← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 21

Sashe 2

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momah har ta yin ƙura zata miƙe Dan aiwatar da wani abu, ko mai ta tuna sai Kuma ta koma ta zauna da tunanin ai yau dai shikenan ƙarshen tuka tukaTik, ta faru ta ƙare, babu abin da ya rage kuma daga yau zata samu nutsuwa zuci da Ruhi Har ta dinga bacci da ido biyu har da munshari...

Sameer Dai wani hoto ya zama ga farin ciki da tausayin su d yaji gaba ɗayan su ya kama shi.

Suna kukan nan haɗe da murmushi suka wuce ƴan biki har zuwa sa shin mommah suka mai rakiya har falon ummah da yake jinta tamkar mahaifiyar Shi Ko fiye da mahaifiyar ma saboda wasu dalilai..

"da sauri ƙannen shi na ɗakin suka taso suma suka rungume shi suna mai murna samun ƴancin kai dan su haka suka ɗauki auren nashi har umman ma duk da bata da tabbacin ze zauna da wacce aka mai dole da ita, Amman tana mai fatan samun nutsuwa da kwanciyar hankali da ita.

Ganin ba rabuwa da shi zasuyi ba ummah ta miƙe ta kamo hanun shi, tayi ɗaki da shi dan gabatar da nasihar da take son yimai.

Har za su bita, ta musu gargaɗin Kar wanda y shigo mata ɗaki, sai suka dakata suna ta murmushi da farin ciki...

Sameer Ma waje y samu ze zauna sai ummah tace "aa Sameer zo mana Ai Har kai za'ayi aikin kai ai yarjajen mu ne bani da matsala da kai ko na sisin kwabo shigo Ina son ganin ka ai kaima" da sauri y fasa zaman ya bisu yana gyara rigar shi su hussy suka bushe da dariya.

Bayan sun zauna, Ajmal ya zauna a gefen ƙafar ummah, ba yadda ba tayi da shi ba ya zauna a kujerar ɗakin ko kan bed side drower Amman Yace "a'a" dan yana ganin ta cancanci duk wani ladabin da ze mata.

Dan har ji yake kamar ya sa kanshi a kirjin ta ko zai ji cewa ita ce mahaifiyar shi ba mommah inda kuwa zata rungume shi yaji dumin ta ze iya ƙarya ta mommah ce mahaifiyar shi ba ummah ba,saboda yadda yake ji a cikin zuciyar sa tun tasowar sa har yau ɗinan da ya kamata ace farin ciki zeyi, Amman babu wani farin cikin da yake d Auren.

Ummah ce ta katse mai tunani da faɗin "Son duk wani abu da zan gayama na riga na gama gayama shi tun kafin wanan rana, dan Allah tun a yau ka sa a ranka zaka yi ibadar zaman Aure da tsarkakakiyar niya ka cire tunanin bin umarni ko cutar da kai, duk bana so ka gina tubalin auren ka da wanan, wanan shine iya abin da zaka min in har ina Amsa sunan uwa a gareka, Amman fa ba umarni bane, son shawara ce"karon farko d ya ɗago ya dube ta idanun shi tab da ƙwalla kamar ƙaramin yaro, ko macen da akasa a gaba ake mata faɗan zaman aure, tunanin shi furucin nan daga bakin mommah ya kama ta ya fito Amman sai gashi a bakin kishiyar uwa kuma wacce take zame mai sanyin idanun shi,a duk lokacin da mahaifiyar shi ta guma mai...

Gyaɗa mai kai tayi, gani ya ɗago yana kallon ta, ta sake cewa "eh ba umarni bane shawara ce dan bansan me zaka tarar ba bare nace ma umarni in nace umarni ka tarar da abun da bamuyi zato ba ai an cutar da kai da yawa, Amman ina ma fatan Alkhairi a yau d gobe da jibi da ko yaushe ma, kaba mara ɗa kunya, ka riƙe sirrin Gidan ka koni sai ya zama dole sanan zaka sanar min, ga Sameer Nan ya riga ka aure wani abun zaka iya neman taimako ko shawarar shi kafin ni, kuma ga mahaifiyar ka nan ma gaba take dani kullum ina tuna ma, ka manta a abin d ya gabata, abin da zezo gaba ake dubawa, uwa uwace ba a sake ta sai dai madadin ta ko ace a rashin ta, to kai baka rasa ta ba, kuma d izinin Allah lafiya zaka rabu da ita, wata rana zaka ji daɗin ta" sosai ummah ta mai nasiha har a ƙarshe ya saki kukan da yake ta riƙewa, har ya kamo hannun ta ya damƙe cikin nashi, ta kwantar mai d kai akan cinyoyin ta tana shafa mai gashin kai, alamar rarashi kamar ƙaramin yaro, tana mai addu'a tana jin inama ita ta haifi Ajmal da beyi irin rayuwar d yayi b da yasan uwa ce gatan ɗan ta a duniya ko yanzun ma tasan tayi iya yin ta akan shi wani abin ne dole ta zuba mai ido.

Sosai yake kuka, dan ya ma manta rabon da yaji ko yatsan mahaifiyar shi a jikin shi koda ace ta mare shi ne, baze ji zafin marin ba sai dai ni'imar da ke hannun da Albarkar, kash! Amman ya jima rabon da yaji yatsun nata ma a kuma tun shi da sunan hukuncin da besan meye laifin shi ba, tun dai wani lokaci da ta mai marin da sai da yatsun ta suka kwanta a fuskar shi, har mahaifin shi ya rama mai ta kusa mai baki, akan hana ta sake samai hannu a jiki da mahaifin yayi, baze manta ba shine rabon da tasa hannu a jikin shi, sai yanzu yake jin dama ta cigaba da watsa mai yatsu biyar ɗin ko zasu zamar mai tabarakin uwa.

