← Book details Deedeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 19

Sashe 8

Deedeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kano state.
Masarautar Kano
"Kee.. Daughter wait for your daddy" cewar wani kyakkyawan magidanci mai kama da deen sosai. Murmushi yarinyar tayi wadda bazata wuce 4years ba hannayen ta take miƙa masa tare da cewa "tautanni daddy" kai my little deenah cewa zakiyi "daddy daukan ni, kinji ko?" eh. Daukar ta yayi saman bayan sa suna zagaye filin gurin. "Au kunanan Kenan" cewar wani "ehhhhhhh," tajasa shi da tsawo sannan ta cigaba da cewa "abbu, momma, umma, Ina mamah da abba?" ta furta a shaƙwaɓe. Dariya sukai sannan umma tace "abba da mama sunji duba mararsa lafiya kinji daughter" ta furta cike da kauna. "babu wani basa sona dan haka Nima daddy, abbu, momma da Ummah nake so bana son su suma" ta furta cike da yarinta. Haɗe furka Ummah tayi tare da cewa "deenah waya ce maki basa sun ki? " shiru tayi batace komi ba. Deenah dake nake "umma na tace kada na faɗawa kowa" ta furta "wacece" ta furta cike da mamaki mai faɗawa deenah haka "ba Zaki faɗawa kowa ba" eh bazan faɗa ba. Pinking promise. Uhummm. Mama two "sarauniya hindatu" ta furta da mamaki "zata iya dan wannan fuska biyu gareta, shiyasa nace tabar barin ƴarta gurin ta, aigashinen tana son rabata da ƴarta tinda ita bata haifaba" cewar wata mata "gaskiya momma bana tinanin hindatu zata aikata hakan, amma bari naji ta bakin ta" ta furta tana barin gurin. "daughty Mike son muyi ƴanzu" cewar daddy "mu zagaye house ɗin nan" cewar deenah "kai daughter Baki tausayin momman ki ko" cewar momma tana dariya. "a'a gaskiya daughter bata tausayin kowa Sai abbun ta" cewar abbu. Murmushi tayi tare da cewa "kudu ka" ta furta tana rugawa. Murmushi sukai suna bin bayan ta. Ganin har yanzu suna bayan ta yasa ta bin wata hanyar. Babu shiri mommah ta kwala mata gira saboda hanyar da tabin suma suna mara ta baya.
*************
Hankali tashe mai martaba da matarsa ke kallan ɗan sandan juna jiran mizece. Hankali chike da girmamawa yace "ranka shiɗade haryanzu munkasa mamun Inda suke ko wata makama. " ya furta. Da sauri abba ya riƙe mama ganin tana naiman faɗuwa. Kallan mai martaba tayi sannan tace "kwana uku kenan ace ba'a san inda suke ba, da wana idon zankali umma da har zance mata mijin ta tare da wanta{abbu} da ƴar uwar ta {momma}, sannan ƴata ɗaya tilo sun ɓace ba'a sannan halin da suke ciki ba " ta furta hankali tashe "innalillahi wainna'ilaihir raji'un allahunma ajirni fimusibatik wa'aklifli kaira mafiha" umma ta furta hankali tashe saboda taji abinda mamah tace. Maida kallon su sukai kan umma. Jiki a sanyaye umma ta nufu cikin parlour, lokacin guda umma tafara ganin parlour na juya mata, duhu na mamaye ganin ta. Ganin umma ta faɗi ƙasa sumammiya. Dasauri suka idaso inda umma take a sume "innalillahi, mai martab.........." kasa idasawa tayi saboda da jirin daya kwashe ta. Nan ta fadi itama sumammiya. Dafe goshin sa yayi dan yara sa ina saisa ransa. Da taimakon hadimai aka kai umma da mama ɗakunan su inda Dr ya dubasu. Kallan sa yayi, sannan yace" colm down Mai martaba suna lafiya "cewar doctor" Mike damun su? "cewar mai martaba" umma dai Bp din tane yahau Amma yanzu normal, hjy kuma damuwa ce "nagode doctor." ba komi aiki na ne "ya furta yana masa sallama tare da barin gurin. Jiki babu ƙwari abba yabar gurin.
Yau kwana shidda kenan ta ɓatan su momma duk inda ka zagaya cigiyar su ake da kuwa ne kafufin sada zumunta. Inda su abba kullum ke cikin zaman tsanmani wanda a yanzu abba ya daina zaman fada. Suna zazzaune kamar kullum. Bakin sa dauke da sallamah yashigo. Inda ya gaida mai martaba "barka Cp Kamal" cewar abba "mai martaba mun samu nasarar samunsu" cewar Cp Kamal. Dasauri abba, mama, umma suka miƙe suna cewa "ina?" suka furta a tare. Shiru Cp Kamal yayi sannan yace "Aminu Kano" ya furta "Aminu Kano" suka mai - mai ta "lafiya dai" cewar abba "lafiya lau idan munje kun gani" cewar Cp Kamal babu musu suka fito inda suka shiga cikin motar tare da barin gidan.

***************

AMINU KANO

fitowa sukai daga cikin motar inda Cp Kamal yace "nuje". Shiru abba yayi saboda faɗuwar gaba da yake ji ba tare da yasan dalili ba "muje mai martaba" cewar mama. Murmushin ƙarfin hali abba yaƙirƙiro saboda gudun tadama su hankali. Jiki a sanyaye abba ke tafiya wanda duk takon da zaiyi faɗuwar gaban na ƙaruwa a dai-dai bakin emergency Cp Kamal ya tsaya. Kallan sa sukai inda abba yace "ina suke?". Shiru Cp Kamal yayi sannan yace "sorry to said Allah ya karɓi hjy Halima saidai muyi mata fatan dacewa, alh. Sa'ad da alh. Abbakar suna cikin emergency tare da ƴarinyar saidai muyi fatan nasara" cewar Cp Kamal."innalillahi, innalillahi, innalillahi" shine abinda abba keta maimaitawa "Ta yaya hakan ta faru" cewar abba atsawace yana kallon Cp Kamal Sannan ya cigabah da cewa "ina kuga same su?" shiru cp Kamal yayi sannan yace "kwara, motar su tayi accident. Inda.... " hannun mai martaba ya ɗaga masa indanunsa sunyi jajir, jijiyuyin kansa sun baiyana. "ina sa'adah, zarah da Muhammad" cewar wani doctor daya fito daga emergency. "gamunan" cewar mama dan abba da Ummah kasa cewa komai sukai "ok, kushigo dan majin yacin baida isassan lokaci, Sannan ɗayan Shima Allah yakarɓe abinda. " ya furta yana komawa. "Dammmm" xuciyar abba ta tafaɗi. jiki na rawa suka shiga. Ganin Daddy da abbu kwanci cikin jini ba ƙarami daga hankalin su yayi ba.
VAVYMK

MARYAM A HADI

💫𝑫𝒆𝒆𝒅𝒆𝒆𝒏💫

PAGE 26-27

Not edited

Bismillahirrahmaninrahim da sunan allah Mai rahmah mai.
Chapter 8 · 0% Book details