Sashe 16
Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ummah ta dawo ta kira Hassan da Safiyya tace su bita su rakata har tasha sai sunga ta tafi sanan su dawo gida, da sauri suka ɗauko hijabai suka zura ta basu kuɗin mota suka tafi har ta fita cikin layi, suka karɓi akwatin suka karɓi jakar Basu ce mata ba bata ce musu ba har suka sami abin hawa, suka nufi tasha babu mai magana a cikin su.
Duk abinan da akeyi ashe wata maƙojiyar su na kallon su tun fitowar ummah ta window Har shigan su abin hawa sai ko hankalin ta ya kasa kwanciya taji bata iya bari labari ya baza gari ba tasan bata taɓa jin wani abu na aibun gidan ba to Bana fa kamar akwai labari jikinta ya bata gara ta samo da wuri dan ta baza a unguwa dan wasu ma Guntsi feshi suke kiran ta tsabar gulma da yaɗa ƙarya da gaskiya, gyalen ƴar ta ta janyo a igiya ƙarami ko lura ba tayi ba be rufe mata jiki ba ta faɗo gidan, da sallamar ta ce ta sanar da ummah da Ajmal Shigowar ta.
Ajmal dama ya tsani matar, ta taɓa kawo ma momah ƙarar shi dama Wai baya gaishe ta tunda momah tamai faɗa ya sake raba gari da ita, gashi dama mugun kwarjini yake mata ko surutu take da ta ganshi zata tsagaita sai ya wuce ta ɗora shi dai har gobe kuma baya gaishe tan kuma baya kallon inda take.
Ko da yaji sallamar ta shirin tashi yake yaje ya kwanta dan tunda kansa ya Sara mata har yanzu bai sauka ba, sai ya koma ya zauna, ummah ma taji daɗin hakan dan tasan tauraruwa mai Wutsiya ce ta kawo musu ziyara wacce ganin ta babu Alkhairi.
"salamu Alaikum maman su Safanaa" sunan Safna ma sai taja tsafar iyayi d kwarewa.
"waalaki salam maman baby maraba"
"ke kaɗai ce in shigo" ta tambaya.
"eh ni kaɗai ce mana shigo"
"yauwa dama maman su kyautar Allah nagani...." tana surutun da ya kawo ta tana shiga tayi turus ganin Ajmal a zaune a kujera ummah na tsaye husaina da Safna suna zaune suma.
Kasa ƙarasa maganar da ta faro tayi, sai ta hau inda inda, sai su Safna suka fara gaishe ta suna hararar ta, sai anan ta tuna bama su gaisa da ummah ba.
"au ko gaisuwa bamuyi ba, Ina kwana ya kwana biyu ku kuna cikin gidan ku abin ku hankali kwance, yafi muku babu wanda yasan me kuke..." Ajmal ne ya ɗago ya mata wani kallo da runanun idanuwan shi da tun ɗazu suka canja kala har yanzu basu dawo daidai ba, da sauri ta haɗiye sauran kalaman ta tama miƙe daga kujerar da take shirin ɗofaba kwankwason ta kamar na sauro.
" eh dama cewa nayi barin leƙo mu gaisa da kuma in ce miki kunsan alawiyya mai kayan miya ta haihu ko? Dan yanzu ta Dena kawo kayan miyan mai sai bayan suna" tanayi tana sosa Kai alamar tama rasa abin faɗa.
"gaskia bamu sani ba sai yanzu dai da kika kawo saƙon ma leƙa mu Mata Allah ya raya"
"yauwa nasan ba lalai kun sani ba ai, to barin koma"
"OK Tom shikenan maganar dama ko da wani dai?" ummah ta bigi cikin ta tasan dodon ta Nanan.
"a'a dama shikenan gaishe kun ma dai nazo yi dama, sai anjima a Gaida maman su kyautar Allah" ta fice jikinta nata kyarma.
"zata ji, uwar gulai" ummah ta firta.
