Lawuri kuwa tana zauna aka kawosu, sam ko alama bata gane suba sedai ta gane daddy ta kuma gane Oga shamsu wanda idansa ke kanta, yana mamakin yanda hasken musulunci ya gama karb'ar fatar jikinta!!! Tayi sumul abunta dukse yaji ta burgeshi haka aka kwana ana abu d'aya karatun alk'urani ake yi da adu'a ana tofesu dashi amma se a hankali sauk'i d'ayane daya zamana yau duk basuyi aman ba, amma bnda haka babu abinda ya sauya na dangane da halittar da suka dawo su dukansu, haka haka dai aka bar su kwana anan, Lawuri jin cewar sune tasha kuka dan Dawood kurun ta gane ita kanta duk wata soyayyar datake ma Abu Hurairah jin take a irin yanayin datakeji yanzu badai soyayyar aure take masa ba, gaba d'aya hankalinta da nutsuwarta sun karkarta akan ciwon su itama adu'a tashiga yin musu babu k'akk'autawa.

Boka ya fusata dan haka yau yace aje lallai a kashesu, dan aljanan tsafin sa sun sanar dashi lallai suna samun barazanar wannan littafin dasuke karantawa ko yanzu ma da k'yar suka sha, umarni ya basu akan su kshe su yau har Dawood yaga tsiyar shi d'an sarkin tsafin k'asar ne kuma ya jima yana gagarar kowa yaya za'ace mutanen wata k'aramar al'umma su fishi iya tsafi!!!

An je sallan azahar an barsu se lawuri dake salla a d'akin tare dasu, gunjin kukansu da gurnanin da suke shine ya sanyata zanzarin son ta kammala salla taji menene? Da gudu gudu ta idar da sallar, abinda tagani ajikinsu susus uku yafi komai bata tsoro, tunawa tae da azaban da mahaifinta ya saba baiwa mutane idan sun masa laif agarin, tabbas duk sukai haka daganan zasu shek'a lahira da gudun fanfalak'i, waje tae tana ihun kiran malam su kuwa har lokacin sallah sukeyi, gashi ta tabbatar cewar daga garin sune wannan mugun abun!! Ilahirin jikinta tsuma yake ganin basu idar da slla ba ya sanya ta koma d'akin da gudu abinda ya saura su gangara shine jini a baki!!!! Ko shakka batayi wannan mugun abun ne ze kashe su, ga jikinsu yanata tsagawa jini na fita duk sun dawo sekace wasu fatalwa! Tana nan tsaye har su malam suka shigo da daddy malam ma ya rikice haka a saki radio sa sautin karatun alk'urani me girma, sukuwa adu'a kowa keyi yana faman tofa musu ana nan har suka soma tari a tare jini ya soma fita daga bakinsu susu ukun...Lawuri kam k'ofar waje ta nausa da gudu tana ihu lallai k'uru mugune me suk masa? Haka nan tana ganin jinin ta tabbatar sunma mutu shine abu na k'arahe dazatayi arayuwarta indai ya kashesu seta koma gida ta kashe har ubanta har bokan!

*Nazata munbar labarin doguwar hanya tuni, ashe k'afafuwan mu da gangar jiki kurin ta baro hanyar amma ruhin mu yana cen har yauu be baro doguwar hanya ba!!! Ko zasu kub'uta?****

*wannan book nawa na kud'ine me buk'atar siya seya biya 200 kacal a sakashi a group..nemi wannan lambar 07084161619*

Mom Nu'aiym.
[11/21, 8:21 AM] Maamah twins💕❤: 36**** lokaci d'aya jikinsu ya soma tashi daga farin da yae zuwa kore shar!!! Hankalin malam ya tashi ga malam babba ya d'aga, dad ma haka ya kira mahaifin zuhrah take yazo shima ya taradda wannan mummunan tashin hankalin,mahaifin Ayusher shine yazo da wani malamin na daban inda yasoma nashi adu'o'in acikin ruwa yana tofawa haka ya dinga watsa ruwan ajikin su na tsawon lokaci, a hankali abubuwa suka soma sauyawa zuwa samuwar lafiya daga barin aman jinin da kuma sauyawar fatar jikinsu zuwa asalin fatar su ta halitta, basu gusheba daga yi musu adu'a dakuma karanto ayoyi daga alk'ur'ani me girma har sanda suka fahimci nutsuwa ta saukarwa dukkansu!! Har suka soma bacci cikeda nutsuwa.

