Sashe 21
Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Ko da ya farka da asuba ma sai da ya sake wanka, sanan ya tafi sallah, suka haɗu da sa'eed suka dinga tsine ma nusy, babu yadda sa'ed beyi da Ajmal ba yau ya bari akai Amarya da shi yace babu inda za shi, dole sa'ed ya haƙura ya rabu da shi.
Da safe sashin momah ya fara zuwa dan da wuri yake son fita ya gaishe ta, ta amsa babu yabo babu fallasa, ya bata kuɗin da sukayi da shi sanan yaba su hussy ba break ya musu sallama batare da momah ta mai ko tayin abun kari ba, duk da mantawa tayi Amman dai sanadin kular da ita da yayi ne yasa ta manta.
Sashin ummah ya sake shiga d sakin fuska ummah ta karɓe shi suka gaisa yaba su safna kuɗin break ummah Nata Mai Godiya da addu'ar nasara a rayuwar shi har sai da yaji idanun shi sun ciko da ƙwalla gudun kar ummah ta gano har ta tsaya tambayar shi sai yayi ƙoƙarin tafiya kawai, ummah ta mai tayin abinci yace a'a zai karya in ya fita, dole tasa su safiya suka kaimai ɗakin shi, ya samu ya karya kafin ya fita.
Daga makaranta ya tashi ya wuce kasuwa babu laifi kasuwar duk da dai kasuwar sai a hankali dan babu kaya ka kasuwar dama taja baya, abin da yake samu Befi ya taimaki su momah ba da ummah sai ƙanen shi maganar ajiya ko adana kam babu ko ware wata riba da za'ace ze iya kashe gararin gaban shi kam har yanzu shiru ne.
A haka rayuwa take ta gara mai ya mai da hankali akan kyautata ma su momah d Abbah ya tafi ya barmai yayi alƙawarin kuma kula dasu da ɗaɗi babu daɗi da wuya duk runtsi baze gajiya da su ba sai ya fara ganin basa cikin damuwa ko zeyi aure ma dan akan su ze iya haƙura da Aure duk da yadda yake ji da halin da yake shiga na buƙatuwa yafi damuwa da mutan gidan su.
Yana kiyaye dokokin Allah ga azumi akai akai ga ibada dan haka abun yake zuwar mai da sauƙi duk da dai in abun ya motsa kamar ze mutu yake ji, Amman haka yake runtse idanun shi daga ko wacce irin ƴa mace dan shi bai taɓa kusantar wata da sunan so bama bare har hirar soyayya ta haɗa su, bare wani abu na laifi ya shiga tsakanin su duk ya kiyaye ya nisanta kanshi da su.