Sashe 15
Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"to Kinji kema mai kika ce? Idon ki na miki gizo tsabar fa kinsa abin ne a ranki, kuma in har hakin shine yau da gobe dole ze aikata kuma fa har a gani, dan Allah ku yadda da ɗan nan" ummah ta firta tana nuna alamar gajiya da nuna ma momah duk wata hanya da zata fahimta dan ta fuskanci tayi nisa bazata ji kira ba dole Alhj ya fusata.
"yaya yanzu ya zamuyi? Haka zamu bari Momah tabar gidanan?" Safna ta furta idanun ta sun gaji da zubar da ruwa.
"yaya dan Allah kace wani abu kafin ta tafi ko Abba ya fita" ya sake jiyo muryar husaina.
Safiya kuwa da Hassan wajen shi suka dawo ganin kamar nutsuwar shi bata tare da su, suka kama hanun shi suka tsuguna Kowa ya riƙe ɗaya "yaya Kayi magana dan Allah, munsan kafimu shiga damuwa Amman ka gaya mana abin da zamuyi"
Da ƙyar ya samu ya kalle su ya seta nutsuwar shi sanan yace "kuyi shiru ku sama zuciyar ku nutsuwa, duk abin da zamuyi ba zeyi tasiri ba a yanzu dan Abbah ya fusata, kawai dai mu jira zuwan ummah sai muji nata hukuncin dan nima kaina ya kulle, baban takai cina Inna tuna Wai duk ni na haɗa wanan bala'in da bamu taɓa ganin shi ba tun tasowar mu, sai naji nayi dana sanin zuwana duniyar ma"
Da sauri Safna ta samai hannu a baki hankalin ta a tashe "yaya babu kyau duk wanda Allah ya halito yana son ganin shine a duniya yasa ya halicce shi yaya kar kayi saɓo ka tuba yaya, kuma ba kai ka jawo ba laifin momah ne ko yaya Hassan?"
Kowa acikin su yace "eh yaya baka da laifi fa kai, duk ma wa moma ta tsana sama da kai a gidanan bamu san mai ka mata ko ka tare mata ba" suka furta suna tura baki.
"salamu Alaikum" suka jiyo Abbah ya furta yana mai shigowa falo.
Da sauri suka miƙe kowa yana jira yaji Abba yace ya maida momah, jikin su har rawa yake dan yayi saurin furta abin da suka fi son ji a yanzu.
[16/12, 8:46 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*
Shafi Na 12
Maman shaheed (Fatima Abubakar)
Shiru sukayi har Ajmal a tsatsayen da suke, Ajmal ne kawai a zaune dan baida kuzarin da zai iya tashi ma.
"Ku zauna" suka ji Abbah yace.
"Abbah dan Allah kayi haƙuri kabar momah badan MU ba dan Allah Abbah" suka firta mai banda Ajmal dan shi yasan bakin alƙalami ya riga da ya bushe dan bai taɓa jin Abbah ya rantse akan abu haka ba da gaggawa, yasan yau dai kam babu wanda ya isa ya gyara lamarin nan sai in shi da kansa ne yaso hakan.
"kimin shiru ku sama ma kanku nutsuwa, na farko hukuncin da na yanke akan maman ku ya yanku, Kar wanda ya sake maganar kuma, na biyu ku sani yayan ku jinin ku ne duk duniya baku da kamar shi ko kuna da shi?" ya tambaye su.
Kowa yace "a'a"
"to dan haka tole kumai biyaya Ku ɗauke Shi a matsayi yaya wanda ko bayan babu raina shine zai kula da ku, har auren ku zai iya bayar wa, ku dinga saka shi a addu'ar ku Allah ya yaye mai abin da yake damun shi kuma ya taimake shi a komai na rayuwa, ni a matsayina na mahaifin ku nake nemar Mai wanan, sanan abu na uku tun tasowar ku Ajmal ya taɓa cutar da wani a cikin ku? "
Da sauri wasu suka girgiza kai wasu suka ce" a'a Abbah"
"kodai ya taɓa ku gayamin magana nakeyi daku ta fahimta tsakanin uba da yaran sa"
"wlh a'a Abbah"
"toh Naji daɗin jin hakan nasan waye yayan ku a ko ina kuma zan iya bada sheda akan shi dan nasan gata ba hauka bane, sanan magana ta ƙarshe ko ina raye Ko bana raye Bana so wani abu ya shiga tsakanin ku na ba daidai ba ko na samun saɓani tsakanin ku ko na ƙin yimai biyaya Kun min alƙawari? "
" eh Abba Insha Allah "suka amsa mai.
" toh nagode muku Allah ya muku Albarka Allah ya shiga cikin lamarin ku ya kare min gaban ku da bayan ku"
"Amin ya Allah Abban mu" suka amsa har Ajmal da addu'ar tamai daɗi dan dama daga Abba ko ummah yake samun irin addu'ar nan.
