← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 21

Sashe 9

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin ta buɗe ƙofar yasa ya haɗiye ragowar abin da yake son furtawa ga wani ƙamshi da ya fito daga ɗakin ya daki Hancin shi, d sauri ya miƙo mata wayar, garin karɓa jikin ta na rawa dan ba ƙaramin kwarjini ya mata ba da ta ganshi daga shi sai vest Sai dogon wando baƙi sai da taji Abu ya tsirga mata hakane ya haifar mata da rawar jiki, garin karɓa wayar ta kusan faɗuwa a tare shi da ita sukayi rige_rigen kamo wayar, shi besan lokacin da ya kamo hanun ta ba ya haɗa da wayar dan bala'e sai da ya iya banbance laushin hanun ta da wayar, atake yaji wani spark ya shige shi fiye da na wutar lantarki, itama saƙon yaje Mata da sauri ta janye hannun ta, kusan a tare suka ɗago suna mai da ajiyar zuciya, wani kallo ya bita dashi kallon da beyi shawara da zuciyar shi ko ra'ayin shi ba, shi dai kawai yaji ya ƙafe ta ido, sai da ƙyar ya ƙaƙalo magana daga maƙogaron shi ya firta a wahale ...

"kisa a kawo miki caza ki dan inason yin amfani da nawa".... Sai yaji dama, dama cewa yayi kar ta kara bashi caji.

Juyawa yayi yana lumshe Ido, ssi yaji tace.

"umm me za'a dafa ma?"

Be juyo ba be kuma tafi ba sai ji da yayi ya kasa ɗaga ƙafar shi yana mamaki, Wai yau shi ake tambaya me za'a dafa ma? Sai dai kash! yaso ashe Auren so sukayi da ko ita ze iya ba zaɓi Amman yanzu shi ko yunwar ma baya ji, gashi baya so su sake samun kusanci har asamu akasi irin na yanzu.

Da sauri yace "a'a ki barshi kawai Kedai ki dafa iya naki" yayi saurin shigewa ɗakin Shi ya rufo ƙofa yana sauke ajiyar zuciya.

Itama kasalaliyar ajiyar zuciya ta sauke, sanan ta samu ta ɗaga ƙafar ta zuwa ɗaki tana cewa ta huta da girki ita ya taimaka ai, ita ko noodles ta dafa Itaji yunwa.

Sosai taga kiran da aka jera mata ya sake ƙular da ita yaga anata kiran ta Amman yaƙi kawo mata wayar ta dan wulaƙanci, kiran Abeed ta fara bi har ta katse be ɗauka ba ta sake kira shima be ɗauka ba....

_Hajiya & Suhai_

"suhail ni nake maka magana kake bani amsa kanka tsaye? Dan ubanka har kayi balagar da zaka fara sa'in sa da ni? To wallahi kayi kaɗan baka kai ba tukunna har ƙwaya nawa kake ina abun yake?" hajiya ce take sirfama suhail masifa da ta samu ya buɗe ɗaki ta shiga ta rutsa shi.

" Nifa ba sa'insa nake dake ba, abun da kike yi ne sam be dace ba ina kin rasa mai gaya miki gaskiya Nifa dole na gaya miki.... "suhail be gama rufe Baki ba, yaji saukar lafiyayun yatsu biyar a kumatun shi.

Wani mugun zabura yayi a zuye ya taso yana huci kamar ze rama ta zaro ido, a firgice da ƙar ta aro jarumta tace" Ko Ramawa zakayi ne? Fitsarare mara kunya ni kake gayama magana haka, kai har ka kai ka sauke ni daga godaben da nake kai? " wayar suhail ce ta fara ringing da take kan bedside drower, karaf idon ta ya kai kan sunan da take zargi na wacce tafi tsana ne a rayuwar ta, ta duniya, sai ko takai hannu zata ɗauki wayar dan tabbatar da zargin ta sai kawai yayi saurin ɗauke wayar, yana huci, da sauri tace "waye me kiran ka bani wayar" lokacin da aka sake kiran a karo na biyu, ganin baze iya kokawa da ita ba dan yana ganin girman ta, kuma baze iya bata wayar ba sai kawai ya figi makullin motar da ta ara mai ya wuce da sauri ta gefen ta ya fice ya barta a ɗakin tana ta baloƙoƙo kamar zata tsine mai dan ya kai ta kusa da bango yau.

Yana fita ya shige mota ya tada ita a zuciye dan beƙi komai ya faru da shi ba a irin fitar da yayi, da ƙyar ya iya kiran wayar da aka kira shi be ɗaga a gaban hajiyar ba dan yasan baida wanan damar, kuma shi ya fara kiran number da sauri yaji an ɗaga "hello Abeed! Suhail kanajina?"

Sai da ya fesar da hucin bakin shi ya iya amsawa "ina jinki a ina gidan ki yake?"

"gidan nan ne da dadi ya taɓa bada hayar shi har yake cewa ze barma Habu Driver in ka tuna, nidai kasan bansan gidan ba Amman Naji mum da ƙawar ta suna maganar gidan ana gobe za'a kawo ni" ƙwafa yayi kafin ya sake cewa..

"shine dan zalunci ta bari aka saki a gidan ko? Any way Ganinan Zuwa hope Dai maigidan Ki Yana nan ko? Dan ina son ganin shi"

Da sauri jumana tace "a'a suhail meye abun zalunci kuma? Zaka fara ko, kabari dan Allah, eh yana nan, najika wani irin dan Allah ka....." be bari ta ƙarasa ba ya kashe kiran yana jin ranshi na mai zafi, ya rasa gane wacce uwa Allah ya bashi.

