← Book details Deedeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Deedeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kallan ta yayi sannan yace "fito munzo" ya furta a takaice. Babu musu tafita sannan suka shiga cikin mall din.Kallan ta yayi tare da cewa "take what ever you want". Kai kawaii ta girgiza masa sannan tai gaba yana binta a baya. "hiii beautiful Arab" cewar wani kyakkyawan matashi kallan sa tayi tare da kauda kanta. Murmushi yayi tare da cewa "haba beautiful Arab wannan izza haka" ya furta haryanzu fuskar sa dauke da murmushi. Gaba tayi abin ta gani hakan yasa matashin bin bayanta yana cewa "ok, bari na taya ki shopping mana my beautiful Arab" ya furta yana ansar basket din hannun ta. Banza tayi ta dashi sannan tai gaba abin ta ba tare da tabi takan saba. Murmushi yayi dan hakan da take yi ƙara birgesa take yi. Nan deenah tashiga shopping Wanda wannan matashi nah riƙe da kayan ta. Kallan sa tayi tare da miƙa masa hannun ta ba tare da cewa komi ba.. Murmushi yayi sannan yace "haba beautiful Arab aiƙya bari nai Maki Rakiya" ganin da gaske wannan mutumin ɓata mata lokaci zaiyi ga deen na jiran ta yasa ta fisge basket din tayi gaba abinta. Bin bayan ta yayi yana kwala mata kira. Ganin deen tsaye a reception tsaye. Da sauri deenah ta idasa gurin sa tana kallon babbar teddy bear pick color Sannan tace "this teddy far?" ta furta idon ta nakan teddy din Dan ya burgeta. "it's for you" yace fuskar dauke da fa'a duk da cewa ba murmushi yake ba. Really? "yeah" ya faɗa yana miƙa mata. Ansa tayi tana murna. Kissing din kumatun sa tayi tare da rungume sa sannan "I love you so much my dearest uncle tajuddeen, I really appreciate your gift. " ta furta tana kuma rungume sa. Wani irin shock deen yaji tinda kansa har zuwa tafin ƙafar sa. Babu shiri ya janye ta daga jikin sa. Kallan ta yayi sannan yace "mikika ce" cewa nayi ""I love you so much my dearest uncle tajuddeen, I really appreciate your gift. "mi hakan ke nufi?. Godiya mana. With hugging ?. Eh mn haka nakewa umma. Murmushi yayi fahimtar wannan ɗabi'ar tane." with everyone haka kike masu "ya idasa fada yana yin fuskar sa na sauyawa. Kai ta girgiza masa alamar a'a, sannan tace" umma said I can only do it with my family members ". Baice komi ba sai miƙama reception card din yayi. Kallan teddys din tayi sannan tace" deen it this teddys all mine? ". Kallan teddys din yayi sannan yace" ko kina son many ne "girgiza masa kai tayi alamar" eh"murmushi yayi tare da kama hannun ta zuwa gurin teddys din. Sannan yace "take anyone you want" babu musu deenah tashiga daukar teddys. Da mamaki deen ke kallan ta dan almost duk wani teddys take gurin ta dauka. "hey, what will you do with all this stuff" ya furta. "yeah mine, anty jawaheed and the r rest for the orphanage children. " shiru Yayi dan harga Allah titanin deenah da halayan ta suna birge sa duk da rashin jinta. "hey beautiful Arab" cewar wannan matashin yana ida sowa gurin su. Deenah na ganin sa ya nayin fuskarta ya sauya. "why beautiful Arab ki katai with out saying bye bye." ya furta idon sa kan kyakkyawar fuskarta. Deenah shiru tayi tana satar kallon deen ta ƙasan ido. Ganin hankalinsa nakan abinda yake da phone dinsa, bata su yake ba. Yasa hankalin ta kwantawa dan yanzu ta rasa miyasa bata son deen yaganta da wani guy. Abinda deenah bata sani ba cewa duk abinda take deen na kallan ta ta gefen ido. "why dan Allah kake ta bibiyata" ta furta fuska a daure. murmushi yayi sannan yace "please your phone number" banda ita. "you don't have phone number" ya furta da mamaki. Is there any problem ne. Girgiza kansa yayi alamar "a'a" sannan yace "ohk, tell me your area". City view estate. Dan Allah idan babu damuwa which school are you?. AJB international school. To zan iya driving dinki.? Kallan deen tayi wani irin murmushi mai wiyar fassarawa na baiyana a kan fuskar ta sannan tace "sorry ina tare da husband dina." husband "ya mai maita da mamaki. Murmushi yayi na rainin hankali kafin yace" where is your husband? "ya furta da yaƙinin ƙarya take" gashinan "ta furta tana nuna deen. Kallan deen yayi wanda fuskar sa take daure wanda ya ƙara masa ƙwarjini. Dauke kallan sa yayi daga kallan deen ya maida kan deenah sannan yace" gaskiya you are lieing this should be your dad or brother ". A hankali cike da izza deen ke kallan sa from head to toe dan duk Wanda ya gansa yasan bai wuce yabasa one to two years ba Amma yake cewa wai dad dinta ne. Ba tare da yabi takan suba yayi gaba abinsa. Ganin hakan yasa deenah cewa" ƙalbi, ƙalbi, ƙalbi "tamai maita kiransa tana bin bayan ta. Reception yatsaya tare da biyan kudin sannan yafita ba tare da daukar kumi ba. Babu shiri deenah tabi bayan deen da gudu. Saiji yayi ta haye bayan sa ta maƙalƙalesa da ƙarfi. Tana cewa" my dearest deen my teddys "ta ƙarasa faɗa tana kwantar da kanta bisa ƙafaɗarsa. Murmushi yayi ganin yadda tayi saboda bata ga an fito da teddys dinba. Ƙara narkewa tayi a bayan sa sannan tace" nidai my chocolate da teddys "ta furta a shagwabe. Girgiza kai kawai yayi sannan yanufi mota. Ganin hakan yasa deenah saukowa. Kallan ta deen yayi sannan yace" shiga mutai "fashewa da kuka tayi tare da faduwa ƙasa tana birgima. Da mugun mamaki yake kallon ta dan ko a mafarki aka ce zatayi hakan zaice a'a." kee...!!! "ya furta fuska a daure. Ganin hakan yasa deenah ƙara sautin kukan ta. Ganin da gaske tara masa mutane zatai yasa ya saɓeta. Dukan bayan sa tashiga yi tana cewa" My teddys "buɗe Ƙofa yayi tare da sata. Sannan Shima yashiga. Kallan ta yayi tare da cewa" ki nutsu konai maki dukan tsiya". Hakan kuwa ƙara ingizata yayi. Ganin tana niyar fita yasa ya sanya motar lock. Bata bi takansaba ta cigaba da kukan ta tana dukan Ƙofar. Tsittt tayi Jin deen ya hade bakin su guri daya. Nan tafara turesa amma kamar ƙara ingiza sa take yi dan ko mutsau bai mutsa ba haka ta hakura ta ƙyalesa. Jin tayi shiru yasa ya cire bakin sa. Kallan ta yayi ganin tayi lamu Kamar babu ita cikin motar murmushi yayi tare da cewa "iya nan tsiwar ta tsaya" ya furta yana danne dariyar dake cinsa saboda yadda take ta raba idanu. Banza tayi dashi. Shima bai kuma cewa komi ba yaima motar key suksbar gurin.

