← Book details Deedeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Deedeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Around 6:00pm tashigo gidan ." deen ya dawo? "ta tambayi mai aikin." no madam but yace ki girka masa shrimp "
ok" ta furta tana wucewa bethroom dinta. Kayan jikin ta ta rage tare da shiga bathroom. Saida tayi 15 minutes Sannan ta Fito tare shiryawa cikin riga da wando na Dior ash color Sai hula ash ta saki gashin Wanda tsawan sa har zuwa mazaunan ta. gashi baƙi wilik Sai daukar ido yaki. Fitowa tayi Inda direct kitchen tayi. Kasan cewa masu aikin ta duk mata ne bbu maza. "hjy wannan wankan fa" cewar wata dattijuwa sanye cikin uniform na masu aiki. Murmushi tayi tare da cewa "iya delo wannan ne wankan" ta furta tana dariya dan ita dai tasan normal shigar tayi ta yau da kullum. Itama iya delo dariya tai sannan tace "Allah hjy wannan wankan kyansa oga ya gansa" ta furta tana murmushi dan deenah nada faran faran da masu aikin ta wanda suma suke jin dadin aiki aƙar ƙashinta saboda tana jansu ajiki. A haka suka gama aikin yin shrimp din. Inda suka jera komai a dinning "iya delo ga shrimp din ku can tare da abincin dare" godiya iya delo tayi mata. Murmushi deenah tayi tare da barin gurin dumin gabatar da salla magrib. Tinda ta shiga daki sai bayan isha'i ta fito. Hjy barka da fitowa. Yauwa Halima Ina iya delo da Nana?. Suna salla ne. "ok" ta furta tana zama kallan halima tayi sannan tace "zoki zauna muyi kallan tare "ta furta tana murmushi. Bbu musu halima tazo ta zauna kan carpat. Daidai lokacin iya delo da nana na shigowa" hjy barka da dare "cewar Nana kasan cewa deenah ta hana su gaidata saboda duka ma aikatan ta sun girme ta." yauwa Nana, iya delo Ina wuni "cewar deenah tana maida Hankalin kan kallon da suke" lafiya lau hjy, koda abinda kike buƙa ta?. "a'a iya delo kuzauna muyi kallan tare tinda nasan kina son film din. Bbu musu suka zauna kan carpat" haba iya delo ku zauna kan kujera mana "a'a hjy nanma yyi. Ganin hakan yasa deenah sakkowa Saman carpet Kamar yadda sukai. Bakin sa dauke da sallamah ya shigo da sauri deenah ta miƙe tana cewa" baban ammi ka dawo? "ta k'arashe maganar tana idasawa gurin su." gaskiya da sakal babanah kawai aka sani banda ni '' ya furta yana tsare ta da kallo, dan shigar ta birgesa. Murmushi tayi tare da cewa "sorry daddy'n babanah" ta furta tana ansar as-sadeeq "mikuke kallo haka naga kowa a ƙasa?" kallo muke nayi nayi su zauna kan kujera amma sunƙi shiyasa Nima na zauna cikinsu. Dariya deen yyi tare da cewa "iya delo dan Allah ku daina zama ƙasa"
"to yallabai" suka furta suna naiman fita "a'a iya delo karmi haka dake kikoma ki zauna kuyi kallan ko" to. Bari in watsa ruwa. To Nima bari naima babanah wanka ta furta ta wuce bethroom din ta. shima haka. Ganin hakan yasa su iya delo komawa su zauna. Bayan mintina 15 deenah ta fito dauke da as-sadeeq wanda aka shirya tsaf cikin kayan barci zama tayi cikin su. Suna Cikin haka deen yafito tare da nufar dinning. Mikama Iya delo as-sadeeq tayi tana nufar dinning. Serving dinsa tayi tare da ɗibar wani a flat Sannan ta koma ta zauna parlour. "iya delo ga snacks" ta furta tana daukar samusa daya tana Mika masu suma su dauka. Dauka sukai sanin yanzu da sunce a'a. Zata daina kula su. Haka suka ci gaba da kallo har deen yagama Shima yadawu parlour ya zauna gefan deenah yana jin gina da kujera miƙewa su iya delo sukai suna masu saida safe. ah'ah, tafiya Zaku tafi?. Eh hjy saida safe. Halima gobe ki cewa ado nace yazo ya hada mako kayan kallo. "To hjy mungode" suka furta suna barin part din. "deenah" yakira sunanan ta. Kallan sa tayi ba tare da tace komi ba. Ganin hakan yasa ya cigaba da cewa "nabila ɗazu tayi min magana kan na baki hak'uri kishi ne yasa tai hakan, sannan zata je taba umma haƙuri itama, sannan ta naimi da na dawo da ita amma nace muddin kika haƙura zan maido ta, Idan kuma baki haƙura ba zan bata hukuri kan bazan mai dutaba" ya ƙara shen Yana kallan Yana yin furkar ta. shiru deenah tayi tana tunanin "idan ta hana deen dawowa da matar tayi adalci tinda tare da gansu sannan komi tayi ai saboda san da take masa ne, sannan tinda har tace yaba umma hukuri ai shikenan ita bata da matsala da dawowar ta" wanda duk cikin ran ta take yi. Kallan sa tayi tare da cewa "bbu komi ni dama ban iriƙe ta ba nayafe mata deen ka dawo da matar ka. Dama ni kawai kan abin da taima umma yasa nake jin haushin ta amma tinda tace zata bama umma haƙuri ya wuce koma ta gane kuskuren ta " ta furta tana kallon as-sadeeq dayai barci ajikinta. Shiru yyi yana nazarin kallaman ta Wanda yasa deen ƙara jin kima da darajar deenah sun ƙaro a idansa. Saida safe tai masa tare da wucewa bethroom din ta. Kwantar da as-sadeeq tayi tare da yin shiru saboda yadda taji gaban ta na faduwa ba tare da sanni dalilin hakan ba. Addu'a tayi tare da ruƙan Allah komi nene dalilin faduwar gabanta yatsareta daga shi tare da sauwaƙa mata ko minene sannan ta kwanta.