_Ajmal and jumana_

Sosai hankalin jumana ya tashi ta rasa yadda zatayi tasan baze wuce shi da hajiya bane, gashi ita bata son tashin hankali yaushe ta rabu da na gidan da tun tasowar ta a horo take da hukuncin laifin d bata aikata ba, gashi tazo gidan Auren da bata san makomar ta ba ga suhail ze sake kawo mata wani ciwon kan dan besan dalili da yasa zeyi magana da mijin da ko maganar minti biyar cikaki basu taɓayi ba, kuma gashi yana nema yasa dole sai ta mai magana kuma shima ba mai son yin magana bane ta lura, dan haka hankalin ta in yayi dubi ya tashi sai zirga zirga takeyi ta kasa zaune ta kasa tsaye har kiran suhail ya shigo wayar ta, jikin ta na rawa ta amsa, yace mata yana ƙofar gida., tace "to Ganinan zuwa"

Da sauri ta fito falo ta rasa yadda zatayi, gashi tana son yin magana da shi dan ya fahimce ta da kuma sanin waye suhail Gashi yace zeyi magana dashi, dan bata san shigo da shi ba tare d ta sanar mai ba.

Ƙofar ɗakin taje, ta kasa bugawa sai zata buga sai ta kasa, gaba ɗaya ta rikice, sai da suhail ya sake kira yana cewa "ko na tafi ne, kin shanya ni" da sauri tace "aa yi haƙuri Ganinan fitowa"

Jin ana waya kamar a ƙofar ɗakin shi, yasa har ze fita sai ya fasa, sai yaji an bika mai ƙofar, yasan dai babu kowa a gidan sai shi da ita, abugu na biyu ya taho ya buɗe ƙofar yana daga gefe.

Be ce mata komai ba kamar yadda itama ta kasa ce mai komai, sai wasa da yatsun hanun ta da takeyi, tana sunkuyar da kai tana mele fuska kamar mai shirin yin kuka.

Shiko Har ya fara harzuƙa "in baki da abun cewa zan koma"

Dagowa tayi a sukwane suka haɗa ido, sai kowa yayi saurin janyewa "umm Dama suhail ne yazo yana waje"

"and so? Kina Bata min lokaci"

"yi haƙuri shi ɗin babamu ɗaya dashi nasan baka san shi ba kuma dama...." sai ta fara inda inda

Sai yace "dama me? Ba gidan ki bane kina da damar kawo kowa ai meye nawa a ciki sai da safe..." ze rufe ƙofar tayi sauri ta tare,

"to yace zeyi magana da kai ne dan Allah shine nace barin gaya ma" tana suke idanun ta da hawaye suke shirin sauka kuma ya lura da kamar a rikice take duk da ko tausayin ta beji ba, Amman sai yace, "to ina jiran shi in ya shigo ɗin, ko akwai wani abu ne kuma?" ganin ta tsaya ta kasa tafiya kuma ta kasa magana bare ta ɗago ta kalle shi.

"juyawa tayi da sauri ta fita dan shigo da shi tana share hawayen da suke shirin zubowa.

Ajamal ko ɗaki ya koma.

Bayan ta buɗe ƙoafar gate ɗin ta fita same shi acikin mota.tace wajen mota ta ce.

" Abeed bisimmillah"ta faɗa tana buɗe Mai marfin motar da ta ganta a rufe kuma ta gane ta gidan su ce tana mai murmushi ƙarfin hali.

"hmm ai da tafiya zanyi dan har na tada mota Salman ya kirani muka gama magana da tuni na tafi tunda naga kamar kin sami ƴanci abinki Ni kin barni a cikin...." bata bari ya ƙarasa ba tace

"haba bro Abeed yi haƙuri abu na tsayayi kasan bazan barka kayi ta jira na ba, yi haƙuri fito mushiga dan Allah, kaji? fito na rufe ma motar" sai yaji ta bashi tausayi, ya fito ta rufe motar suka shiga ta kulle gidan tana gaba yana Binta a baya yana kallo gidan yana taɓe baki har suka ƙarasa falon,

Ko da suka shiga ma bakin ya sake taɓewa,gani yake gaba ɗaya an cutar da yarinyar, yana tambayar ta "ina mijin naki, dan ba jimawa zanyi"

Cewa ta yi "yana ɗaki barin mai magan" ta tafi kiran shi, Ƙirjin ta na dukan uku uku.

09064271655
[10/12, 6:09 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*

Free book...

Shafi Na 8

Maman shaheed (Fatima Abubakar)

_Ajmal & jumana & suhail_

Koda Juma ta tafi sanar ma Ajmal zuwan, suhail ƙarfin hali tayi na zuwa ƙofar ɗakin shi zuciyar ta na luguden dukan uku uku dan bata taɓa ba, ganin bata da zaɓi ko damar tsayawa dogon tunani dan suhail wani irin fusatacen bawa ne wani lokacin duk da dai yana da kirƙi aman wani lokacin zuciyar shi akusa take, shiyisa suke yawan faɗa da mahaifiyar shi, dan haka tayi saurin aro jarumta ta fara knocking ɗin ƙofar tana haɗawa da sallama da taushashiyar muryar ta mai daɗin amo,daga cikin kamar a bazata taji ance.

"waye shigo" furucin Ajmal da yayi ƙarfin halin furta hakan dan besan lokacin d y bata izinin shigan ba ma, ita kuma sai tayi tunanin yayi hakan ne dan ya goge kokwanton Kar nagane yanayin zaman d tun zuwan su gidan suke yi.
Chapter 9 · 0% Book details