← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 21

Sashe 4

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"oya tashi ka canja Kaya malam dan wallahi ba zan ɗauke ka da wanan yamutsatsun kayan ba a ganka kamar wanda aka ƙwato daga bakin kura ranar angwancin ka guda" Sameer ya ba Ajmal umarni.

"kai babu abin d zan canja uwar mai zan maka ko aikena akayi a daren nan da sai na canja kaya" Ajmal ya firta yana sake gyara kwanciya.

"a'a kawima fa sameer ka fiye Sanabe Ko a haka ya tashi mu tafi ina abun da ya yamutse anan mutumin da ba kokuwa yayi ba, kasan fa sunan mutum a lalaɓa auren zamani ka bari mu tafi kar ya ɓotsare...." be idar ba, Ajmal ya taso a zuciye ya buga mai filo, yana huci Har cikin ran shi shadow yake ƙular da shi.

Sameer ko yana cin daɗi kunna shi da yake aranshi a zahiri kuma sai ya nuna baya kyauta wa, dan Y rasa ya zema abokin nashi.

Da gudu shadow yabar ɗakin Yana dariyar Mugunta, dama haka yake so.

"Bro yi haƙuri dan Allah mu Dena abu guda mufa ba yara bane, Kaga sa'ed ma yana kira na nasan sun juyo tashi ka canja mu tafi, yi haƙuri nasan sai an cuci mutum ake bashi haƙuri Amman babu yadda zamuyi yi haƙuri mutumin tashi dan Allah"

Badan yaso ba ya fara shirin saka babbar rigar, sameer ya riƙe yana girgiza mai kai ya karɓe ya ninke ya ajiye a gefe ya buɗe drower ya ɗauko Mai wani farin yadi mai taushi da kyau ya miƙa mai..

Ƙin karɓa yayi sai ma cewa da yayi "kai wallahi....." sameer yayi saurin rufe mai baki ya fara mai magiya da rarashi kamar ƙaramin yaro, har sa'ed ya shigo, da shadow, Aiko sameer ya kora shadow waje suka haɗu da sa'ed sukai ta bashi Baki had ƴa canja kayan, akace ya fesa turare yace, bai da shi, sameer yace "Muje mota ni ina da shi, duk ta inda ka billo Ai zamu toshe, gidan suka koma suka ma mommh da ummah sallama, ummah har mota ta rako shi tana ta shafa shi da shimai Albarka, idon shi tab da ƙwalla.

Mota ko sai da aka raba musu mota da shadow, dan Ango cewa yayi sai dai a kaima Amarya shadow Ba Dai Shi ba, indai be bar motar ba, dole sameer ya canza mai mota suka tafi da sa'ed.

Kafin ango y fito a shiga gidan ma sai da aka ci kwakwa, dan sai da shadow ƴa fara tsokana Shi ya fito a fusace, shadow ƴa gudu, Yana mai gwalo.

Suna shiga wani ƙamshi y daki Hancin su, sai shadow Yace "Anyi tuya fa an manta da Albasa, gida iya gida ango iya ango, Amarya iya amarya da zamuje mu tarar Amman banga tsarabar ledar da Ango ya sabo shigowa da ita ba da kayan shaye_shaye...." sameer ne ya bashi amsa da, "kai dai akwai munafuki wallahi to mu mun gama komai ko da kai za'a jira"

Ajmal Har ya tsaya da tafiyar d yake, kamar mai shirin yima shadow wani abu, sameer ya riƙe shi yana bashi baki akan kar ya kula shi, dan duk sun san halin shi, barkwanci ne da shi acikin su duk yadda suke cikin ɓacin rai in suka haɗu Sai ya kular da mutum ko ya bashi nishaɗi, kuma yana da kirki kuma duk abokanai ne, gashi cikin tsokana ze faɗa ma gaskia.

Bayan sun zauna a falo, hussy suka fito suka zo wajen su, suka fara mai sannu da zuwa, kafin su cika shi da surutu ya kamo hannu safna yace "maza ku wuce ku tafi gida sameer ze mayar da ku, kar ku bari na sake muku magana" duk yadda suka so suyi hira ganin kamar baya farin ciki kuma sun san komai, sai ma tausayi da ya basu, sai suka mai sai da safe, shima ya musu, sameer yace su jira shi a mota.

09064271655
[04/12, 7:01 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*

Free book....

Shafi Na 4

Maman shaheed (Fatima Abubakar)

_Ango da Amarya_

Bayan fitar su hussy, su zakkiya suka fito da Amarya falo dan yi musu abin da ya tara su kamar yadda sameer ya buƙata, sa'ed ya buɗe taro da addu'a yayi nasiha, sameer ma ya ɗora da nashi, ƙawayen Amarya nata amsawa, a ƙarshe shadow ya rufe da addu'a baza kace shine mai tsokanar ango ba, an shiga fagen serious tongue, Har ƴa basu haƙuri da su zauna da juna da gaskia da Amana.

Aka shafa addu'a, sameer y ba ƙawayen Amarya kuɗin d ƴa hanasu ciniki a farko dan baya son wanan cinikin dan yasan ran abokin shi a kusa yake, ƙawayen amarya suka fice su uku dan an sami kuɗi zakkiya ma tama Amarya sallama ta bisu, sai haly da Jumana ta hana ta fita, ta ruƙunƙume ta, dole ta kamata ta kai ta ɗaki dan taji meye matsalar ta.

Suna shi ga, haleema tace "meye kuma?"

"Haly abun..." Jumana ta firta.

"ban gane ba, OK na fahimta ki nutsu ki dage da addu'a, Ina miki fatan komai yazo ƙarshe a yau...."