"a lalai yaya ka zama boss ɗin matar nan," Safna ta faɗa da sai yanzu ta samu nishaɗi tun faruwar abun sai yanzu suka ɗan dara.
"wlh yaya ka zama dodon ta kai kunga yadda duk ta rikice wlh ko Abbah ta gani ko baban baby bazata yi irin wanan rikicewar ba" husaina ta faɗa suna dariya.
Ummah na dariya tayi tace, "Ku bana son shegantaka ba ta fita ba dai sai ku shafa mata lafiya"
"Hmmm naso ta ƙarasa Amman bayanan ta da wataƙila Shigowar yau da zamar mata ta ƙarshe, dan bata san me nayi niyar mata bane, ba kiji mai ta fara cewa ba?"
"Hmmm Naji ta mana ba gashi ba Salin Alin ka mana maganin ta ba"
"Hmmm munafuka kawai shiyisa bazan taɓa gaishe ta ba, ni bari naje na kwanta ummah"
"toh, Amman dan Allah ka kwanta ka huta ne kar ka sama kanka damuwa dan Allah ka barma Allah komai zai kawo daidai to" ummah ta furta ma Ajmal.
"in sha Allah ummah, Allah ya shige mana gaba"
[17/12, 8:41 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*
Shafi Na 13
Na maman shaheed (Fatima Abubakar)
"In sha Allah, ummah, Allah ya shige mana gaba"
Da "Amin" ta amsa, ya wuce falon momah ya kwanta a kujera mai cin mutum uku.
Sosai Ajmal ya nutsa a kogin tunani ya rayuwar shi zata kaya a wanan yanayi, haka ya dinga addu'ar Allah ya kawo mai sauƙi ko canji na rayuwa da kawo dedaito cikin gidan su.
Yana wanan dogon nazarin ne, kiran wayar sa'ed ya shigo wayar shi da kamar baze ɗauka ba dan sai da ta katse ya sake kira sanan ya ɗaga
"Helo" Ajmal Y firta
"Kai ya akayi ne ina ta zuba ido ka fito shiru tun asuba da muka haɗu" sa'ed Y tambaye shi.
Ajmal amsa mai yayi da "kai ina gida kawai..."
"kawai me?" sa'ed
"share kawai ba komai" Ajmal.
"kai wlh ban yadda ba akwai abin da kake ɓoye min, dama bamu zama ɗaya ba?" sa'ed
"mtsss! Sa'ed da damuwa fa bazaka gane bane ina gida bana jin zan iya ko fitowa ma"
"OK, Ganinan zuwa gidan"
Bayan ummah ta kama aikin girkin rana su hussy na taya ta duk jikin su babu ƙwari.
Sai sa'ed yayi sallama dake sashin ummah ne a farkon shigowa sai na Abba a gefe sai na momah a cikin gidan da ɗakin Ajmal dake ta wajen gidan.
"Assalamu alaikum" suka jiyo muryar sa'ed da ke ta sallama.
"waalaka salam" safna ta leƙo, "laa yaya sa'ed"
"na'am, Autar ummah, Ina ummah?" ya tambaya.
"tana ciki shigo, ummah ga yaa sa'ed" ta sanar mata.
"OK, sa'ed Kaine, ya mutan gidan?" ummah t fito daga kitchen tana tambayar shi.
"lna wuni ummah?" y gaishe ta.
"lafiya lau, ya mutanen gidan?"
"lafiya lau suke" sai y fara in-ina, ummah tace "anzo wajen mutumin ne ko? Yana ciki part ɗin momah je ka same shi"
"OK, Tom, su sofi d da twins?" ya tambaya yana shirin barin falon.
"Hussaina na kitchen, saffiya da Hassana kuma sunyi rakiya"
"OK, to barin ƙarasa wajen shi"
"Tom afito lafiya"
Sa'ed ya tafi yana mai shakka ƙarasawa dan yasan momah Sai a hankali bata sake mai fuska kamar yadda ummah take mai.