Ihu boka keyi yana guje guje daka ganshi kaga hauka sabon kamu tuburan!!! Gabaki d'aya gidan sa seda ya qone da duk wani abu daya shafi tsafinsa da mugun bokancin sa, haka ya dawo tsirara ya ruga da gudu se waje, haka mutanenngarim suka d'auka cewan boka ya haukace gidansa ya qone k'urmus ana haka k'uru yazo ana rirrik'e da Bokan, ya shiga tashin hankali shi kanshi sabida jin me ya faru, acewar en garin duk sanda wani abu ya samu boka toko tabbas masiface zata afka musu dukkansu, haka suna kallo jikin bokan ya soma ci da wuta dole suka sakeshi ya dinga gudu yana ci da wuta har inda ya dena motasi ya mutu a sandare!! K'uru se kuka yake ga 'yan gari hankalin su duka a tashe yake.

*************
*Bayan sati uku*

Yanzunkam alhamdulillah dukkansu sun samu waraka daga ayayoyin Alk'urani me girma da kyawawan adu'o'in da ake musu dukkansu, da wannan suka bar gidan malam zuwa kowa gidan sa se dawood daya koma gidansu inda mahaifiyarsa, Dad kanshi yayi mugun d'aurewa da wannan abun, gashi Lawuri ma tayi bayanin haka boka keyi idan akawa K'uru babban laifi har amutu tsafi ne, ita kanta ta k'arayin imani da Allah da manzan Rahma (S.A.W).....ganin a garin su sedai ka shek'a lahira amma anan dazaran aka soma ambaton Allah se waraka ta samu lallai tayi imani da Allah kuma ta yarda annabi muhammadu bawan sand kuma manzan sane.....

Nisawa yae bayan dogon tunani kafin, kafin ya tattare nutsuwar sa sosai zuwaga Oga shamsu ya soma magana

"Shamsudden kasani koba maganar aiki na d'aukeka ne matsayin d'a wanda na haifa da cikina, nakuma yaba sosai da yanda kake girmamani bako kad'an ba, kaima ka d'aukeni matsayin uba bawai wani bare ba, to anan wata alfarma nake nema a gunka har qwaya biyu, wanda babu takura ciki alfarma nake nema idan kuma kaga akwai takura aciki don Allah ka gayamun gaskia, ayau ina magana dakaine ba a matsayin Babba dake sama dakai agun aiki ba ina magana dakaine a matsayin mahaifi"

D'agowa Oga shamsu yae ya kalli General kafin ya mayar da kanshi k'asa, yana matuk'ar so da k'aunar general be tab'a ganin babba me karamci kamar oga shamsu ba, yana matuka'r tallafawa maraicin sa shi kuwa menene a duniya oga shamsu ze nema ya gagara yin masa shi?

