← Book details Deedeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Deedeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Murmushi tayi tana lafewa jikinsa. Dr where are you going. Home. But Dr.."hannun ya ɗaga masa. Tare da ficewa daga ɗakin." deen "Jin an ambaci sunan sa da muryar da ya sani yasa shi juyawa dan tabbatar da abinda yake ji. Nabila ce tsaye tana kallan sa. Jiyayi gaban sa ya fadi dan harga Allah baiso nabila tagan sa dauke da deen koda kuwa sunji faɗa." wow deen "ta furta tana tafi sannan ta ci gaba da cewa" wato ka samu yarinya mai mai aji ko? "shiru Yayi dan baiga abinda ya kawo wannan maganar ba tinda a hospital ta gansa ba wani guri ba. Murmushi tayi tare da cewa" dole kai banza dani tinda na gama maka anfani ko?, gani shashasha? ". Haryanzu deen baice komi ba kallan ta kawai yake yi. Babu shiri ta daukesa da mari ji kake" tassss.... "jin marin yasa deenah sakkowa daga jikin deen din. Hannun ta takai gurin da nabila ta maresa ga sahun hannun ta raɗo - raɗo abinka da farar fata. A fusace ta juyo tana cewa" kee, wata irin shashasha ce, ballagaza, wawiya, jahila da Zaki Mari mijinki ko ce maki akai zina yake ko kama shi kikai yana yi da zaki marai bare koma ba ita yake ba, ko uwar ki bata koya maki tarbiya bane mare kisan ƙima da darajar mijin ki bane, haba dan Allah ke yanzu ki gansa a hospital ai ƙya tambaya ko lpy amma kawai saiki maresa? "ta furta A Fusace." kutumar ubancan, ni Zaki tambaya saboda mi namari Mijina "ashe ban taɓa sanin jahilcinki yakai haka ba. Durun uwa, ni kike kira da jahila. Eh jahilar first class ce. Ihu na nabila tayi wanda yasa hankali kuwa na gurin kuma kanta." Kee lafiya kikema mutane ihu a hospital?, please akwai majin yata a ciki." cewar deenah. Gadan - Gadan nabila ta nufu deenah tana ihu kamar wata zautatta "nabila karki kus kura ki taɓa man matata dan wallahi a bakin auran ki" turus nabila tayi danji tayi kamar saukar aradu dan kuda wasa deen baitaɓa ce mata hakan ba bare ace mata yayi wannan furucin. Deenah ta buɗe baki kenan deen yace "deenah mutai" kallan sa tayi sannan tace "ba zaka ramaba" ta furta "eh mutai" ya furta yana janta suka bar gurin. Nabila kuwa faɗuwa tayi a gurin tana ta kurma ihu kamar wata sabuwar ma haukaciya. Nanfa mutanen gurin suka fara cecekuce inda dayawan mutane ke ganin laifin nabila musamman ma wanda suka ga lokacin da nabila ke marin deen. "lafiya nake jin ihu" cewar Dr meerah. "Dr kinganta can" ta furta tana nuna nabila. Da mugun mamaki Dr meerah ke kallan nabila dan ta gane ta. Kallan wanda tai maganar tayi tare da cewa "sis Asiya Mike damunta? ". Dr. Ina wannan babban Dr din wanda yake shikin manyah manyan masu faɗa aƙasar nan shifa Tamara. Waiwah?. DR. TAJUDDEEN SA'AD SALIS mana Wato Dr. deen. What taya.? Nantakwace komi tafaɗa mata tare da cewa "gaskiya Dr nayarda cewa da akeyi yana da mutunci dan wallahi idan wani ne saidai wani babin nata." "To aita din matar sace" cewar Dr meerah. Mata fa kuma har tana iya marin sa cikin mutane komi yayi mata bai kamata ta maresa ba cikin mutane sannan ai a hospital ta gansa ai ta tambayi lpy. Amma najinjina mata da ikon marinsa, tayi dace data samu irin namijin da zata mara yabar ta , gaskiya shi din ɗaya ne tamkaar dubu. Ko kina son sane? Na Isa. Dadai yafi maki dan duk wannan haukan da take yi saboda mahaifiyarsa ta aura masa wata. Eh lallai. "To ai saboda irin haka da take masa kamar Danta yasa aka aura masa waccan. "ta furta tana kiran security tace" kufitar mun da ita daga hospital din nan "tana gama fadi tawuce.

" hubbies ya kuke gani, shin abinda nabila tayi daidai ne ko a'a, kishi ne kuwa, muji ra'ayoyin ku a comments section "

*************

Kallan deenah yayi wadda Tunda suka shigo ta haɗe fuska. Murmushi yayi dan aganin sa nabila kishine yasa ta maresa. Amma baiga dalilin da yasa deenah yin fushi da shi har haka ba saboda ya hana ta biye wa nabila. Maida kallon sa yayi kan driving da yake kana ya furta "mata" shiru motar tayi. "deen miye Durun uwah" ya tsinkayi muryar deenah da furta hakan. Babu shiri yaci birki dan tambayar tazo masa a bazata. Kallan ta yayi wanda itama Shima take kallo. "why did you ask" ya furta yana son kaucewa tambayar da tayi masa. "to ai bansan mi waccan matar taka take nufi da hakan ba." Daure fuska yayi kamar bai taɓa dariya ba sannan yace" karna ƙarajin wannan kalmar a bakin ki ". Ganin babu alamar wasa a tattare da shi yasa tace" toh"bai kuma cewa kumi ba ya tada mutar. "mikike so? " yafurta. "new teady bear da chocolate" Murmushi yayi baice komi bah. Ya cigabah da driving. Jin deenah nabin karun alqur'ani maigirma Cikin lafazi Mai daɗin ji. Kallan ta yakeyi cike da birgewa dan duniya yana son yaji ƙira'a mai dadi wanda hakan yasa yaso nabila komawa lslamiya Amma taƙi. "taya kika iya ƙira'a?" ya tambaya "Islamiyya" ta bashi ansa "izihinki nawa" ya kuma tambaya "sidtin" ta furta ba tare da sanin dalilin tambayar ba. "saukar ki nawa?" shiru tayi sannan tace "uku" da mamaki yaki kallan ta. Bai kuma cewa kumi ba. Parking yayi a dai dai wani katafar mall. Kallan ta yayi sannan yace "fito munzo" ya furta a takaice. Babu musu tafita sannan suka shiga cikin mall din........

VAVYMK

VAVYMK

MARYAM A HADI

💫𝑫𝒆𝒆𝒅𝒆𝒆𝒏💫

PAGE 18- 19

My WhatsApp group

https://chat.whatsapp.com/JKiBagO4i0lDaIXRQDAxEA?mode=wwt

Bismillahirrahmaninrahim da sunan allah Mai rahmah mai.
Chapter 4 · 0% Book details