Sashe 20
Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan Anyi ukun Abbah Ajmal Sai ya Zama shi yake Rarashin su Safiyya da musu nasiha, da subi Abbah da addu'a.
Ranar bakwai ɓaki suka watse bayan Anyi sadaka.
Gida ya zama sai su kaɗai, momah b ƙaramin daɗin dawowar gidan tayi ba, da ta rabu da ganawa da mijin ta na ƙuruciya da bata ji daɗi ba dan da abbah ya tafi da tabon ta.
Tun da Abbah y rasu Ajmal ya ɗan sami sassauci daga momah ɗan Sai a lokacin rasuwar ya sake jin ɗumin jikin momah a tare dashi bayan ya suma ɗinan, dan yasan duk sun damu dashi har ummah dan sai da yayi addu'ar Allah yasa hakan yaci gaba da ɗorewa.
Bayan an zauna Abbah ba wani abu ya bar musu ba na gado sai wanan kuɗin da bai cika miliyan ba, sai gidan d suke ciki sai tsirarun kayan da su Ajmal suka kwaso na shago sai, aka raba musu gadon iya abin da aka lissafi da kiyasi ya bayar, sukace Ajmal ya ci gaba da juya ragowar kuɗin da kuma sai da ragowar kayan Abbah, bayan yaba su momoh da ummah wani kuɗi a hanun su, su hussy dama suna makarantar gwamnati ne shi kuma ya ɗora da karatun shi na NCE...
Haka rayuwa ta fara garawa Ajmal yana kiyaye abin da momoh take so, itama kadaran kada Han Bata sakar Mai ba bata cigaba da tsangwamar shi ba.
Dama sun sami kayan abinci a rasuwar sai aka raba sai suke cefane da kuɗin hanun su kafin kasuwa ta buɗe ma Ajmal.
Wata rana Ajmal sunje party wani abokin su da sa'eed da sisco suka matsa mai dole yasa yaje badan yana so ba dan bai fiye shiga duk irin abubuwan nan ba, koda sukaje haka ya haɗu da wata uwar rawar kai ta dinga shige mai kamar ta lashe shi ko ta rungume shi take ji duk yadda yake kauce mata sai da tasa shi yayi mata masifa, su sa'ed ma suka mata magana abin ya mugun bata kunya ya dizgata a gaban mutane dan haka sai taci alwashin ramawa dan bata barin bashi, ana haka kuwa bayan an gama taron kowa na tafiya su sa'ed sun fito shida Ajmal da hankalin shi yayi gida dama gashi sunyi karo da wata mace sai da jikin su ya haɗu da na juna tun da ya koma gefe bai sake bari ya shiga cikin turmutsutsun bikin ba ko liƙi ma da sisco ya ja shi sukaje sai da wasu matan suka mai goge hankalin shi ya tashi ya bar wajen gaɓa ɗaya.
Ajmal beyi Aune ba yaji an Mai wawan Rungumar da duk Duniya mahaifiyar shi ce kawai zata mai yaji sanyi na ɗa da uwa da nuna kulawa in ko wata ce ta mai to matsala ta tono mai, duk ƙarfin shi kasa ƙwatar kan shi yayi dan ji yayi kamar yasa ihu,gashi ta gabashi motsi atake ta saukar mai da kasala, itako magana take tana cewa "wai kai na Allah ko? Wa zaka jama aji ƙaryar banza bacin da ganin kura kasan zataci mutum kai ɗin banza kace baka so?" da ƙyar sa'ed da sisco suka fincike ta daga jikin Ajmal da yayi mutuwar wucin gadi dan shi kaɗai yasan yanayin da ya shiga, sai hucin ɓacin Rai da yake furzarwa, sisco da ranshi ya gama ɓaci da wani bahagon Mari ya ɗauke ta yana furta mata" karuwar gidan biki, da Shirmen nan naki zai kula ki abin da kowa ma kai mai kanki kike yi, tunkiya wacce bata san darajar da Allah ya mata ba aladiya kawai jelar ki a ɗage kullin"ya bita zai tattaka ta sa'ed ya ruƙo shi, aka bar sisco da hucin ɓacin Rai dama haushin ta yake ji, suka kama Ajmal da kunya da takaici da baƙon lamari duk suka kawo mai ziyara, da bai shirya tarbar su ba.
"eh ai na faɗa mai kowa yaci tuwo dani miya yashaa, ko banza yanzu na mai da mugun yawu, banda dizgani da yayi, sa'a ma yaci naga ba ɗan hayaniya bane kuma ba ɗan hannu bane da wallahi in na sako shi gaba sai ya bar garin nan tsirara ko ya zagwanye zan watsar da shi" wata ƙawar ta taja ta "ke dallah kowa kike rabama ke matsala ta dake kenan indai yawun ki ya tsinke Sai kin maida kaurin shi, ko a network kike ne? zo muje mu rage ta a hotel, gobe ma dawo gidan bikin nasan fitina kike ji abin y motsa" ta jata suka tafi, ita ko idanun ta sun kaɗa sunyi jajir.
Sa'eed d sisco Sai Abdallah da ya tuƙo su har gida suka rako Ajmal suka ajiye mai kayan Abincin da suka sa aka mai takeaway ɗin shi d lemukan da bai ci ba bai sha ba, suka bashi haƙuri sunsan baze yadda ma a koma gidan bikin dashi ba shi yisa suka dawo dashi gida.