"yauwa kai kuma, ga ƙanen ka nan Amana inaso ka tabbatar ma da duniya da mahaifiyar ka da ni kaina yadda da na baka bazata tafi a banza ba da addu'ar da nake muku kullin, ka jasu ajiki ka basu kulawa ka tausaya musu ka ƙaunace su kamar ciki ɗaya kuka fito ko bayan raina, ka fuskanci karatun ka ka guji abokanan banza ka guji ruɗun zamani ka riƙi ibada da azumi da izinin Allah bazaka taɓe ba kuma baza ka kai inda mahaifiyar ka take turaka da bakin ta ba, addu'ar ta ina fatan ta danne Tata duk da mahaifiyar ka ce, Allah ya dubeka ya baka kariya da tsari daga shaiɗan da biyema zuciya ka fahimci mai nake nufi ai? "
" eh Abbah Insha Allah, nagode uba nagari da ana samun irin ka da yara da yawa matsalan iyayen su mata ba tayi tasiri akan su ba, nagode sosai da yadda Abbah, nasan kai ɗin mahaifina ne abin Alfaharin mu, nida ƙanena kuma bazaka ji komai ba sai Alkhairi da izinin Allah"
"Naji daɗi sosai, Allah ya muku Albarka, su hussy su dawo nan da zama kai kuma in babar taka ta fita sai ka koma can saboda kar abar wajen babu kowa, kaji ko kar ka kula ta in ba haka ba kasan akan ka zata huce kafi kowa sani"
"na gane Abbah In sha Allah"
"ni zan fita sai na dawo da azahar sai ka taho ko?"
"toh Abbah"
Fitar shi ke da wuya sai ummah ta shigo, ta same su kamar sun ɗan sami nutsuwa atare da su, sai jikin ta ya bata kamar abban su ya shigo, sai ta tambaya, suka ce ya shigo har ya fita zai tafi kasuwa, da sauri ta bishi dan yau an jama kowa a gidan.
Har zai fice ta kira sunan shi ya dawo "Ahj yau ko sallama babu? Allah ya huci zuciyar ka, dan Allah kayi haƙuri, nasan bango aka kaika Amman alfarma guda zaka mana nida yaranan Kar fushin ka yayi nisa ko tsanani akan momah damu baki ɗaya zata tafi, fatan mu ka sauko da wuri ka..."
"Naji kuma ni ba kuyi min komai ba, ai a hayyaci na nake babu akan wanda zan huce mai laifi daban kuma akan shi na sauke fushi na, ki kula da yara nace su dawo sashin ki da zama sanan shi kuma ya koma can ɓangaren ki kula da komai"
"yauwa nima dama haka nayi tunani, ba tare zaku tafi da shi ba?"
"eh naga ai be gama dawowa hayyacin shi ba, abar shi ya huta zuwa azahar sai ya biyo ni, kar ta ɗaukan min ƴa ko ɗaya kar a bari ko kallon banza tama ɗana"
"toh Alhj duk d kasan Ai bazan iya kokawa d ita ba, Ajmal kuma fa ɗanta ne kai dai Allah ya kyauta kawai, Allah ya dawo da kai lafiya"
"toh Amin, na tafi"
"Allah ya kiyaye"
Ummah ta fira ta koma ciki wajen su.
Momah ta gama tunanin duniya sai ta kira wata ƙawar ta "ke ki bari kawai zan gaya miki inda za kizo mu tattauna dan ni yanzu ina hanya zan yi wata ƴar tafiya zuwa ƙyauye"
"ƴauye kuma yin me? A wanan lokacin?" aka tambaye ta daga cikin wayar.
"nace miki uzirin hakan ne ya kama zan tafi zan muyi magana kawai sai kinjini"
Ta katse kiran bata bari an sake magana ba.
"hello kawu kana gida?" momah ta sake kiran wata wayar.
"eh ina gida, lafiya" kawu ya amsa.
"lafiya kawai ji nayi nayi kewar ku shine zanzo na ganku" ta firta.
"to to shikenan Ai yau an waiwayo mu kenan injin dai da yaron nan da kike mana rowar shi zakizo Ajamalu yake kowa kudai kuka sani suna kamar na karawan zamani, da kuma tagwayen yaran nan Kinga daga nan ma a basu maganin baki dan naga sun fara girma kar a lashe miki su ku ba wani kula kuke be mutanen maraya Sai an cinye ku tas ku rasa yadda za kuyi ƙarshe ku dawo gida Ata fama har Allah ya kawo sauƙi"
Tun da ya furta sunan Ajamalu (Ajmal) ta haɗiyi wani abu mai ɗaci, sai ta daure tace, "a'a kawu suna makaranta ni kaɗai ce zanzo"
"kash ba haka aka so ba to Amman babu komai sai kinzo din gona zani na dawo kawai"
"to kawu sai nazo" ta katse wayar ta zira hijab ta ɗau Atm da ragowar kuɗin da yake hanun ta ta saka a jaka ta saka takalmi ta sake goge hawayen ta, ta gyara fuska yadda ba za'a gane tayi kuka ba taka akwatin ta madaidaiciya ta fita, har ta gota ƙofar falon ummah Sai Ajmal ya jiyo motsin Jan Abu kamar Kaya ko akwati da shan majina yasan babu kowa gidan sai momah bayan su da suke sashin ummah, sosai yaji wani abu ya tsikari zuciyar shi na ɗaci da yanayi mara daɗi har sai da ya runtse ido gashi ya kasa furta ko ufan.
Sai da ƙyar ya taɓa husaina ya nuna mata ƙofa alamar ta leƙa da sauri ta leƙa ta dawo da sauri ta ce mai "yaya momah ce da kaya zata tafi yaya ka tashi muje" kai ya girgiza mata,sai ya mata nuni da ta kira ummah ta sanar mata.
Haka kuwa akayi tana gayama ummah, ta fito da hijabi a hannu a wajen momah ta ƙarasa Sawa tana ta bata haƙuri da mata alƙawarin bazata jima ba dasu da yara zasu ta bashi baki har zaman su ya dawo kamar a baya, kai kawai momah ta iya ɗaga mata dan bata so tayi magana kar kuka ya biyo baya.