← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 39

Sashe 11

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gani sukai wasu mutane suna yawo sa wuta suna zagayar d'akunan mutanen garin, sannan daga bisani suka cinnawa wata bukar wuta sega mutanen ciki sunfito da gudunsu suna qoqarin guduwa, suna kallo suka sassaresu su kusan hud'u, sannan suka d'aukesu suna rera wak'a abakunan su suka rawa, general jikinsa yae sanyi suna nan a b'oye har safiya ta soma yi suna kallo aka hasa wuta aka d'add'auresu ajikin ice aka soma gashin su, kansu ya masifar d'aurewa mekenan ake nufi, komawa sukai inda suka fito suke baiwa sauran labari, sabida akwai mamaki akasheku kuma makasanku suzo suna gashinku acikin gari sannan babu yako d'aga ido ya kallesu me za'ayi da naman? General dai duk dauriyar sabyau seda yae kuka yana tsoron indai ba ankashe masa yaran saba, tunda wancem garin sun sanar cewar sun gudu kuma anzo nemansu ba'a samesu ba. Shawarar kaiwa garin hari akayi amma koda suka bazama sesuka tarar kowa naman nan ake yanka masa yana ci, cikin tashin hankali sukai gaba, dan duk yanda sukaso babu wanda ya kulasu, kenan gudun da mutanen garin keyi gudu ne na gudun kar a yankasu a gasa? To amma shirun fa? Na meye? .

General yasha kuka sanda suka bashi akan sunada yaqinin yanda basu kulasuba suma bazasu kulasuba koda sunzo dan haka sunyi gaba, da wannan suka k'ara ci gaba da tafiyar dasuke.

*************
Sunyi enjoying rayuwar su abakin ruwan, har kamun kifi sukayi, sannan suka hasa wuta suka dafa shi, suka yanke shawarar kurun suje su kaiwa wannan matan dasuka baro, sunga yanda duk suka rame akwanaki qalilan kenan.

Kwanansu hud'u agarin suka nemi hanyar yi gaba inda Me garin ya basu 'yan rakiya susu biyu suka jagorance su har suka isa bakin ruwa daganan ma seda suka tsallaka dasu sannan suka dawo, anan ma sunci karo da wata rugar fulani masu karamcci an karrama su ba kad'an ba agarin, seda suka kwana uku sannan suka bar garin, a haka a haka har suka isa inda motar zata tashi zuwa cikin gari nanda kwanaki uku masu zuwa, sedai ba kamar sautan garuruwa ba dole ce ta sanya su kwana a tasha.

*********
General kuwa yasha wuya shida yaranshi kafin su taradda wannan ruwan, basu wani sha wahalar tsallaka ruwan ba suma suka isa garin,anyi sa'a general da kanshi yake jin fulatanci, bayan doguwar tambaya aka sanar masa tabbas sunzo anma sun wuce yafi da sati motar ma da ake saka ran su hau nanda kwanaki uku zata tashi, da wannan ya bada umarni akan manyan su koma inda jiragen shida wasu zasu bi sahun su twins, amma se wani ya bada shawarar su bari suje gaba d'aya inyaso se aje da wasu jiragen a d'auki wancen tunda garin dake kusa dasu naman mutane ne abincin su, hakan kuwa akayi jirgi uku suka hau a ranar suka naushi d'ayan garin.