Sosai yayi kuka ummha da Sameer suka rarashe shi, ga abokanai da suke ta mai waya yasa ta a silent Sai damun Sameer da waya da suke yi dan zasuje ɗauko Amarya Ne. ..

Ummah ce ta kama shi bayan ta gama rarashin shi ta goge mai fuska da tissue ta sake fesa Mai turare mai ƙamshi da tsada, ta kamo shi tamai rungumar gefe duk Dan yaji sanyi a ranshi d ƙarfin gwiwa ta fito da shi, mutane suka fara guɗa ana mai dariya har da masu musu hoto da vedio, kowa ya gansu sai sun birge shi kamar uwa da ɗan ta kawai kama ne da ba sayi kwata kwata da babu mai cewa ba mahaifiyar shi bace.

Su huusy da hassy da Safiyya da safna yaran ummah ne suka ce "yaya Sameer mudai abamu motar Mu da ban muje ɗauko antin mu Mai ƴar baiwa da iko" wata harara tare da gargaɗin ya Ajmal ya wurga musu.

Ummah ma ta ƙara da cewa "ana ta babbakar giwa wake jiyo ƙaurin zomo, kudai bar manyan ku suje ku waze wani baku Amarya duk babu wacce ta yunƙura a cikin ku" sai ko wata aunty kubrah kanwar ummah tace..

"haba aunty Rai dai sai mun sha shagali kika sani ma ko lokaci ɗaya zamu miƙasu" Sai ko suka fara cewa "eh mana Allah yasa banda safna da hussy dan sunfi kunya acikin su" daƙuwa ummah ta musu suka ɓoye fuska.

Sameer Yace "OK, ku tsaya barin ma Khalifa magana sai ya kaiku dan yafi muba nutsuwar tuƙu, waze hanaku ɗauko antin Ku Ai sai da ku ma za'a bada ita suma gidan su dole su san tana da ƙanne masu capacity" da wata muguwar harara Ajmal ya bi shi.

Dan y ƙarama Ajmal ɗin haushi ya sake cewa "to kunga ango mai capacity yana harara ta naƙi tafiya na ɗauko mai Amarya mai capacity sa, sorry ango mai...." bai ƙarasa ba Ajmal ya fara neman abin da ze wawura ya jefe shi da shi, tuni Sameer ƴa arce ya fice daga falon ummah nata mai dariya, ta karɓi filo kujera da Ajmal Y ɗauka d ze wurge shi da shi, ta ajiya tace ya zauna kar ya kula su, ya barta da su duk ta ishe su har Sameer ɗin, Ango Ai baya kula ƴan tsokana.

Nan Akazo aka ɗibi wasu tsirarun ƴan uwa aka haɗa da su hussy aka tafi ɗauko Amarya a akwota nan sai a wuce da ita gidan da mai matsayin Uwar Amarya ta basu dan su zauna ita da angon ta a aka musu Auren haɗin wasu kuma suce na dole ko na manufa.

Aboka nan shi ne suka shigo da suke jiran zuwan amarya sai su tafi can gidan, ganin yaƙi fitowa, wani shadow Ne a cikin su ya fara cewa "Kai malam y kamata fa kasan ka girma yanzu kayi bye bye da su ummah, yau dole a tafi gidan...." be ƙarasa ba Ajmal ya mai wata muguwar harara, sai shima ya ankare da umma da take gefen shi kar yaje yayi katoɓara, Allah ma ya taimake shi be furta abin da yake son firtawa ba.

Nan suka fara gaishe da ummah ta amsa tana ta shi musu Albarka, ta tashi ta bar su da Ajmal ɗin.

"kai wai meye haka naga kamar kuka fa kayi mutumina?" Sa'ed ya faɗa.

Shadow Ne ya bashi amsa da "ba dole yayi kuka ba, yayi babban kimu kai kifi daga sama gasashe fa, Alkhairi fa yake ciki dumu dumu kai inda nine n samu gatan da gayen nan y samu za'a ga bura uba ina gaya ma, ga gida ga mata ga gara fa lefe ma fa yafe mai akayi kana gani mu lefen ma shi yafi damun mu dan shine hargitsa lissafin gaye Yanzu da tuni mun ɗauko rigimar nan Muma, Amman babu komai tunda rabo y fara zuwa kan abokin mu da sannu zezo kammu muma"

"banza ɗan cima zaune, irin ku ai basa samu, musu dogon buri" sa'ed Y firta Yana hararar, shadow.

"kai wlh ka tofar da mugun yawun ka, abun rabo ne fa" shadow Y bashi amsa.

"kai dallah gara kai kullin cikin shirme kake wallahi badan nasan baka tsotsan Komai ba da nace yau kasha over, tun ɗazu ka ishi mutane, Ai d ka sani da, da kai aka ɗaura" inji Ajmal da duk surutun shadow ƴa ishe Shi.

"Auzubbillahi! Kar kayi Sabo fa, matar ka ce fa? Kuma ka sani ko ka fara bani a yau bikin ka na Afa, Kai fa wani lokacin sai a rasa gane kanka, Sameer Ne Kawai yasan makunin ka da wajen seta ka" shadow Y firta Yana zama kusa da shi ya fara mai raɗar da iya su biyu ne kawai suke ji.
Chapter 2 · 0% Book details