Bayan tafiyar su yana so ya shiga gida dan sunyi magana da momah akwai kuɗin da ze bata, gashi a halin da yake cikin baze iya shiga gidan ba dan yasan momah muguwar fahimta ce da ita sai ta tsare shi da tambaya shi kuma baida amsar bata dan kowa ya ganshi yasan ba a hayyacin sa yake ba.
Yana katifar shi yaji marar sa ta ɗaure abu yana taso mai sosai ya kwanta ya fara murƙususu, yana shirin zuwa ya sakar ma kanshi Ko ruwan sanyi kenan yaji salamar Hussy "Yaya momah tace ya maganar da ta maka?"
Da ƙyar ya iya amsa mata da Kice sai da safe zan bata, zoki kai muku wanan ke da su safna kuci"
"laa yaya biki kaje ne? Yaya lafiyar ka lau kuwa?" ta tambaya.
"eh biki naje uwar surutu je ki kai muku, kuma ni lafiya lau nake" ya bata amsa a gajarce.
Bayan ta fice ta kira su safna suka faraci Bayan sun ma ummah d momah tayi duk sunƙi ci, momah Dai tunda taji husy tace taga Yaya kamar baida lafiya Amman yace babu abin da yake damun shi taji hankalin ta yaƙi kwanciya tace dole sai taje ta ganin ko fitinar ya sake dawo ma da kanshi dan a wawan tunanin ta kwana biyu ya dena ne ko ya cire abun a ranshi ya hutama kan shi ta ƙi yadda da HALITTA shi ce hakan.
Ajmal sosai yake fama da marar shi da ƙyar ya tashi ya shiga wanka dan wanka sai da ya hau kanshi, fitowar shi kenan yayi daidai da sallamar momah,da yaji kamar ya nutse a wajen, dan yana jin muryar ta gaban shi ya faɗi ya runtse ido ya kasa amsa sallamar ma, har ta shigo.
"Hmmm na sani ai kai dai bazaka bar wanan ƊABI'A taka ba ko? Kai dai fitanan nan bazaka rabu da ita ba ko? Daga ina kake? Me kaje kayi da har kake wanka masifar da ka ɗorama kanka?"
Jin zargi ya shigo ciki da sauri ya buɗe baki ya fara magana "momah zargi kuma? Wallahi Allah ne shaida na ban taɓa ƙoƙarin aikata abin da duk kike zargi na ba, ko kusa ko alama Allah ɗaya kenan, ni daga bikin mujittapha muke d su sa'ed Ai na gaya miki..."
"yauwa kaji ba biki ka haɗu da mata sai mai ya faru kuma? Ina jinka" momah ta katse shi ta mayar mai da tambaya.
"babu, har rantsuwa fa namiki momah na rasa ranar da zaki yadda dani"
"ai kai ɗin ne ba abin yadda bane ni kaɗai nasan fitinar ka daga aikata abin da zaga jamana magana nake ƙoƙarin Maka shinge Kai Kuma baka Ganema kanka abin da nake hango ma Ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba wankan kayi, ko ba haka bane gashi nan naga alama, kai Wai haka Kaga su sa'ed sukeyi? Ko duk kanwar ja ce? Kamar akanka aka fara halitar mazantaka Ne Wai? "
Ajmal dai zama yayi kan wata kujera a ɗakin nashi ya runtse ido ya rasa da kalmomin da zeyi amfani momah ta fahimce shi.
"kaci gaba da yi, nidai kar ka sake ko inuwar ka ta kusantan min yara da fitinar ka ɗin nan na zata ka dawo mutum ne ashe hali na ƙoƙon rai, sai ka dage ka nemi kuɗi kayi aure ko alkadarin ƊABI'A ka zai karye in ka tashi yi sai ka nemi mazaƙaƙura in kuma cigiya za'a bayar inada hanyoyin su ai ni"da wani irin sauri gami da mamaki Ajmal ya ɗago rinanun idanun shi ya kalleta.
Yana maimaita cigiya? Mazaƙaƙura? Aure? To dame zeji da rasuwar Abbah Ko da nauyin su da ya dawo kanshi ko na Aure da be ma taɓa kawo wanan tunanin nan kusa ba, ga karatun shi, kwaya nawa ma yake? Duk haka ya dinga jero ma kanshi tambayar da ya rasa mai amsa mai su.
"eh inada hanya gara kaje ka ƙarata, da kajamin abin magana" ya tsinkayo muryar momah.
Bayan ta mai tas ta fice ta barmai ɗakin.
Sosai abun ya haɗun mai biyu ga yanayin da yake ciki da yaƙi barin shi ga damuwar da momah ta sashi a ciki, kiran sa'ed ne ya shigo wayar shi, "ya abokina komai lafiya dai ko?"
"eh" kawai ya bashi amsa.
"shegiyar yarinya zata jiƙa mana aiki, nasan dai dole a sami matsala Amman sai kayi dabara ka samu ka ɗan sami sassauci dan ka iya bacci" sa'ed y mai magana kai tsaye.
"haka nake son yi, ai kadai kawai sai da safe"
Sa'ed "OK, Allah ya ƙara sauki, ya kuma tashe mu lafiya kar fa ka damu kanka da yawa nasan ka"
"OK" kawai yace ya kashe wayar, ya duba yaga yana da lemun tsami a ɗakin Dama yakan ajiye ya ɗau waya ya kira safiya yace ta kawo mai ruwan zafi a kofi da wuƙa, babu jimawa ta kawo mai ta tafi ya haɗa abin da zai haɗa ya samu yama kan shi flushing sanan ya kwanta duk da bai dainajin yadda yake ji ba gaba ɗaya Amman ya ragu, sai dare sosai kafin ya samu bacci.