**********
Zazzab'i sosai Lawuri keyi amma bata sanarwa kowa ba, tarasa dalilinta najin yawan fad'uwar gaba me tsanani aduk sanda ta tuna mahaifanta, da 'yan uwanta anya ta kyauta kuwa? Yanzu harse yaushe zasu samu wani sui sacrifice dashi? Idan akace basu smu bafa hakan yana nufin ta kashe iyayenta da 'yan uwanta da hannunsu, ada tana tunanin tamkar yin hakan ba komau bane mma yanzu ta hango tsantsar rashin kyautawar dabatayi ba, amma yazatayi da rayuwar ta? Tsari d'aya kenan dayazo mata, batasan yazatayi da ranta na akan wannan al'amarin, taso ta yakicewa zuciyarta amma batasan meke hanata ba akan yaran nan, ita kanta bazata iya cewa ga takamaimai abinda yasanya take binsu ba, bata tsammani akwai ranar dazatazo rana d'aya ta guji danginta ba haka kawai, anya bazata koma ba kuwa? Amma idan kuma wani abun ya same tafa? Ta tabbatar wa kanta yanda suke murna sun baro wannan bala'in bazasu yarda su rakata ba bare kuma har sun tarardda wurin da ake gasa mutun, kai koma ba hakan ba ita bazata komaba ta rasa me mata wannan maganar dasuke susu uku, ga kayan da aka sanya mata ma a wancen k'auyen a bingili suke ga masifaffen sanyin dake ratsa ta sabida zazzab'in datakeji tako ina, tarasa nutsuwarta da farin cikin ta, gefen k'irjinta na hagu zafi sosai yake mata, Barbo cema ta fahimci batada lafiya harta gayawa Dawwod data kula shishi kad'ai yakejin yaren su, anan suka taimaka mata sun neki chemist amma babu haka suka kwana tanashan wahalar sanyi.

*******Bayan kwana uku*

Ba k'aramin sanyi sukaji ba a ransu dasuka samu hawa mota for the first time tun bayan dasuka bar motarsu a wannan jejin, abin takaicinsu d'aya sama suka samu asaman kayan amfanin gona suda wasu Fulani masu qarnin tsiya, sunyi sa'a sosai sedai fa hanyar batada kyau sam, sunyi tafiya ta kusan awa uku kafin su tarar da wani titin dasukeda tabbacin tun zamanin mulkin soja aka shinfid'ashi, duk ya gama mutuwa sedai sufa hakan wata rahama ce agaresu dankuwa yaushe suka saka ran zasu ga qara ganin titi ma a rayuwar su? Ai basu zataba sam.

Su General koda suka zo ansanar dasu ai motar tafi sa'o'i uku da d'aga wa, kuma tabbas samari uku da 'yan mata biyu sun samu shiga kotar, sedai shi general baze iya jiran zagowar makon nin biyu ba kafin ya koma gida dn haka ya nemi wata hanyar musamman yasa azo masa jirgi me saukar angulu yawa hanyar k'aura, atake wani bafillatani yace dashi shi yana motar sama, kurun k'a'idane sati bibbiyu ake zuwa kuma hanyar ce ba kyau, take general ya tilas ta masa kaisu cikin garin zema k'ara masa kud'i akan wanda ake biyanshi.

Tafiyar tasoma gajiyar dasu sanda aka taresu, wasu mutane masu furka a rufe da qyalle sa manya manyan bindigogi ne suka tare motar, take dulanin nam suka soma salati suma su Dawood suka hau yin salatin, duk inda kake kanajin qarar bundigar sanda wanin su ya harbata a sama, hankula sun matuk'ar tashi musamman twins dake tsammanin wahalar su ta k'are ashe ashe tsugune bata gama k'are musu ba!!!! Sunfi 4 hours suna binciken su snin hanyar bame bi ba soja ba 'yan sanda kafin daga bisani su soma shirin barinsu anan suna qoqarin tafiya da motar cikin jeji sabida dama kayan amfanin ginar suke so, da kudad'en dasuka zo dashi, Abu Hurairane ya shiga musu magiya akan su taimaka su barmusu motar, yaya zasu bar wannan *Doguwar hanyar* idan babu mota dan Allah su taimaka......aikam take agun wani daga cikinsu Ya dage bundigarsa ya danna masa harsshi take ya xube agun kowa yae tsit se Abu sufyan daketa faman kuka yana rik'e dashi, suna kallo suka bar wurin bayan har wayoyinsu sun karb'e suka kuma tafi da motar, cikin azaba Abu huraira ke mayar da numfar fashi sama sama, sauran se kuka suke Abu sufyan cikin kuka yace

"Daddy kana inane haka? Gashin mun shiga halaka ka turomun wannan *Doguwar Hanyar* mara b'ullewa, daga wannan bala'in se wancen Allah ka kawo mana d'auki, Allah ka ceci ran d'an uwana ya Allah, kowa kuka yakeyi cikin tashin hankali....

