← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 21

Sashe 8

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ohon miki ki kirani da koma meye, gaba a bambance ɗan iss... Ɗin In ma ƴar guguwa ne ba iska ba ki kirani"

Atare suka fita, lokacin har sun kammala cin abincin, sameer ne ma ƙarfin ci, Shima yayi ne dan suga kamar anci.
Amman Ajmal cacakala yayi Sai da ya gaji da mitar sameer ne ma ya ɗan ci.
Suka koma falon suna jiran fitowar su.

Suna fitowa, kuwa sameer yace "to ni dai zan wuce Amarya sai gani na biyu in mmn fadeel ta dawo, dan suna Ghana akayi bikin tace a baki haƙuri sai ta dawo zata zo in sha Allah"

Kallon ta halee tayi sai ta amsa da "OK, ayya babu komai, Allah ya dawo da su lafiya, nagode"

Halee ma tamai Allah ya tsare, Ajmal ko bema kalli inda jumana take ba, har ya tafi raka sameer.

Halee Dan ta fara koyama jumana yadda zata sami kusanci da mijin ta, tasa suka zauna a falo kafin y dawo har da kunna musu TV ta sa musu tasha, duk da hankalin jumana baya kan TV tafi so suyi hira da haleema, ita kuma guduwa take son yi.

Ko da ya dawo a falo ya gansu, ya wuce ze shiga ɗaki halee tace "yauwa ango dan Allah ƙo cazan ka na kusa ka sa mata caji dan mun manta an baro nata a gida sai anjima ko gobe za'a kawo mata" duk tayi hakan ne dan ta haɗa su.

da kamar yace shima ya manto nashi, sai yaga meye caza, kuma ma baya so halee ta fahimci abun matsayin wulaƙanci, sai yace "OK, barin ɗauko a gwada ko ze yi"

Ya a shiga ɗaki, jumana ta kalli Halee tace "kai Halee meye hakan?"

"kusanci yarinya" kawai ta ce mata ta fizgi wayar dama tasan cajin ta Befi 50% ba ta, miƙa mai da ya fito ya ƙarɓi wayar ya koma ɗaki da ita, gani miƙa mai taƙi karɓan cazan.

Mamaki duk ya gama kashe jumana, daga ƙarshe suka taɓa hira, haleema tace zata gudu ta kira shi ta mai sallama, jumana tace "Ai bakin ji yafi nawa tsayi wallahi babu inda zani dole sai kin haɗa bala'e kin ɗau wayana kin tura mai yanzu kuma zaki turani gaba ɗaya, sai dai ki ɗauke ni ki kai ni da ƙarfi" ta tura mata baki gefe.

"to kar kije, wacce bata jin shawara" suna taƙaddamar nan sai ya fito daga ɗakin da alamu alwala yayi ze tafi masallaci, nan haleema ta fara ce mai "to ango nidai zan wuce, a kular min da ƙawa kuma muna godiya da kulawa sai wani lokaci in Allah ya kawo ni dan ita nasan fita ba yanzu ba kam"

Fara'a dole ya ƙirƙira, yace "tun yanzu ba wuni zaki yi ba?"

Amsa ta bashi tana dariya "wuni, tab! Ai nema na za'ayi hakan ma ai nayi ƙoƙari, sai wani lokacin dai na wuni Amman ba yanzu ba, tafiya zanyi"

"OK, to hakan kinyi ƙoƙari thanks, Ki Gaida mutanen gida" ya mayar mata da sakakiyar fuska.

Jumana nata mintsilin ta, taƙi ko juyowa bare ta nuna taji ko hana ta mai magana tafiyar da zatayi.

Badan yaso ba kawai yana haɗa ido da jumana yaji bakin sa ya firta "wayar na ciki in zaki yi amfani da ita"

"OK" kawai tace ta sauke idon ta daga nashi tana jin abu na tsirga mata.

Sosai hakan yama halee daɗi.

Kafin ya fita haleema ta musu sallama ta riga shi dan in ba haka ba baza suyi rabuwar lafiya da jumana ba,kuma jumanan bata so hakan b dan duk kasa mata kyakyawan salama tayi.

Tana tafiya ya fita daga falon yayi haraba gidan ya wuce masallaci.

Jumana Har zata shiga ta ɗauko wayar ta taji ta kasa shiga ɗakin dan bata son abin da ze dinga haɗa su ma.

Dole ta cigaba da zaman falon tana ta karatun zuci har ya dawo gidan bakinta shi ɗauke da sallama dan ɗabi'ar shi ce ko waje babu kowa sai yayi salama in ze shiga.

A ciki ciki ta amsa yadda bata da tabbacin yaji ko beji ba, Amman shi yaji, ɗakin shi ya wuce, a zaton shi ta cire wayar yaga bata cire ba sai ya ɗauke ido daga kan wayar yana lissafin yadda ze miƙa Mata wayar.

Tashi tayi ta tafi ɗaki dan yin sallah itama.

09064271655
[09/12, 6:45 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*

Free book...

