← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 39

Sashe 31

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zuhra sannu ya jikin?" Kallon mamaki take binsa dashi, runtse idanta tae gagam cikin rashin fahimtar komai, kafin ta bud'e su ta zuba su akansa

"Al-hassan inane nan mafarki nake?" Girgiza masa kanta yae

"Bakida lafiya please save your strength basekinyi magana ba, basekinyi tunani me yawa ba Al-hassan ne" rufe idanta tae kurun tarasa tunanin me zatayi.

*********
*Bayan sati biyu*

Babu yanda iyayen ta basuyi ba amma ta kafe ita lallai idan ta haihu yaransa zata bashi su rabu, yama sauwaqe mata auren sa itakam inyaso yama haihuwa tayi iddah kenan, anyi anyi taqi, taji zafin abinda ya mata sosai taji zafin tozarcin daya janyo mata yaci amanar ta fiye da k'ima, ya tona mata asirinta dan haka ta kafe

"Ina ga zmu baku sati biyu nan gaba, ku sasata kanku, idan har kayi galaba akant ta hak'ura shi kenan amma idan har Zarah tace bazata koma ba a gaskia ni bazan tilasta mata aurenka ba, kaima shaidane akan abinda kayi sam sam baka kyautaba wlhy" shiru yae daganan aka basu wuri, mik'ewa tayi

"Idan da zakabi shawara Ko Al-hassan karka wani jira sati biyu suzo danko shekaru biyu suka zago nida aurenka har abada" kanma yace wani abin tayi ciki, gabaki d'aya duniyar juya masa take, shi yama rsa dalilin daya sanya yakejin sonta har cikin b'argon sa yanzu, ya tabbatar Allah ne ya jarabcesa da sonta dan ya wulak'anta aure.

**********
Su Lawuri dai se gasu asaman lodin yaji, sabida rashin kud'i yunwar cikinsu ma ta ishesu ga gardawan garin su sun koma dama haka akai dasu, bamusan yanda zata kaya ba idan suka isa OGUN state gamu gani dai.

Mom Nu'aim.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

*please idan kinsam baki siyaba bakida haqqin sharing ma family and frnds, idan ma kin siya ban yarda ki tura a groups ba indai ba k'awarki ba, idan kika tura a groups kina kashemun kasuwa ne, me buqatar siya 07084161619*

29

Lawuri tunda suka shigo garin OGUN STATE take rarraba ido, duk wanda suka gani zasu masabyare sama Allah ya taimakesu akwai yarbawa sosai a garin, idan tace Abuja take so suje se ace akwai nisa sesun hau mota, sunyi yawo harsun gaji, atasha ma cewa sukai a sakasu koda saman motar ne amma aka koresu akan basuda ko k'wandala.

***
Dafa hannunshi yae bayan ya gama jin komai

"Haba Hurairah, sekace ba namiji ba, karka kulata kuma koda zata kasheka karka saketa, kayi amfani da iliminka da basirar wurin ganin ka saka ta soka kota halin yayane" kallon Dawwo yae cikin damuwa

"Dawood koda inason inyi hakan dole seta bani damar yin hakan, bata fitowa koda zuwa nayi gidansu fa, waya inta kira bata d'agawa wani zubin ma sekaji wayar a kashe" Dafe kanshi yae

"Muje gidan yanzu" ya furta bayan daya d'ago yana kallon sa, ba musu ya karkata akalar motar sa zuwa gidan nasu, me gadi na ganin motar sa ya wangale masa gate ya zura kan motar ciki, suka parka suka fito.
Abu hurairah yasha mamakin jin dawood yace akira masa mahaifiyar zuhra, bayan tazo kuwa suka gaisa cikeda mutunci yace

"Dama Mama zancen daine na zuhra da kuma Abu huraira, labari ya samen akan hukuncin data yanke masa, yanata k'ok'arin ya gyara kuskuren sa amma be samu damar hakan ba, sabida bata bari ya ganta ga kuma sam bata d'aukar wayarsa, wlhy mama bmason mutuwar auren nan wancen ma abun yarasa yanda ze fad'a ne kamar yanda ta gagara gaya muku, sabida dukkansu suna tunanin bazaku yarda dasu ba, ga kuma besn an samu k'aruwa a tsakanin su ba" Jinjina kai umma tayi

