← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 21

Sashe 13

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"momah abin da ya faɗa miki haka ne mana, ko mai kike tunani?" suka tambaye ta dan su tunanin su ma beje inda momah kai da tunanin ta ba, sai wani mugun kallo da ta bishi dashi da harara duk da bata gama yadda hakan ya faru ba kuma taji daga wajen su, sai taga kamar kariya suke son bashi.

Shi ko abincin ya fita ya bari ran shi a ɓace, har zebar falon ta kira shi ta fara mai ruwan masifa har tana cewa ita zema fushi da abinci, to yazo ya ɗauka ya cinye ko ranshi ya ɓaci, ganin baya son bijire mata kawai ya haƙura ya dawo ya zauna yana kallon wani wajen ba inda take ba.

Wani kabbarar sallah ta sake tayarwa, dan ta sami nutsuwar zuciya yanzu ganin yana kusa da ita.

Hassana ne suka biyo shi da abincin ganin ranshi duk a dagule suka dinga bashi haƙuri da ido, dan suna magana in ta idar zata balbale su da cewa uwar me tamai, duka ko zagi? Ita zasu nuna ma su kashin awaki ne ƙarshen ƴan uwan taka, dan haka sukayi gum.

Abincin ma ya fice mai arai yaƙi ci ya zama wani sababin, haka yaci kaɗan ya bar mata sauran, har ta idar tana ta hararar shi...

Sai da yaji shigowar Abba shi ne ya fita ya mai sannu da zuwa, ya samu ya sulale ya wuce ɗakin shi zuciyar sa fal ƙunci.

Yauma kamar kusan ko da yaushe dake garin akwai sanyi, lokacin sanyi ne ya fara shigowa, haka yayi mafarkin da mafiya lokutta mafarkin kebewa da macce yake addabar shi, koda ya tashi be gabatar da ibada ba sai da yayi wanka sanan ya fito zasu tafi masallaci, momah ta fito kenan daga ɓangaren ta zata tashin shi tasan fa yana tashi, Amman dan ta tsangwame shi ko ta tabbatar da zargin ta take zuwa tashin shi, su hassana ko dama ta Dena aika su tashin shi wai bata san mai zai faru ba, har yayi gaba ta dawo dashi ta shafa gashin kanshi taji shi a jiƙe ta keɓe baki tace "haka dai Allah ya yaye Maka in ka yaye ma kanka Fitinannen yaro da sauran ka wane mutum inji mutuwa ƙwaya nawa kake shekaru naka nawa ne ko secondary Baka gama ba" shi dai anan ya barta tana maganganun da inda sabo fa ya riga da ya saba da jin su, tun da ta tabbatar da yayi wankan ai shikenan.

Ko da suka idar da sallah a masallaci, Abba yace suzo su tafi gida, cewa yayi zasuyi karatu ne ze tawo.

Ya koma gefe yana ta tunanin makomar rayuwar shi indai ya tafi a haka da momah, sai yaji an zunguri kafaɗun shi ana mai magana "sarkin ƴan tunanin duk duniya ya ne mai ake tunawa Assignment Ko lamarin duniya?"

Doguwar ajiyar zuciya ya sauke sanan yace "kai wa yaje ta wani rayuwar duniya har ƙwaya nawa nake da zansa duniya a gaba, Assignment Kuma Ai bani da matsala da shi, kawai dai ka share Sameer"

"Hmmm haka kullin kake faɗa, toh shikenan tun da bankai ka gaya min damuwar ka ba, shikenan ɗin kawai hakan duk yana daga cikin yadda da aminci" ya ja shi suka koma gefe malam mai akhadari ya biya musu shafin da suka tsaya, daga baya aka musu dogon jawabi da akan abin da ya shafi wanka da sabuban shi da dalilin da yake sa ayi wankan, sai Ajmal yaji yau kamar dan shi akayi dogon jawabin dake yau Asabar babu school sai tahafeez.

Bayan sun gama karatu suka tafi gida.

A haka rayuwa taci gaba da tafiya, Ajmal na fuskantar tsangwamar momah, shi kuma kullin buƙutuwar shi na sake ta'azzara duk da yadda ya ware Litinin da Alhamis duk kwanan duniya sai yayi azumi ya raya su da karatun Qur'ani, shine yake samun sassauci.

Bashi da sakewa matuƙar ba a ɓangaren ummah yake ba.

Ana cikin wanan hali karayar Arziki tazo ma Abba, sosai hankalin iyalan shi ya tashi shima dan yana da ƙarfin imani ne Amman duk da haka sai da zuciyar shi t raunana, har hawan jini ya kama shi, duk Ajmal yafi kowa shiga damuwa dan yana son Abban shi.

Haka aka dinga mai jaje da addu'a, har ya samu ya dawo hayyacin shi.

Yaso ace ya ɗora Ajmal akan harkar kasuwancin shi kafin faruwar abun to Ajmal baida hutu tun safe in ya tafi school sai yamma suke dawowa dake a haɗe da Islamiya Abba ya mai dashi ko ya huta da tsangwamar momah, su kuma duk sai sun dawo daga school suke wucewa Islamiya.

Akwana a tashi Abba ya gaza biya mai kuɗin makaranta dan makaranta ce mai kyau da tsada, Ajmal ɗin da kan shi yace Abban y canja mai, haka kuwa ya ɗauki shawarar shi gashi yana ajin ƙarshe ne, ba a kai ga sashi a wata ba Abba na duba mai mai ɗan kyau da sauƙi sai, a makaranta aka fahimci baya zuwa sai aka tambayi abokanen shi, suka ce cire shi ma za'ayi, aka tambayi dalili suka ce basu sani ba, dan shine monitor ajin Nadu sss three A, Sai aka wakilta sa'ed ya tambayo Shi dalili.