"Dad ina saurarenka" ya furta a hankali, gyaran murya general yae kafin yace

"Da farko dai so nakeyi ni da kai dakuma tawagar soja mu shiga wannan jejin mu kai addinin islama a wannan garin, malam da mahaifin sa sunce tare zamuje dasu idan kun aminta, naso inje da 'yan biyu amma ina tantama akan mahaifiyarsu bazata aminta ba kuma kaga tafimu gaskia tayita roqar mu muna kaucewa hakan muyi yanda mukaso, sabida haka ina neman jajircewarka duka duka kwanaki bakwai nakeso muje muyi mu dawo ina gani ina kuma ji ajikina *Doguwar hanya* da yara suka bi ba bisa son ranmu ba har muke ganin be zamar mana alkhairi ba to tabbas alkhairin ne a dunk'ule, idan ka duba da kyau zakaga cewar munjima munawa k'asa hidima me hatsarin gaske amma wace hidimar ce mukaima addinin Allah? Ga kuma dama har gida me zamu tsaya jira? Munyi ta yiwa al'amarin nan kucce kucce amma kaga idan kayi duba da kyau zuwaga lamarin zakga mud'in dai mune Allah ya zab'a kuma da ace bamu bame da baze rik'a kawo hanyoyin daze had'amu da waccen yarinyar ba duk girman nisan duniyar mu data banbanta, sabida haka wannan itace buk'ata ta ta farko, mu musulman soja Allah ya bamu dama da iko da makamai ya dace mu taya annabi yak'i, kaga da arna ne wlhy da tuni sun yad'a manufatsu a wannan guraren, da dukiyar su da iliminsu da karfin su suke tafiya gaba d'aya" Nisawa shmsu yae

"Daddy wannan aiba komai bane ba, wannan tafiyar tayi kuma koda zan kutu acen tabbas sena keta doguwar hanyar domin yad'a addinimun islam, koba komai zan yi farin na mutu a b'angaren bautawa addinina na bada gudummawa domin ci gaban addinin nawa na islam addini me daraja da d'aukaka, addinin gaskia addinin Allah" Fara'a sosai General ya shiga yi babu k'akk'autawa yana shiwa Shamsu albarka ya k'ara da cewar

"Naji dadin wannan al'amarin Allah ya albarkaceka ya tallafeka, se magana ga gaba kuma itace, zancen auren ka nayi nayi kak'i kayi aure Shamsu, sabida haka nakeso wannan yarinyar Naja'atu (Lawuri), ka taimaka ka aureta kaga yarancen dukkansu sonta sukeyi bazan so kansu ya rarrabu ba amma tunda duk sunyi aure kai bakayi ba ka daure ka aureta" Nanma beyi musu ba haka ya zauna ya dinga godiya har seda ran dad ya b'aci.

**********
Ayusher jikinta se rawa yake tunda Taga yaa sufyan agabanta, yaji sauk'i har suna tab'a hira, ita gashi ko angwancewa basuyiba ya fad'a ciwo, yau dai duk an cire kunya a jikinsa aka makara, anan aketa luguden sa baji ba gani, yanzuma kwance take a saman jikinsa shikuwa yana shafa sumar kanta a hankali, hannun sa yaja zuwa lips nata masu laushi ya shiga murzawa a hankali, bud'e bakin tae ya zura d'an yatsanshi inda ta gallamai cizo med'an zafi, da sauri ya janye yatsansa yana dariyar a hankali

"Baby ni kuma mena miki haka?" Turo baki tae

"Tobayan kaine kak'i kazo muje mui baccin rana" murmushi yae

"Ayush baccin rana yanzu? Shagwab'e fuskar nan ta k'arayi

"Bafa kada lafiya, bayan haka kuma bacci kakeji" murmushi ya k'arayi

"Lallai ma wato nida idona kece kikejimun bacci" Langwab'ar da kanta tae

"Yaa Sufyan dan Allah to muje d'akin mana" d'agata jikinsa yae a hankali shima yae shirin mik'ewa

"Hajiya d'agani ina patient dani baki d'aukeniba amma yau duk ajikina kika wuni, to muje d'akin" Doddoka k'afa tashiga yi a k'asa

"Gwara in huta abuna asaman jikin mijina yanzu dai mijinane babu me shamakanceni daga yin rumfa akanka, ciki kuwa hadda kai" murmushi yae

"Naji me miji, kunyar kuma fa kin siyar?" Ya tambaya yana kafeta da ido, janye idanta tae daga nashi
Chapter 37 · 0% Book details