← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 21

Sashe 7

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"zaka iya mana Abokina you can do it, try and see zakace na gaya ma, saboda idan da ina baka kana amfani dashi yanzu be kyautu ka dinga amfani dashi ba saboda you have a wife, a Yanzu, so akwai banbancin tsakanin da can baya da yanzu, dan haka nace ka ajiye duk wasu dabarun nan ma da nace ka dinga yi, kuma zaka iya haba be a man mana, mai uwa a gindin murhu fa baya cin Tuwon shi gaya, indai baka yi abun da ya dace ba to zan iya cewa kamar baka gode ma Allah da ni'imar da ya maka bane, kasan abin da Allah yake nufi da hakan? It just like tsuntsu Daga Sama gasashe fa? "sai Sameer da Dr Anas suka kalli juna suka sa dariya banda, Ajmal da yake ta jin wani abu a game dashi.

Sanan yace" to ya zanyi da yadda nake ji tun jiya idan muka sami kusanci da..... "

" babu yadda zaka yi sai aiki da bin umarnin da lafiyar ka da gangar jikin ka suke umartan ka, in a ɓaya y zama saɓo yanzu fa? Bani amsa da kanka... " Dr ya tambaye shi.

" ni fa bazaku gane bane duk yadda zan muku bayani... "

Sameer ƴa kalli Ajmay ya ce" Hmmm mu ko muke ganewa, kaifa matsalan ka ɗaya ne zuwa biyu na farko so kake ka nuna ma mommah ko zaka mutu a haka ka wuce ja mata abin kunya ko? Sai na biyu cutar ku akayi daga kai har wacce aka jona ma, to munji an cuce ku, to ku kuma kanku adalci kubama kanku mafita ku nuna baku aka cuta ba duk wanda ya muku hakan kanshi yama sai ku juya akalar lamarin daga ɗaci zuwa daɗi ku zauna ku yi abin da ya dace, dama gidan Aure ai rufafen sirri ne sai kunso ku buɗe Har duniya ta gani ko ta ji, kai ne jagora kuma Kaine aciki Kuma kana da yadda zaka magance matsalar nan ayau in kaso, wuƙa da nama duk suna hanun ka, ka gwada ka gani, to kai baka gwadan ba Amman kake yanke hukunci akan abun da baka da tabbas"

"Ajmal maganan gaskia Sameer BA Iya aboki bane a gare ka he is ur Dr ma in kaso dan har magani yake baka cikin kalaman shi, babu wani abu da ya wuce abaka shawara a yanzu" Dr ya faɗa ma Ajmal.

"OK, Naji zan gani, if possible Kuma nidai zaka jini" murmushi suka mai, sanan Dr yace "to babu matsa ur welcome, Ina MA fatan Alkhairi, Amman dai b magani kafi buƙata ba a yanzu dai"

Miƙewa sukayi sukayi sallama da Dr Anas suka bar office ɗin shi, Sameer ya kai shi gida suka gaisa da su mommah da ummah su Hassan nata murnar ganin shi duk d dai babu yabo babu fallasa sai yaƙen dole da yake musu, Amman mommah sai da taso gano wani abu,kawai bata samu damar magana bane.

"kai wai ina zamu naga kayi hanyar nan?" Ajmal y tambayi sameer.

Sameer be Ko kalle Shi ba ya bashi amsa da "gidan ka mana, kana da inda yafi nan ne?"

"kai dai wallahi ka fiye kafiya, to in akwai abin da zanyi a kasuwa fa? Sai bazan je ba saboda Anmin wani Auren...."

"kai kadai ka zagi Aure, dan Aure yafi gaban zagi ko wata mumunar kalmar Dan ka ganni arzikin shi nake ci duk inda na shiga ake ganina da mutunci da kwarjini gashi har da ladan Auren fadeel Nanan Kaine sheda ma, kuma kullin in ba bargon Auren na shiga bani da sukuni a duk inda zansa ƙafa, kai Aure fa kan Kat Ne in kana jin ƙurunƙus to Aure ne, malam ka bada kai kawai bori ya hau ka tsaya kana ta wani..... "

" kai wanan ya dama, daman halin ku ɗaya da shadow goyon ka ne duk ƴan iskan ɓoye ne ku ɗin irin Kaga jiya Kaga yau har kana kan ganin gobe ɗinan zaka gaya min magana"Ajmal yana faɗa yana wurga ma sameer harara.

"hhh nagode da shedar nan wato mu ƴan iskan ɓoye, Kai Kuma ai na bayyane be dan kai da kake da signing ma me wanka ba tare da...." wani zabura da Ajmal yayi kamar ze daki sameer yana wani hucin ɓacin Rai.

"ni zaka gayama magana dan na bari kasan sirri na, gori zaka min ko buɗe sirrin da ba kowa na iya gayama ba, zaman da muke yi kenan dama Sameer?"

Parking sameer yayi a gefen hanya dan yaga abokin nashi ya harzuƙa yana neman canja mai maganar shi..

Dafa kafaɗar Ajmal sameer yayi Yana cewa" broh I d'nt mean to hot you wallahi, ka kuma sani in fact ban faɗa da wata manufa ba ka sani, kafi kowa sani na sirrin ka nawa ne naka nawa ne, naga kaima kasan nawa sirrin, naga kwanaki da muka sami matsala da mmn fadeel kai kaɗai na gayama har ka min umarni nakuma bi har komai ya wuce babu wanda yaji har yau, so hakan be zamana yasa mun zama Aminan juna ba masu rufe sirri kan juna sai dan kace min ɗan iskan ɓoye cikin wata irin na aboki da Aboki sai ni dan nace maka mai.... "sai ya kasa ƙarasa wa.