Yana zuwa kuwa sukayi magana da Ajmal be ɓoye mai komai ba ya sanar dashi maganan kuɗin makaranta ne dan kuɗin shekara ma ake biya mai tun da ya fara daga jss one Har sai ya canja class ake sake biya mai.

Sa'ad na zuwa kuwa ya sanar ma da pc dalilin Dena zuwan Ajmal ɗin hukumar makaranta ta fara tunanin ya zatayi dan kar karatun yaron ya ruguje dan yaba da feature Mai kyau in ya ginu, sai sukayi shawara a tsakanin su suka tsaida matsaya akan sa a ɗauke shi scholarship Sai baban Shi ya biya mai kuɗin waec da neco.

Koda aka kira Abba yaji abin da hukumar makaranta tayi sosai yaji daɗi ya dinga musu addu'ar, yace to Allah ya hore mai kafin lokacin zai biya mai, suka rabu washe gari Ajmal ya dawo karatu ƴan class ɗin su suka dinga ihuu suna sowa Wai babban ƙwaro ya dawo dake baya wasa ko kula kowacce yarinya a class ɗin matan ma mai masifar girman kai suke cemai ko mai fuskar sannu, in Kaga fara'ar shi a cikin maza, ne ƴan uwan shi, dan da ya keɓe da mace musamman in ta baɗa turare Ko tana mai kwarkwasa shi kaɗai yasan halin da yake shiga, dan haka yama kanshi karatun ta nutsu ya nisance su, har wani mai shegen kula mata yana tsokanar shi wai shi ɗin ya binciki kansa ko baida lafiya, dan duk zuƙazuƙan matan class ɗin ƙarya yake yace babu wacce ta mai ko take burge shi, sai dai in yana da lalura,ahaka ya barshi ya yadda shi mai allurar ne

Wata rana momah ta bar su hussy suka tafi biki har dare ya musu ta kasa zaune ta kasa tsaye wai tana gudun tunda fati ne kar aje ama yaranta wani abu, saboda ita kullin cikin wawan tunani take, guma tana gudun ta aiki kare gidan kura ta aika Ajmal ya nemo mata su, ƙarshe dai shi ɗin ta aika, aike da sai da taji dama tare suka tafi.

Lafiya lau yaje ya dawo mata dasu suna shigowa taga ya kama kunnen hussy dake tafi tsiwa yana mata gargaɗi Sai, taho da sauri tana mai masifa, har da cewa da ta sani da bata aike shi ba wayasan uwar abin da ya musu acan gashi har gida ma bai barsu ba, Wai baze Dena kusantar yaran ta ba, ita bata so wacce masifa ce take damun shi haka, Abba caraf a kunnen shi, yaji tana ta ruwan masifa, har ummah sai da ta fito ta fara mata nasiha tace "malama barni ke tunda kin barshi yana ta kunna nitso cikin yaranki Mata ni ba haka nake ba, kinsan illar da hakan ze haifar? Tabo yake zama na har abada fa"

Ummah da sauri ta bata amsa da "a'a ni rayuwar Ajmal tare da ƙanen shi mata khairan in sha Allah, bazamu ga wanan ba ai ko ban haifi Ajmal ba nasan waye Ajmal, Kedai ki cire daddti a ƙwaƙwalwar ki ƙi rungummi ƙaddara in ba haka ba sai fushin Allah ya sauka akan ki"

"a'a akan ki dai ba kaina ba, da kike magana naga dai ɗana ne, Ai kasa tana taka ɗanta ne badan bata so ba sai dan ta ɗora shi a doran Tarbiya" momah ta faɗa a kausashe.

"kai kuma wuce muje munafiki, jarababe Kamar akanka aka fara tashin balaga" sum sum ya wuce su hassana ko dama tuni sun wuce sashin su.

Abba ne ya ja hanun Ajmal yayi ɗakin shi dashi dan yanzu baya son hayaniya tun da ya fahimci yana da hawan jini, ɗakin ta bi Ajmal tana masifa.

"wai kai wanne irin Fitinanne ne dole sai ka ɗaura hanun ka akan yara na? Mai kake ji in ka ɗora? Na wancan ɗakin da kake latsawa basu isheka ba sai kazo kan ƙannen ka uwa ɗaya uba ɗaya..."

"ke shamsiya ya ishe ki haka ki Dena jifar min ɗa da gurbatacen bakin ki, Wai mai kika ɗauki yaron nan? Lalacewar shi bata kai haka ba wallahi in kika cigaba da kumfar baki ko jifan shi kwalamar zargin ki na banza zan baki mamaki zan miki abin da baki taɓa zato ba, muguwar uwa kawai"

"yi haƙuri Abba ku Dena sa'in sa a kaina dan Allah" Ajmal ya furta yana shirin kuka.

"dallah can munafiki ba Kai kaja komai ba mai fitinar tsiya da na rasa inda ka gado kai ba shaye shaye ba bare Nace acan kake shawo wani abun"

"au bazaki yi shirun ba?" Abba ya tambaya a zafafe.

"bazanyi ba indai akan Fitinanne ɗan ka ne mai mai ɗabi'ar Ayu kullin cikin wanka, dole na tsayar mai kafin ya jamin abin kunya, na dai faɗa na sake duk lokacin da kayi wani ta'adin a waje makaranta ko unguwa sai dai ayi shari'a da waccan uwar taka ko wanan uban naka, Amman babu ni aciki" momah ta faɗa cikin nuna halin ko in kula.
Chapter 13 · 0% Book details