Shafi Na 7

Maman shaheed (Fatima Abubakar)

_Ajmal & jumana_

Jumana na son amfani da wayar ta Kodan ta ɗebe mata kewa Amman ta rasa yadda zatayi, tsaki tayi mai sauti tana mitar duk halee ce ta tsula mata iskancin nan tana zaman ta da wayar ta.

Ganin ta rasa yadda zatayi dole ta fito falo ko zata ganshi, ko da kanshi ze iya miƙo mata wayar ba tare da ta nemi hakan ba, wayam ta gani a falon alamar yana ɗaki bai fito ba, komawa ɗaki ta sake yi tana mita.

Ajmal ma yana cikin latsa wayar shi, sai yaji wayar ta tana ringing, wani gajeren tsaki yaja ya shafa goshin shi, irin an haɗa shi da damuwa ɗinan, har wayar ta katse bai da alamun tashi ya ɗauki wayar bare ya miƙa mata, sai da akayi wajen kira huɗu, ana biyar ɗin ne d yaji za'a dame shi y tafi dan ya rejecting call ɗin yaga wani suna ne yake kira dan besan ma ya akayi har y iya karanta sunan b, yaga ansa *Abeed jini ɗaya* sosai yake mamakin waye wanan jini ɗayan dan Yama cire sunan farko, sai zuciyar sa ta bijiro mai da tambayar, to kai ina ruwan ka d koma waye meye haɗin ka da shi? Wata ba taka ba, atake ya sake wani tsakin yana mitar koma waye shi y sani, yayi ta kira, Amman shi dai kar a dame shi, y koma ya zauna y kasa fita bare y bata wayar ta.

Ita ma ta kasa yimai magana, sai TV da take ta aiki ita kaɗai har falon ta dawo dan ko zata ganshi ta karɓi wayar Amman bashi ya fito ba har sai magariba da ze tafi masallaci, tana zaune tana ta tunanin yadda zatayi.

Samun kanta tayi da kallon shi a karon farko duk da ba kallon nutsuwa take mai ba, Amman ta hango wasu abubuwa da dama a tare da shi da basu ne a gaban ta ba a yanzu.

Shiko ko kallon ta beyi, Amman yaganta ta Wutsiyar idon shi, sai yaji kamar ya ɗauko mata wayar ya bata, ganin bata yi niyar ce mai komai ba ya rabu da ita da niyar ya ficewar shi, sai jayi kamar tayi magana, da sauri ya tsinci kansa amai kallon ta dan tabbatar da abin da kamar yaji, sai yaga bama shi take kallo ba wasa take da gefen Mayafin ta Amman kamar TV take kallo kamar mai tunanin wani abu kuma, hakan ya bashi damar yi mata wani kallon da bai taɓa mata ba dan baze iya cewa ka kalar ta ba yanzun ma haka dan a tsorace yake kallon ta yana gudun ta ɗago su haɗa ido, dan haka yayi sauri ɗauke kanshi yayi hanyar fita daga falon har ya fice.

Haushi ne ya kama ta, tabi ƙofar da harara ta ji kamar ta shiga ta ɗauko wayar ta dan tasan ta cika tun tuni yabar mata waya a wuta sai ya kashe mata batir kawai a banza.

Kashe TV tayi dan takaici ta koma ɗaki da fushi taba cewa In yaga dama ma ya riƙe wayar gaba ɗaya indai sai tace ya bata ko in sai taje ta ɗauko, sallah tayi ta fara tunanin mai zata ɗora, ita fa dama ba Auren ba girki, Aikin gida da sauran su dama zaɓin ta ta aura to da sauƙi har tana da damar jin ra'ayin shi na tambayar me za'a dafa mai, Amman yanzu ita kaɗai zatayi kiɗan ta da rawar ta ki girkin ɗazu da halee ta zura mata basu cinye ba ga na dare kar taje tayi ya barmata, ita fa gaskia in ba dole ba bazata dinga mai girki ba dan ta fahimci mugun miskili ne ga nuna halin ko in kula, sai wani kumburi yake kamar garin kwaki, Alhalin ita ya kamata ta dinga cika tana batsewa akan an mata Auren dole ba shi ba dan maza ai su ko Auren dole aka musu ai suna so kuma su karɓa mata dai ake karɓa da wuya maza kuwa duk inda ta faɗi sha ne, a tunanin ta.

Iya tunanin da zatayi tayi, tanaji har ya dawo duk da be dawo da wuri ba ya haɗu da yan hira a masaliaci, ya dawo babu Jimawa ya sake tafiya sallah isha, be dawo ba sai da aka idar, itama tayi Tata a gida.

Ko da ya dawo yana shiga ya samu wayar ta nata ringing ya gama tsakin Shi ya fizge wayar a caji ya wurga ta gado sai yaga dai baza a daina kiran ba kawai a zuciye ya fita d wayar d niyar kaimata, ya samu bata falo, haushi ya kama shi yayi hanyar ƙofar ɗakin ta ya kasa bugawa.

Itako taji ƙarar wayar Tata Amman ta zuba ido taga gudun ruwan shi.

Sai da ya gaji da jin ƙarar wayar ya buga ƙofar a tsorace ya sake bugawa yana sauke nanauyan ajiyar zuciya, ya samu ya furta "ga wayar ki ana..."
Chapter 8 · 0% Book details