"To yanzu ni wace gudunmawa kuke tunanin zan iya baku a rayuwa? Ni nafiku qin yanda auren nan yake shirin lalacewa amma ya zanyi, matsalar Bintu halin mahaifinta sak tayo, kafiya sosai idan tajewa abu, nayi nayi nima sedai adu'a kawai" Nisawa yae

"Nasani babu uwa ta gari dazataso mutuwar auren 'yarta Mama, Doguwar hanya tayi sanadiyar zuwan auren haka, amma idan so samune a bashi damar ziyartar ta a d'akinta, tunda bata bari su gana dole seda hakan" murmushin manya uwar tayi sabida ta kula dawwod duniyanci yazo dashi a ladabce

"Duk inda ze ganta ai iyalinsa ce har yanzu, bayida shamaki da wannan indai ganin matar sane, ko yanzu ya shirya zan sanya a kaishi b'angaren su, dayake b'angarena daban nida su, se Hafsat tazo ta rakashin" Murmushi yae

"Hakane mama mungode sosai da fahimta, kuma dan Allah muna roqon iri aci gaba dayi mana ban hak'uri, lallai bamu kyautaba amma muna neman yafiyar ta daku baki d'aya, muna kuma neman alfarmar abamu wata damar domin gyaran b'arakar damuka aikata" Godiya tae mus sosai da karamci sannan ta juya domin turo hafsat sabida tayiwa Abu Hurairah iso zuwa wurin Zuhra batare da sanin zuhra ba dan idan tasani seta datse k'ofar......

Akaratun k'urani me girma takeyi daga ita se er vest duk ta gama d'ameta d'am, zafi sosai takeji wannan ya sanya ta rufe iya kanta sabida ambaton ayar Allah, taji sanda ake knocking k'ofar amma batace komai ba seda takai aya, sannan tace

"Waye" hafsat dake tsoron masifa tace d'ari d'ari

"Hafsat ce anty" tsaki taja tace

"Kije bar wanki anjima kya had'a" kallon Abu Hurairah tayi tace

"Ka shiga kawai, kayi sallama" tayi 1mns dabarin gun kafin cikeda jarumta ya d'aga k'farshi ya tura k'ofar da sallama d'auke a bakinsa murya k'asa k'asa, waigowa tai a daidai sanda ya shigo d'akin gaba d'aya, da zama cikin dabaru na masu ciki ta mik'e cikeda mamaki

"Al-hassanx meye haka? Yaya zaka shigomun cikin d'aki babu izini, beside wayema ya baka damar ka shigomun d'aki waya nuna maka nan d'in?" K'ura mata ido yae cikin kasala ya gaza furta wata kalma gaba d'aya yaran cikinta tunka suzo duniya yaji yana musu wani so dabesan akwai ironshi ba a duniya, ganin kallon ya ankrar da ita yanayin shigar ta, da sauri ta zari ta janyo hijab zata saka yae azamar rik'e mata hannu, kici kicin k'wacewa tashigayi cikin azama yae saurin k'wace hijabin ya jefar gaba d'aya, cikin zafi tace

"Wannan wane irin wulak'anci ne abinda kazomun dashi kenan har cikin gidan ubana? Me kake tsammani danine eh?" Manyan idanuwan shi ya zuba mata tanata masifa, be cika son surutu ba halin yana nan tunda ya shigo aikin kenan na zuba surutu

"Zuhrah calm down mana, bakya ganin bake kad'ai bace ba?" Kallon sa tae cikin takaici

"Nida waye? Idan ma mu dubu ne meya shafeka eh?" Mamakin tsiwarta yake ba haka ya santa ba sam

"Kiyi Hakuri zuhrah dan Allah ki baki second chance wlhy zan kula dake" Tab'e bakinta tae

"Nagaya maka neman kai nake da kaina? Kokuma rasa me kulawa dani nae, niba yarinya bace ka sauqwak'e mun zan kula da kaina" Fuskar sa ya kwab'e tamkar zeyi kuka