*Littafina na kud'i ne idan baki biyaba karki karanta, idan kinaso seki tuntub'i wannan lambar 07084161619*

Mom Nu'aiym
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

*Littafina na siyarwane idan kanaso ka biya ka karanta  idan karantamun littafi baka biyaba kaida Allah, idan ma biyan kai kayi sharing kaida Allah. Me buqatar biyar litattafanmu ya tuntubi wannan lambar 07084161619*

    10

Haka ya dinga zubar jini yana juyi agun, lawuri ta kalli Barbo tace da ita cikin yarensu

"Yana zubar da jini da yawa, naga kaman akwai ganye aja anan wurin da sauri ki tsinkamun" Batare da Barbo tayi magana ba ta juya da gudu cikin jejin, seda ta had'o ganyaye kusan uku sannan ta dawo, ba wani ruwan dazasu wanke ganyayen hakla ta murje ganyayen da hannunta ta ta kama k'afar da aka harba ta cura su tana nan manne da wurin sesa taga jinin ya dena zubowa, sannan abu sufyan ya qara yagar rigarsa aka d'aure k'afar

"Mubar nan wurin, nizan goyeshi, mu taimaki kanmu kar daren
yae mana anan, bamusan mezai faru ba" Driver kuwa kallon su yae yace da hausarsa ta fulani

"Sa'a suka samu daganan zuwa cikin gari ba wani nisa, ko'a mota befi mana saura mintuna 25 ba, sunsan kota bata zuwa k'auyen nan se bisa tsautsayi dan haka mutaka, bana tunanin nanda awanni biyu ma bazamu isa koma qasa ga hakan" jinjina kai dawood yae

"Bakajin dad'i abokina, barin goye shi idan na gaji ka tayani, ni asibiti nakeso mui rushing muje" shidai Abu Hurairah bayama cikin hayyacinsa azabar dafin billet daya ratsa shi kawai ya ishesa, haka suka rankaya Dawood yana goye dashi suka ci gaba da yankan doguwar hanyar, taimakon da Allah ya musu ma titine ba kwana ko shiga gona ko jeji bare ka b'ata.

***********
Sunyi tafiyar kamar awanni biyu kafin suka taradda babban gari anata hada hada, kai tsaye asibiti suka wuce dukda bame waya acikinsu babu kuma wanda yakeda ko k'wandala,wahala sosai sukasha akan sesun kawo police report kafin a karb'eshi daga k'arshe kuma akace baza'a musu aiki ba kud'i ba, a binciken da Abu sufyan yae kuwa garin dasuka sauka ko kusa beda alaqa da garin dasuke yanzu, tafiyace ta tsawon kwanaki kafin ka isa wancen garin dasuka baro kayansu kuma ATM card d'inshi yana cikin kayan sa, dama Na huraira ne suka fito dashi kuma ya b'ata tuni, ajakar dasuka baro k'auyen su Lawuri yake, dafe kanshi yae ganin yanda jini ke zubar masa cikin ma an tsare dana hausa gashi harya suma ma sabida azaba

"Dawood yanzu ina zamu samu kud'i anan? Yaya zamuyi ni kaina ya d'aure wlhy" kallonshi yae shima cikesa damuwa

"Bansan yanda zamuyi ba? Bansan wasu irin k'addarori bane marasa dad'i suke bibiyar mu, na rasa gano inda al'amarin ya dosa" shiru sukai dukkansu suna tunanin mafita

************
Sun tsaya da motarsu ganin jini akan titin, inda d'aya daga cikin sojojin wanda likitan soja ne shi ya Duba jinin, kallon general yae yace

"Baze wuce 3 hours ba da faruwar abun, abun kuma jinin na mutum ne" Nisawa yae cikin tashin hankali ya kalli dirensu yace

"Dama ana fashine anan?" Asuwakin dake bakinsa ya goga hak'waranshi dashi
Chapter 11 · 0% Book details