← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 21

Sashe 14

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wai momah wani irin zato kike min? Anya ke kika haife ni kinsan zafin yawun ki kuwa akammu yaranki yafi wuƙa Mai suna gayama jini na wuce fa, kullin kita jamin masifa in banda addu'ar Abba na tare min Allah kaɗai yasan mai ze faru da ni, kuma wlh abun da kike zargina dashi ban taɓa kurkuren tunanin aikatawa bare Har nayi, kuma bazan taɓa yi ba Allah ne shaida ta, kawai abu guda na sani, da yawun ki akaina kike ƙara rura min wutar al' lamarin dan da addu'a kike tayani da lamarin bai kai haka inajin a raina dama ummah.. "

Abba bai bari ya ƙarasa ba ya dakatar dashi," rabu da mahaukaciyar uwar nan taka jahilci ne yake jagorantar ta, yi shiru yanzu zan kawo ƙarshe lamarin.. "
[15/12, 7:47 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*

Free book...

Shafi Na 11

Maman shaheed (Fatima Abubakar)

Sosai hankalin Ajmal ya tashi yasa. Duk hukuncin da Abba ze yanke ba lalai yama kowa daɗi ba dan haka ya taso ya fara magana da kakausar muryar da besan yana da ita ba.

"momah ki dinga tausasa lafuzanki in kina nagana da Abba ni yaron ki duk ihun da zaki min kin isa ne Amman Abba kam shugaban ki ne, kibi Umarnin shi kiyi abin da yace..."

Tass! Ajmal yaji saukar yatsun momah a fuskar shi, da sai da ganin shi ya ɗauke na wucin gadi, atake ya tafi tunanin dama be wuce Marin Nan ba a wurin momah, har yanzu?

" bazaki fita ba ne nace, kuma kar ki sake maran min yaro" Abba ya bata umarni.

Mai zakayi inna mareshi Ko Kai ka haifan min shi, ta ɗaga hannu zata sake marin shi kenan Abba ya riƙe hannu, a lokacin Ajmal ya runtse ido yana jiran saukar wasu yatsun kamar ɗazu dan beyi ƙoƙarin guduwa ba ya gama sadaƙarwa.

Hannun ta Abba ya jefar yayin da Ummah ta shigo da taji abun yaƙi ƙarewa tazo bada haƙuri.

"ke kije na sawake miki ki koma gida Kice su maidake Islamiya Ko bokon Bai samu ba na gaji da jahilcin ki, kuma wallahi sai kin barmin gida na a yau" momah ji tayi kamar an ɗora mata tifar sumuti Kamar wani abune mai nauyi ya danne ta sai amon sawaƙewa da take ji na kururuwa tsakanin kunuwanta da ƙwaƙwalwar ta, dan tama kasa rabe mai kalmar sawaƙewar take nufi, taje ta huta ko Rabuwa na saki?..

"inallilahi wa'inna illaihi raji'un Alhj kasan Mai ka furta kuwa? Da bakin ka?" ummah ta faɗa hankalin ta a tashe kamar ita aka saka.

"Abba kaji mai kace kuwa? Akaina? Abba dan girman Allah kar ja mana abin magana kar ka tona mana asiri kayi haƙuri ka janye kalamin da ban taɓa tunanin zaka iyayi ba, Abba ka gafarce ni akaina hakan ya faru Inata saku magana, tuba nake Abba" Ajmal ya tsuguna yana roƙan Abbah.

Momah kuwa da ta dawo hayyacin ta hankalin ta ya dawo ta tabbatar sakin ta yayi sai, ta ji saɓon ɓacin rai da tsanar Ajmal ya ninku a zuciyar ta, dan da bata tsanan shi ba sai yanzu,kamar ba ɗan da ta haifa b da ƙyar ta iya furta "roƙon me kake mai hankalin ki ya kwanta sai ka zuba ruwa a ƙasa kasha dan daɗi,zan barka da uban naka ai, ke kuma gashinan ki haɗa da naki dama yana cikin su kamar namata na mata, kai kuma in ya miki illar da nake jiye miki shikenan..." bata idar ba taji Abba na bata umarnin ta fice mai daga gida.

Ya ƙara da faɗin" ki ga illa a kanki babu abin da zamu gani sai Alkhairi, mai baƙin yawu, Ai ba ke kaɗai ce kika haife shi ba da ze rasa wata addu'a, duk lokacin da kika mai mummunar addu'a, Ina roƙa mai Allah y kifar da taki ya amshi tawa mai farin nufi da aniya mai kyau, dan kin shiga duhun da ganin hasken ki zeyi wuya, ki fice min anan mara tunani kawai"

"eh zan fita ai kuma ka sani bazan ba kura ajiyar nama ba, dan bazan bar yarana mata baligai a hannu wanan gurjejen gardin baligin ba ya murƙushe min yara mai..."

Abba ne ya tsaida ita da cewa "kar ki sake kiyi kuskuren ɗaukan min Yara ai bada su kika zo ba daga gidan ku ko agara aka haɗo ki dasu? anan kika same su tare da ni da kika raina baiwa ta dan haka ke kaɗai zaki tafi, kuma idan kikayi gigin bijirewa karo na biyu ina iya sake datse ragowar igiyoyin dan banga ribar zama da mai kan kifi ba kullum ana nuna miki Allah kina sake rumtse ido kiji wa'azi Ko ki koma makaranta ko zaki yadda da Allah kinƙi"

Sosai momah ta kasa motsi ta kuma kasa tanka mai, dan tunani take anya ba canja mata ma'aruf akayi ba? Agidan zata tafi tabar su twins, in aka lalata mata rayuwar yaran ta fa? Wa gari ya waya? Ranta a ɓace ta nufi hanyar fita.