"Haba Zuhrah anya wannan hukuncin bemun tsauri ba ya dace ki saurreni ai ko?" Tureshi tae iya k'arfin ta

"Sanda ka wulaqanta budurcina neman ka nai? Sanda ka ketamun haddi na nemn ka nae? Sanda kake zuwarmun da sauk'i alfarmar hakan na nema? Kokuma aa sanda aka mana aure ban nemi shwararka, dangina kowa ya d'auka shege nayi har masu aikin gidan nan da masu gadin k'ofa gulmana suke akan nayi shege, ban tab'a aikata zina ba duk zamana a jeji kame nake sa kaina sabida mutuncina dana iyayena da hakk'in musulunci, ka sanya ina cikin gidanmu amma zuwa tsakar gida seya gagaran sabida bakowa ya gama yarda dani ba, Allah kad'ai ne yasan wanda bazuwanka ba ko'a gabansa aka d'aura aurwnmu baze yarda dani ba sabida mugun abun daka aikata mun, na rayu wulak'ance a hotel sama da watannin biyu, naga wulak'anci harme gyaran d'akunan hotel seda yanemi yin lalata dani danyasan halacci baze kaini zaman hotel ba, na wuni da yunwa na kwana da yunwa duk a ta dalilinka, ka d'irkamun ciki ka barni da d'an hals ana cewa shege, me ya saura zaka gayamun? Kai a tunanin ka wannan abubuwan zasu gogene duk a wuni d'aya? Kana ganin akwai ranar dazatazo dazan yafe maka ma bare ayi zancen wai mu zauna a inuwa d'aya ta miji da mata, kayi kuskure wlhi Abu Hurairah, hakk'oki'ina daka take bazan yafe ba har abada, kuma kome zakace na dad'in baki na gama zaman aure dakai damacen rabon wannan cikin ne maza kaficemun saga d'aki" Jikinsa yayi mugun sanyi ba abu bane me sauk'i kam ace wai ta yafe masa a yanda ta d'auka da zafin nan, yama rasa me zeyi, bashida bakin magana gwiwa a sace ya baro d'akin batare daace kanzil ba sam yawun bakinsa bazasu isheshi ya kashe bushewar mak'oshin saba!!!

*********
Tunda ya soma magana dad ke kallonsa yana murmushi

"Lallai Al-hussain ba kunya, yanzu dai so kake inje nema maka auren Aisha kenan? Lallai ma dole inwa wannan aure" sadda kanshi yae a k'asa batare dayace k'ala ba yana zuba murmushi

"Katashi kaje zanyi yanda ya dace kaji?" Shiru yae ya mik'e aranshi yanajin dad'in wannan ita kad'ai ce hanya madaidaiciya....

Waya ya kida mahaifin Aysuher akan yanaso suzo zancen yaran, Alhaji yusha'u yace

"Ba damuwa Ganeral ran sati su yaya Mu'az zasuzo dama inyaso se kazo kaima ranar lahadi da safe semu zauna a tattauna kawai" godiya ya masa kan suyi sallama.
********
*Bani tunanin Yusha'u kanada hankali wlhy, Aishan yarinya ce? Akan me bazamu d'aura mata auren yanzu ba, ina manemin auren ba mara k'arfi bane? Tun yaushe muke bibiyarka akan batun nan? Kana sani ka take zancen mu ka turata london, shekarunta 4 acen, ta dawo munata zamcem aure kace wai ba miji yanzu shekarunta biyu kenan da dawowa, akan me zaka nemi mayar damu k'ananun yara, to zab'i ya raga naka kodai ka janye sha'anin dogon burin nan naka akan bidi'o'in banza kokuma na aura mata Auwalu ina komawa kai kokumama wlhy tallahi nida al'amarinka dana iyalanka har abada" mahaifin Ayusher sadda kanshi yae k'asa ganin yayanshi yanata yarfashi agaban manyan mutanen dasuke girmamashi gashi babu halin musawa
Chapter 31 · 0% Book details