*************

City view estate.

horn yayi inda gate man yabude masa gate din. Parking yayi a parking lot. Kallan deenah yayi Wanda tayi lamu a seat kaiba kace deenar da tagama kuka bace murmushi ne yasu buce masa sannan yafita tare da za gayuwa ta gurin tare da bude mata Ƙofar yayi sannan yace "fito" sumimi sumumi tafito Kamar wata muna fuka. Sannan tafara tafiya ganin yadda take tafima kamar marar lakka yasa ya kama hannun ta. Bakunan su dauke da sallamah suka shiga. Fuska dauke da murmushi mommy ta ansa masu. Gaida mommy sukai inda deen ya zauna kusa da kabir. "sannu bro, ya hanya" cewar kabir "ban sani ba, shine yau baka jeba ko" murmushi yyi tare da cewa "oh, ka sakko Kenan kura da hali kaiman fah" ya furta fuskar sa dauke da jin dadin cewa deen ya sakko. "anty jawaheed ina wuni" cewar deenah wanda tai lamu ajikin mommy. "lafiya lau ya jikin" cewar jawaheed. Alhamdulillah. Lafiya na ganki haka kinyi shiru"Bah deen bane yyi kissing ɗina a Mota," babu shiri deen ya ƙware da ruwan da yake sha. Mommy jitai kunya ta kamata. Jawaheed kuwa toshe bakin ta tayi da hannu gudun kar dariyar da take riƙewa ta fito. Kabir kuwa kallon wautar deen yyi. "to yanzu shine ƴata ki kayi shiru" cewar mommy "eh mn, umma fa tace babu kyau haramun ne". Ta faɗa a shagwabe. Deen kuwa jinjina irin yarintar deenah yake saboda wani lokacin idan tai wani abu Saika dauka batai makaranta ba. "deenah to miye haramun nan naga uncle deen mijin kine?" cewar jawaheed." Taya yazama Mijina "ta furta tana barin gurin.

*************
Chapter 5 · 0% Book details