VAVYMK
VAVYMK

MARYAM A HADI

💫𝑫𝒆𝒆𝒅𝒆𝒆𝒏💫

Page 40-41

Bismillahirrahmaninrahim da sunan allah Mai rahmah mai.

Tinda sassafe ta farka tare da yin duk wani aikin gidan tare da taimakon ma'aikatan ta saida suka gyara gidan tsaf duk da baya buƙatar gyara amma hakan suka gyara sa. Sannan suka shirya breakfast. Saida taga duk wani aiki angama sannan ta shirya as-sadeeq sannan tai wanka ta shirya ganin har 6:35am kuma tana da exam 7:20am yasa ta kallan Nana tana cewa "Nana shirya duk wani abu da as-sadeeq zai buƙata har zuwa ƴanma sannan karki manta da custard dinsa, kiyi sauri" ta furta tana sabar as-sadeeq data gama bashi abinci "amma hjy baki karya ba?. " nana wannan exam din nada mahinmanci Bana so nayi late a school,jeki dauko abayar ki. "ta furta tana barin parlour dauke da as-sadeeq sai bag dinta Acikin Mota Nana ta iske ta. Shiga tayi suna barin gidan zuwa School.

**************

DEEN POV

Bakin sa dauke da addu'ar tashi daga barci dan tinda ya dawu daga masjid yake barci zai yanzu ya farka. Parlour yafito yana kiran sunan deenah shiru. Iya delo ce ta ƙara so tare da yi masa barka da safiya sannan tace "yallabai hjy bata nan" ta furta cikin ladabi. Kallan ta yyi ido waje yana cewa "bata nan" ya furta da mamaki "eh, tace exam gare ta karfe 7:25am". Yanzu fa 6:55am, Ina as-sadeeq?. Dashi ta tai. Shiru yyi yana dafe goshin sa yyi tare da Barin gurin yyi ba tare da yace komi ba. Ganin hakan yasa iya delo koma wa bakin aiki. A gurguje ya shirya tare da yin breakfast yana barin gidan zuwa office.

***********

DEENAH POV
Kallan Nana tayi tare da cewa "ki kula dashi" ta furta tana shegewa exam hall ganin har 7:19am yyi. Nana A cafeteria tazauna kasancewa deenah tayi magana da shugaban makaranta. Sannin wacece ita sannan sannin Waye mahaifinta da mijin ta. Sannan daga familys din da ta fito yasa ba musu ya yarda wanda deenah bata san dalilin yarda ba. Tinda suka shiga exam 10:00am tafito saboda exam biyu tai. Direct cafeteria tanufa ida wasa tayi inda Nana ke zaune tanama as-sadeeq wasa. Zama tai tana mai numfashi dan tagaji sosai ga batai breakfast ba. Ansar as-sadeeq tayi tana masa wasa har lokacin komawa exam yyi ta koma. Haka deenah ta wuni suna exams kasan cewa exam shidda tayi na boko da Islamiyya kowane three. Sai gurin 6:00pm suka tawo gida. Kallan Nana tayi tare da cewa "kije ki huta "ta furta tana wucewa bethroom dinta. Inda taima as-sadeeq wanka tare da shirya sa, sannan itama tayi wankan ta shirya cikin riga da wando mararsa nauyi tare da gabatar da sallar magrib. Kwantawa tayi kusa da as-sadeeq dake barcin gajiya itama Bbu bata lokaci wani irin nan nauyan barci yai awanga da ita.

************

Bakin sa dauke da sallamah yashigo. Mamaki ne ya kama sa ganin parlour ba kowa kamar yadda ya saba idan ya dawo ba. "yallabai barka da dawowa" ya tsinkayi muryar Halima da furta hakan. Ba tare da ya ansa gaisuwar ta ba yace "ina madam take?". Tana ɗakin ta, tana barci. Tin yaushe?. Tin lokacin sallar magrib da tashiga bata sake fitowa ba. Taci abinci da ta dawo?. A'a. Ba tare da yace mata komai ba ya nufi bethroom din deenah. Murmushi yyi ganin yadda take duƙunƙune gurin daya. Kyara mata kwanciya yyi yana rufe ta da duvet kasan cewa ta lilliɓe as-sadeeq. Addu'ah yyi masu tare da barin bethroom din. A haka deenah ta cigaba da Exam din tana kula da as-sadeeq. Harsu ka gama exam din su.

************
Chapter 18 · 0% Book details