Da fargaba yayi sallama "Assalamu alaikum" sai yaji muryar Ajmal yana cewa "shigo mana"
Cikin ya shiga ya ganshi kamar wanda yayi jinyar shekara duk a wani har gitse.
"ya momah fa mu gaisa?" sa'ed ya tambaya.
"bata nan, ta bar gidan, Ina cikin damuwa sa'ed, bazan ɓoye Maka Komai ba, yau har saki ya gift tsakanin momah da Abba kuma duk ta dalili na ne sa'ed"
"kai ban gane mai kake nufi ba, saki fa kace yanzu momah Bata gidanan?"
"tabbas, kamar yadda kaji na faɗa"
"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" sa'ed Y firta.
"garin yaya kai Amman abun beyi daɗi ba sam wlh, to yanzu meye abin yi har ta bar gidan? Ai da batayi saurin tafiya ba maybe Allah ya daidaita komai"
"Hmmm komai baze dedeta ba a dai yau kam, sa'ed, dan Abbah yayi rantsuwar da be taɓayi ba kan sai ta bar gidan, dole yasa ta tafi"
"kai abu beyi daɗi ba gaskia, to wai me ya kawo hakan ta faru?" sa'ed y tambayi Ajmal.
Sai da Ajmal ya nisa kafin ya zayyane ma sa'ed komai be ɓoye Mai ba na gane da *HALITTA* shi da mama take ma kallon *ƊABI'A* har zuwa sakin Da ya gifta a tsakanin su da Abba akan hakan, sosai sa'ed ya fuskanci bakin zaren da mamakin irin yadda maman take ma Ajmal.
Sa'ed rarashin Ajmal ƴa dinga yi yana sake kwantar mai da hankali da nuna mai ai allurar shi ba wani abun tashin hankali bane sai ma gane ingancin lafiyar shi Dan da ace bashi da lafiya gara ace tayi yawa, kuma in sha Allah ma akwai mafita ya ƙarfafa mai gwiwa sosai da sake bashi shawarar riƙe ibada da yin azumi akai akai, da kiyaye dokokin ubangiji zai sami daidai to.
"sa'ed Duk bani da kasala yanzu a kowanne, Amman fa kullin kamar abun ƙaruwa yake, Nifa ko ƙamshin turaren Naji Kai ko kusanci na samu da wacce take ba muharrama ta ba dan haka za Kaga ko a school ina nisantar duk abin da zai haɗani da matan nan ƴan kuci ku bamu wanda wasu basu kai matan ba ma Amman suta maka babanƙra suna kawo ma kansu, kai ai kasan komai, inda na ke godema Allah wlh Azeem in Ina tare da Hussaina ko hassana ko safiya ko safna, banajin irin wanan yanayi, kuma koda ace jikina zai haɗu da nasu ne wlh jin su nake kamar nida kai haka, Amman momah taƙi yadda da hakan ta gaza gane hakan kullin cikin zargi jamin alkaba'e take, Wai mahaifiyata, wacce ta haife ni tafi kowa sani na fa sa'ed" Ajmal Yana magana yana jin ɗaci a zuciyar shi.
"to ai mu gode ma Allah, kuma ai jini fa ba ƙarya bane jini yafi ruwa kauri, jini yafi gaban wasa, shiyisa baka jin feelings akan su da ace kuna da wata ƴar riƙe misali da zaka fahimci banbanci da nake so ka gane, Amman hakan ma yafi lada, kaci gaba da gudanar da rayuwar ka kawai abokina Allah zai shiga lamarin, wanan shine ake cewa wasu sun samu wasu kuma sun rasa"sa'ed ya faɗa yana girgiza kai da alamun magana a bakin shi.
"ban gane wasu sun samu wasu sun rasa ba, me kake nufi?" Ajmal ya tambaya.
"hmmmm wlh yau kusan good one year Kenan anata fama da yaya mahadi akan Unaisa ƴar ƙanin baffa da ta nuna tana son shi akace a haɗa su wacce take gaishe mu har sai ta risina ɗinan?"