Yaci gaba da cewa" duk da sigar wasa muka furta, to dan Allah ya tafi a haka mu barshi a hakan, ni da zuciya ɗaya na firta ka kuma fi kowa sani na in fa ka yadda "

" nima nasani kawai dai Abunne yazo min intentionaly, amma muyi haƙuri duka, kaima Kayi haƙuri, Kuma Naji shawarar ka zan gwada wanda zan iya, ya wuce, Amma dai jibi zan koma kasuwa"Ajmal y furta yana kallo sameer da sakakiyar fuska.

"OK Allah ya kaimu, sanan ka ɗan sake ma yarinyar nan ko yaya ne, ban nemi sanin y kuka kwana jiya ba kasan nasan komai, bance kuma dole yau kayi abin da ya dace ba, Amman dai ko gaisuwa da cin abincin ta ne please indai har Tama tayi kaji?"

Ajmal ya amsa da" OK Naji, duk da ba alƙawari na maka ba, wai ina mmn fadeel basu dawo ba har yanzu? "

" Hmmm bata dawo ba sai jibi ai na gaya mata kunata fushi kai da Amarya tace kuyi haƙuri kanta bisa wuyan ta, nima on be half of her Ina sake baku haƙuri saboda indai bata je ba a yanzu ba ajin akwai ranar da zata ƙasar nan dan duk dangin baban su rabi ne fa acan rabi kuma anan kaga fa har cewa tayi rabon ta da ƙasar kusan 15yrs kenan Kaga Ko sunjima dan yanzun ma zuwan ta ai ba nan kusa ba in ta dawo"

"gaskia kam tafiyar ce ai tayi tsayi, na karɓi uzurin ta Ai, ita kuma ka gaya mata da bakin ka ai ka iya surutu har da tambayar yadda ta tashi" Ajmal ya ce mai.

"kai to ai abun da baka yi bane nama cikin hikima ko dai.. Amman dai shikenan, kuma kasan zan iya isar mata da saƙon ai, nidai a daina zama kamar ana gaba baida kyau a sha'anin aure" Ajmal ko kula shi be yi ba har suka iso ƙofar gidan.

_Jumana & Hleemah_
"OK kindai ga abokin shi bashi d case dan Allah ki sake ki riƙe gidan ki a wajen ki zanga wasu abubuwan fa inna shiga daga ciki nima na dinga ma bawan MD, to wallahi kiyi mai kyau" suka sa dariya a tare.

Da tai makon halima suka girka jalluf ɗin taliya dan da tumatir ɗin Leda ma sukayi amfani dan babu kayan miya, sai suka sa ragowar kazar da jumana ta rage suka tashi girkin sai lemu da ruwa da suka kai daining din suka jera ma ango da Taimakon Halee, suma suka zuba suka tafi ɗaki suka ci.

Sosai halee ta taba jumana shawarwari da kwantar mata da hankali har ta ɗan saki jiki.

_Ajmal & Sameer_
Bayan su shigo halee ce ta fito ta musu barka da dawowa, Ajmal ganin ba jumana bace har yana ɗan murmushi ya amsa ta nuna musu daining tace "komai yana can na abincin su, jumanan wanka take ne, in ta gama zata fito"

"OK ni ai wucewa zanyi sai dai ko ango" wani kallo Ajmal Yamai, sanan yace.

"ashe duk mun ƙoshi wa zaka bari yaci wani jagwalgwalon yara" ya faɗi jagwalgwalon ƙasa ƙasa yadda halee bazata ji ba.

Shimo Sameer ganin ze gwasale ƙoƙarin su Sai yayi ƙoƙarin tursasa kan shi dan dai yaga Ajmal yaci abincin, yace "toh muje sai Musa albarka"

Harara shi Ajmal ya sake yi ze zauna ya, kamo shi yayi wajen daining dashi yana mai magana da ido.

Sai da halee taga sun zauna sameer ya fara buɗe womers ɗin tukunna ta koma wajen jumana.

"ke ashe kin fito, to yi sauri ka shirya gasu can suna cin girgin Amarya, nima fa na kusa tafiya" halee ta ce.

Kallon tausayi jumana ta mata "kai sis tun yanzu, kuma yaci abincin?"

"Hmmm ashe kin damu da yaci da kika ƙi girka mai, gulma, to gashi can sun zuba harma sun fara ci" ta bata amsa.

"shine dai mai gulma ashe zeci yayi shiru da kamar bazeci ba" ta mayar mata.

"to in zeci zuwa zeyi yace miki zan ci abinci kamar yaron goye, shi ai sarki ne namiji a gidan shi ba sai yace ba girkawa ake a bashi dan Sarautar shi, inna tafi kika Dena keda Allah nidai nayi iya yi na" hali ta dungute mata kai.

Dariya jumana tasa tace "eyeee har da wani nida Allah, kamar wacce ta aikata wani zunubi"

"iye da ame kika ɗauke shi, to babban zunubi ne ai kin sani, nidai gama kije kima mijin ki sannu da zuwa" ta bata umarni.

"kai nidai wallahi, to ai ba dai muna gidan ba zan mai ko yaushe ne ai"

"ke kika sani nayi iya nawa, lokacin da zaki maƙale abin ki har ki fito da sabin sample na kyautata ta mai ina ina, ba sai nazo zan gani ba, kun fi kusa, da kun zama abu guda an wuce wajen" haly na kallon ta take firtawa.

"kai halee Kedai kamar ƴar iss...."
Chapter 7 · 0% Book details