← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 21

Sashe 18

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanan Abbah huɗu aka sallame shi, ya koma gida duk yadda yaso komawa kasuwa ummah da Ajmal suka hana shi.

Hasana da su safna kullin cikin Yima Abbah hidima suke Har ya samu yaji sauƙi bayan sati guda ya koma kasuwa Ajmal ya koma makaranta.

***
Momah tunda kawu yaji labarin sakkn ta sosai tasha faɗa har wajen wasu ƙanen maman ta dan ita aka dinga ba rashin gaskia, musamman da suka kira Abbah ya gaya musu irin raina shi da tayi da takura ma Ajmal da take kamar ba ita tahaife shi ba damma ya saya bai faɗa musu dalilin tsangwamar ba dan luluɓe asirin ɗan shi karya mai tereren bankaɗa, itama momah akaci sa'a Bata faɗa musu ba sosai tasha faɗa zaman ƙyauyen duk ya addabe ta, sai da sukayi waya da su hassana suke gaya mata rashin lafiyar baban su shine taji bata kyauta ma kanta ba duk da bata sauka kan batun ta ba na Ajmal da fitinar shi, taji babu daɗin sanadin ta ciwon Abbah ya tashi tama kira shi ta duba shi yaƙi ɗauka Sai da ummah sukayi magana, Ajmal ko ya kira ta yafi so nawa bata ɗaga kiran shi har ya gaji ya haƙura sai dai in suna waya da su hussy susa a hands-free Sai yaji muryar Tata hankalin shi ya kwanta in ya tabbatar tana lafiya, yaso zuwa ƙyauyen tunawa da yasan bazasu kwashe da daɗi ba sai ya haƙura.

Zaman momah a ƙyauye da sati guda rak sai da ta gane shayi ruwa ne, bata tashi tuna gidan Abbah canji ne da ta samu mai daɗi da take alfahari dashi tun barin ta ƙyauye sai yanzu da ta dawo da zama ba ziyara ba, da ƙyar take iya wanka a bayi mara rufi gashi dai anan ta taso, Amman duk ta manta, mutanen ƙyauye ana samu masu hankali da tunani mai kyau dan wasu da dama sunfi na birnin zurfin tunani da sanin ya kamata musamman in suka sami kulawa da ilimi ko damar ilimi na arabi da bokon, momah ta sami ko wane dama daga ciki tasa ƙafa tayi fatali da shi musamman da taga aure zatayi ta tafi birni ji take da ta shiga birni bata buƙatar komai kuma sai zaman aure ko da ta fuskanci tana buƙatar ilimi na addini da na zamani girman kai ya hanata komawa ta samu duk yadda Abba yayi da ita kuwa haka har ya haƙura tunda bata rasa na sallah ba.

Da gari ya waye tayi tozali da waina zallah Ko tsuran kunu Mara kauri Sai taji hankalin ta ya tashi, duk yadda taso cin mai daɗi sai ta kasa tasan faɗa zata sha wajen su kawu, dan shi ne ya bata ɗaki guda a ɓangaren shi ta share da ƴar katifar yayi take kwanciya akai, da Raha ne take samun taliya da mai da yaji ko ɗanwake ko shinkafa da wake dan suna nuna mata karamci irin na ƙyauye dan ƙyauye badai karamci ba, dare nayi kuma zata samu ciyarar cima irin su (Arne da kote) Tuwon dawa miyar kuka (baƙin dogari ) Tuwon gero (ci iya cinka) Tuwon masara Haka za a mata jerin gwanon su saboda gata sai wanda ta zama da miyoyi kala kala harda zawo salamu alaikum, miyar yauƙi tafi samu ta tsakura gudun kar ulcer ta ta tashi.

Momah ta jigata a wanan zaman mahaifar ta da ta manta dashi ta ma waiwaye da bata san ranar barin ta ba, sai in ranar kasuwa ne take samu a siyo mata su balagu da kilishin tsummah (wani kilishin da zaka iya rantsuwa kace da bargon rufa akeyin shi ko kwaki Ko tsummah ka rasa yadda zaka sashi a matsayin kilishin da ka sani) ko na kitse sai su rake shine take samu ta maida mugun yawu, ranar da ta bada kuɗi ayi girki a gudan har kusan so biyu kawu Sawa yayi a mayar mata da kuɗin ta wai tayi haƙura ta tuna baya suci abin da suka rayu akai tun kaka da kakanni ranta ba ƙaramin sosuwa yayi ba da haka, sai bata sake ba, rayuwa taci gaba da gara mata a haka tana juriyar dole tana zuba ido kullin taji ko Abbah zece ta dawo ɗakin ta shiru.

Wasa wasa sai da momah ta kwashe kusan wata uku a ƙyauyen Garko sanan su kawu suka dinga ba Abbah haƙuri, gani ta gwaru Har ta magantu, gasu ummah da su Ajmal da suka dinga mai magiya sanan ya haƙura, yace ta dawo, da ummah da Ajmal da su hassana aka je dawo da ita dan shatan Sharon suka ɗauka aka cikasu da tsaraba kuwa su hussy ji sukayi kamar kar su dawo, safna ma ƙyauyen ya musu daɗi.