Da sauri Jumana ta girgiza, mata kai, Alama a'a.

"OK kin fison kita dakon...." bata bari haly ta faɗi abin da yake bakin ta ba, ta ce.
"haly bazan iya ba ko da zan mutu kuwa, bazan iya ba wallahi"

Sosai ran haly y fara ɓaci tace "koda shine ya nema?"

Da sauri junana ta ɗago tana kallon ta cikin kaɗuwa ta ce "eh Bama ze nema ba na sani, nidai kawai a barni na mutu a haka kawai" ta fashe da kuka, da sauri haly ta toshe mata baki tana cewa.

"ki rufa mana asiri kukan ki yayi yawa malama ni wallahi na gaji da baki baki sai na nuna miki fushi na tukunna haba duk kin gajiyar da ni a bikin nan y bazaki hango abin da ake hango miki ba, in wasu sun cutar da ke nima kina nufin zan ce kiyi abin da zaki cutu ne? "

Da sauri Jumana ta girgiza kai.

" to ki nutsu ki tsanan ta addu'a, kisa Allah a ranki kiyi bautar Aure, Allah baya haɗa maka biyu Kinji, nasan yadda kike ji Inaji ciwon a raina kema kin sani, Amman babu yadda zamuyi sai abin d Allah ya zaɓa mana"sai kuka ya ƙwace musu duk su biyun suka rungume juna suna tayi har zakkiya ta dawo, da Taimakon ta, ta samu ta raba su ta kama haleemah suka tafi.

Shima Ajmal har waje ya raka su sameer,yana fita yaga su hussy zasu shiga mota ya ƙarasa kusa da su, hassy tana ganin shi ta fara share hawayen da take ta adanawa, ashe ya ganta dan akwai haske kamar farin wata a ƙofar gidan, ya ƙarasa y kamata yace "meye kuma sis?" kai kawai ta girgiza mai alamar babu komai ta kasa magana, ya fahimci tausayin shi ne da murnar ya samu ƴanci yau, sai ya shafa kanta yace "ya isa kuje gida kuna isa ku kirani komai dare Kinji ko?" kai ta ɗaga mai alamar to.

Shadow ƴa fito ya rungume shi suka rungumi juna, sai sameer yace "malam kar ka fara ka barshi ya tafi ya bar ƴar mutane dallah ita kaɗai"

Shado ne ya bashi amsa d "ai kuma wasa y wuce kewar mutun ce ta fara addaba ta tun yanzu wallahi, sai da safe fatan Alkhairi da hak'uri da juna bro" ya shafa bayan Ajmal da ya tsaya kamar mai tuna wani abu.

Sa'ed yace, "na ajiye ma ledojin a gefen dining, please Kayi abun d ya dace ko duka be samu ba dan Allah Kar mu ta abu ɗaya" kai kawai ya ɗaga musu, suka ɗaga mai hannu, suka tafi ya shige gida, har yayi gaba, sai ya dawo da baya ya ma gidan addu 'a ya tofe ko ina.

Sosai yake mamakin Wai da gaske dai an mai aure, ya jima kafin ya shiga falon, ganin bata falon, sai hakan ya mai daɗi.

Ko ina ya kama kallo a falon a zahiri ba kayan alatun yake kallo ko tsaruwar falon ba, neman Inda zega toilet yake ɗan sameer da sa'ed ma sun fi shi sanin kan gidan, dan shi yau shine zuwan shi na farko kamar yadda ƴan kawo amarya suka kawo ta, shima sai da aka kawo shi yau, haka itama ɓangaren Amaryar.

Can y hango wani ɗakin da in be manta ba sameer yace a ciki kayan shi yake, sai kuma yaga toilet ɗin falon, Sai yaji bari ya shiga ɗakin dan gabatar da sallah isha.

Yana shiga ya shaƙi wani ƙamshin turaren wuta ɗana jiki mai daɗi dan nan aka fara kai amaryar sai da haleemah ta zo tace ai ba nan bane ɗakin ta suka mai da ita nata suka turare nan din suku kulle,

Sosai ya shiga cikin wani matsananci yanayi na shaƙar ƙamshin ban, dan sai da ya jingina da ƙofar ɗakin ya samu ya ɗan seta kan shi.

Ganin hakan baze mai ba ya faɗa bathroom ɗin, Daga alwala besan lokacin da ya bige da wanka ba, sanan ya ɗora da alwalar ya fito ya ga akwatin shi ya duba jallabiyar da sameer ya siyo mai guda 6 ya zari ɗaya ya saka, ya nemi salaya sabuwa itama a cikin kayan shi da ya kasance duk aikin sameer ne, ya tada sallah, yana idarwa ya jima yana addu'a har da hawaye kafin ya faɗa dogon tunani da son sanin ina ya dosa da sabuwar rayuwar shi kuma.

_jumana_
Sosai taci kuka ta gode ma Allah, taga babu sarki sai Allah, ta tashi ta fara dube duben inda zata ga bathroom, tana ganin shi ta faɗa tayi alwala ta fito dan yin sallah da kai kukan ta wajen mai duka.

Tana idar da sallah ta dinga addu'a tana hawaye da jerama Allah ikirari da ya kawo mata agaji a cikin rayuwar ta, koda ta idar a wajen ta zauna ranta fal tunanin wa aka aura mata, ya zatayi da matsalar ta da take ciki? Ko ze karɓi aure? To in y karɓa ma ai ita bata karɓa ba, kawai dai zatayi zaman wani lokaci ne kafin taji kutsarin iya firta Bata son Auren a zahiri ga hajiya da kawu Labaran...
Chapter 4 · 0% Book details