"Alhj ka rufa mana asiri dan zatin Allah ka barta a gidan, kar ka sake aikata wani ganganci wanan ma da kayi ze dame ka ka dubi girman Allah" ummah ta firta.

"rabu da ita ai na rantse sai tabar gidan nan gani tayi na zuba mata ido gani take ƙarfi na tafi, zan bata mamaki sai tayi gigin fita da ɗaya daga cikin twins zata gane ba ma'aruf ɗin da ta sani bane" Abba ya furta yana huci.

"Abba dan Allah..."

Ajmal Be rufe baki ba, Abba yace "yi shiru Ajmal mahaifiyar ka mai iyawa da ita sai karan Maguzawa inna barta da Kai kashe min kai zatayi kwanan ka bai ƙare ba ka mata biyayya kana kan yi mata Amman duk idon ta ya rufe ta kasa gani, kar na sake jin kace komai umarni nake baka"

Shiru Ajmal yayi sai kuka, jin hayaniya tayi yawa ashe su hussy da su safna duk sun leƙo har sakin da ya shiga tsakanin Abba da momah sunji, atake hankalin su ya tashi suka cure waje ɗaya hassana da Safiyya kuwa tuni sarakan kuka da tausayin yayan su, tuni hawaye ya wanke musu fuska, momah na fita taci karo dasu idon ta fal da hawayen da yake neman izinin zuba, da gudu suka rungume ta suna kuka gaba ɗayan su sakamakon baƙon lamari da ya ziyarci gidan su yau, Ajmal fita yayi yana kallon yadda suka rungume momah,Yana Jin babu daɗi a zuciyar shi, baida iko da halittar shi da ya rabu da ita a yau ko kafin ma yau din koda kuwa zai zama dutse dan rashin buƙata,

yau ɗaya itama momah ta haɗa su ta rungume tana jin kewar su da rashin sanin inda ta dosa da tantance dama haka kalmar saki take da ciwo fiye da raɗaɗin shigar wuƙa tsokar Jiki? Su safiya da safna basu taɓa kusantar momah ba bare Har su raɓi jikin ta sai yau tun tasowar su duk ta haɗa tana shafa musu baya tana jin babu daɗi a cikin ranta, Amman izza da yadda da tunanin ta ya hana ta, ta sakko ta bada haƙuri ko ajiye tunanin ta, dan bata taɓa ganin abin da take zargi a zahiri ba, akan ɗan nata da ƴan uwanshi.

Ajmal ma ji yayi dama ta sashi a kafaɗun ta yayi kuka ta shafa mai baya haka, be taɓa samun hakan daga gare ta ba, har ya manta yaushe rabin shi da ɗumin jikin mahaifiyar shi, musamman yanzu da take ganin da ta rungume shi gara ta rungummi transformer Ko ta rungummi garwashin wuta sai hakan yafi mata sauki.

Daki ta tafi don tunanin mafita, duk suka bita, suna kuka.

Shigowar ummah ne yasa duk suka zuba mata ido, ummah ta kore su suka fita suka koma sashin ummah har Ajmal ɗin da sukayi zaman jigun jugun Kowa da abin da yake saƙawa a ranshi.

"yaya, dan Allah ki sama zuciyar ki salama, zargin da kikema ɗan ki ya munana yama zarta zargi dan haka Alhj yake kiran shi da wawan tunani ko ya danganta shi da rashin ilimi, shima fa ɗan ba haka yaso ba, bashi ya zaɓa ma kanshi wanan ƙadararen lamarin ba, HALITTA shi ce tazo a haka ke kuma gani kike ƊABI'A ce da ya ƙaƙaba ma kanshi, shin dama mutum na iya sama kanshi? A gaban mu fa ya taso kin fimu sanin komai, ki sassauta mai dan Allah, yanzu ga abin da hakan ya jawo? Shi ɗan hankalin shi a tashe namu a tashe kema naki a tashe"

Wani kallo momah tama ummah da idanun ta da suka rune da ƙyar ta iya furta "Nifa nasan waye Ajmal nasan mai ze aikata nasan abin da baze aikata ba, fitinar yaron bazaku Gane bane, Nifa gudun ya ɗauko mana magana nake mai hakan da kuma kar ya fara daga gida, yanzu ai shikenan ya shiga tsakanina da ubansa, zan tafi zan barsu in yaga dama ya kashe su ma ya fita waje ya ƙara da na waje, yaron da baya iya kwana biyu beyi wankan tsar..."

"naji yaya ki daina maimaita zance ɗaya ke kalmar ko nauyi bata miki ne? Ko wani bare ana so ka kyautata mai zato bare naka na cikin ka, to Naji ƊABI'A asa ce yau shekara nawa kin taɓa gani a zahiri wani mummunan abu ya faru? Ko an taɓa kawo mana ƙara daga waje? To wanan be ishe mu yimai kyakyawan zato ba ashe? "

" toh ai kare Karen da nake mai da yanzu ta'adi da zeyi Allah ne kaɗai ya sani, wai nan ai ni nake dakatar da shi, Kuma dan ban taɓa gani ba ai yana kai hannu jikin su kawai bana tabbatar da abin da nagani ne sai abun ya dinga min kamar gizo suma muna fukan yaran inna tambaya Sai suce Idona bai ganin min gaskia ba"momah ta furta ranta a ɓace.
Chapter 14 · 0% Book details