Bayan sun dawo zaman yaci gaba kadaran kada han tsakanin Abbah da momah, Ajmal kuwa daga gaisuwa baya dogon zance da ita dan ko yaje I zeyi awa nawa Bata janshi da hira har sai ya gaji ya haƙura, sai shima yake sake ja baya da su hassana dan yasan jira take yayi abu dole zata magantu dan ya fuskanci bata gama nadama ba, dan haka zaman shi da hura tafi a ɗakin ummah har ake jin shi yana dariya.

Bayan wani lokaci halin momah ya dawo ganin Abbah ya saki jiki da ita, tun da ta fuskanci shaƙuwar su tana nan babu inda taje ta dawo da tijarar ta na ya Dena raɓar mata yara, haka ya dinga haƙuri da ita.

Abbah ma ƙaleta yayi da halin ta, ya dena kula ta doka ɗaya ya mata karta sake sa hannu a jikin Ajmal dan ya wuce duka, to taji wanan Amman ko ƙofar ɗakin su hussy ta ganshi ko sallah take zata yanke ta mai iyaka, ƙarshe shima ya Dena zuwa kuma in yana halin yanayin halittar shi baya zuwa wajen ta sam sai har ya sami kanshi ya dawo daidai dan da wuri take gano shi.

Wata rana ciwon mara ya addabe shi tun yana daurewa har ya kasa ko fita ya kasa Abbah ne yaje ya fara duba shi koda ya sanar ma momah sai cewa tayi "ai Jarabar shi ce a ƙoƙon rai bazai fasa ba" haka kalmar tama Abbah ciwo da Taimakon ummah da su safna har sa'ed aka kai shi asibiti aka bashi gado da ƙyar momah tabar su hussy sukaje duba shi, sa'ed shi ya dinga jinyar shi da Taimakon ummah da su safna, dan Ummah tace Abbah y kula da kasuwar shi kawai ya dinga mata godiya, momah ko so ɗaya bata je ba, har aka sallame shi tare da shawarwarin likita ya bashi wasu magunguna da zasu rage mai yadda yake ji da abin da ya tarun mai a mara, tun daga nan da yaji ɗan dama-dama sai ya sarƙafi Dr yake ɗan bashi abin da bazai zamar mai illah Ga lafiyar shi ba da shawarwarin da wani lipton da yace ya dinga amfani da shi da laimun tsami sanan yake samu sassauci duk d ba ko yaushe Dr yake bashi ba.

A haka rayuwa taci gaba da gyarawa har Ajmal ya kamala karatu ya tafi yin NCE dan Lokacin inda karfin shi ya kai kenan dan Abbah ma babu duk ƙoƙarin da yake wani lokacin abin sai addu'a, su safna ma sai da aka canja musu makaranta daga private suwa community school, private Mai sa hanun gwamnatin aciki haka suka dinga lalaɓa rayuwa, Ajmal nata zuwa kasuwa kamar wasa Wani abokin Abbah ya ɗauki Ajmal suke aiki tare in baida makaranta suna harkar kayan sololi, Abbah yaji daɗin hakan kuwa, shi kuma Abbah suna bakin hanya da nasu shagunan da babu wasu kaya aciki sosai.

Ana haka kwatsam iftila'in rusau ya faɗa ma su Abbah aka rushe Shagon su Abbah, duk da an basu notice, Abbah Basu ɗauka da gaske gwamnatin take ba, wai shagunan ba bisa ƙa'ida take ba, su da da suke da shaguna cikin kasuwa da wajen ta, sai gashi yanzu ɗaya ma za'a raba su dashi, wanan damuwar abbah yasa a ranshi har ciwo shi yake neman tashi.

Ana haka kuwa sanarwa tazo a daren ana washegari za'ayi rusau ɗin, sa'ed ne yaji a majiya mai ƙarfi kafin sanarwan gidan TV da radio abbah kuma ma'abocin jin radio ne Ammah ranar yasha maganin hawan jinin shi da wuri bacci yayi gaba da shi dan short notice aka Basu, shine fa hankalin Ajmal ya tashi ya rasa ya zeyi yazo ya sami ummha da maganar ganin Abbah yana ta bacci.

Suka yanke shawara da ummah akan suje su kwashe kayan ciki kar abin ya musu yawa dan duniya babu yadda ƴan ganima suna gefe suna jira, ummah da kanta ta ɗauko mai makullin Shagon suka tafi da akori kura suka samu kuwa masu dabara suna ta kwashe kaya Ajmal ɗin ma yace, Abbah sa ne ya turo shi dan yana gida baya jin daɗi, sukace Ai suna ta kiran wayar shi bai ɗauka ba, basu san ummah ce ta saka wayar a silent ba dan Kar adame shi yasha magani ya kwanta.

Tas su Ajmal suka kwashe komai na Shagon har kuɗin da Abbah ya ajiye a Shagon, suka tafi gida aka zuba a ɗakin Ajmal ɗin ba tare da momah ta sani ba dan yasan ma bazata bashi listing ears ba dan Haka bai shawarce ta ba..
Chapter 18 · 0% Book details