← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 21

Sashe 6

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ƙawata base na Kira Ki ba kema bance ki kira ni ba da sanyin safiyar nan, na miki saƙon nan ne kawai don Naji kin kwana, lafiya, ko kin kirani ma bazan ɗauka ba, Amman anjima ko gobe zanzo, Ina muku fatan Alkhairi keda mijin Ki" shine abin da ta rubuta mata.

Sosai ta sake murmushi gami da ajiyar zuciya a karo na biyu, sai taji kalmar miji ta tsaya mata a rai.

Tasan ko ta kira haly ba ɗagawan zatayi ba tunda tace bazata ɗagan ba, dan haka batayi yunƙurin kiran ta ba.

Ajmal sosai ya zazagaya unguwar har sun gaisa da wani maƙocin su, yake tambayar sa badai shine ango gidan ba, Ajmal ba dan yaso ba ya amsa mai da shine, dan mutumin akwai surutu shi ya ɗan ja Ajmal ɗin ma da hira har ya ɗan jima a wajen, Amman kuma ta wani gefe yaji daɗin surutun mutumin Dan ya nuna mai masallatan unguwar har guda biyu da kantunan unguwar saboda siyaya Sai surutun da be tambaye shi ba, kaf sai da ya mai bayanin maƙotan su har da sana'ar da kowa yake yi da iya adadin da matan da kowannen su yake aure, banda yaran gida shima dan Ajmal ya dakatar da shi, ne, ƙarshe yaso sanin sana'ar Ajmal ɗin, ataƙai ce yace mai shi ƙaramin ɗan Kasuwa ne, sukayi canjen number da maƙocin ya nema, Ajmal ya bashi second number shi da be fiye amfani da ita ba dan baya son damuwa, Yamai sallama suka rabu, har yana Agaida Amarya, Ajmal Ko amsa mai beyi ba ya shige gida.

Tun dawowan shi gidan yake ƙare ma gidan kallo, babu laifi gida yayi komai ya ƙawata gidan babu wanda ze kushe har da filawowi da parking space ɗin da mota biyu zasu iya tsayawa ga shi gidan na ɗauke da 3 toilets Ne 3 bedrooms one parlor Sai dining area, Ko hasidin iza hasada yasan Gidan ya wuce a kushe, Amman babu yabo babu fallasa Ajmal yake bin gidan da kallo har ya shiga falon ya koma ɗakin shi yana tunanin meye makomar shi da yarinyar nan ne wai ya suke so yayi ne mommah da iyayen yarinyar?

Rasa amsar da zeba kan shi yayi dole ya ɗauki wayar shi ya kunna data ya fara ganin saƙonin da abokanai da ƴan uwa suke ta mai Allah ya sanya Alkhairi, da godiya da Amin ya dinga bin su.

Daga baya sukayi waya da Sameer, akan ze fita kasuwa Sameer na ta hanashi, Wai uwar me zeyi a gidan in ya zauna, har suka kusan faɗa ma, Sameer ƴa kashe wayar shi.

Har rana ta farayi Ango da Amarya ana wasan ɓuya, suna zaman ɗaki, Jumana kuwa sai da ta gaji ta kira haleema ta dinga mata magiya shine ta amince tace zata zo to, dan babu wanda yazo anan ta sake gane cewa lalai bata da gata sai daga wajen Allah, bayan haleema tazo tana ta bugu jumana bata ji ba sai Ajmal ne ya fita yana tsaki yaje ya buɗe mata, suna ganin juna, kowa ya tsaya na yana ma ɗan uwan shi sannu, ya bata hanya ta wuce tana gaishe shi, tana tambayar shi Amarya yace tana ciki amai makon yace tana lafiya.

A kusan tare suka shiga falon, ya wuce ɗakin shi ta wuce na jumana, yana jin yadda jumana ta rungume ta tana murnar ganin ta daga baya ta rushe da kuka haleema na rarashin ta. Ajmal ya taɓe baki yana kukan daɗi kike ni dama zanyi kukan da ba kwaɗo ba inji gaya.

"baby meye kuma na kuka nifa indai haka zaki dinga yi wlh sai na dena zuwa dan bazan dinga zuwa ina sama mijin ki amaryar shi kuka ba" dake tun suna school d baby suke kiranta sunan d Dady ta yake kiranta da shi tayi ta shagwaɓa.

"miji Hmmm ke kika ga wani miji, ni wallahi da ina da hali yanzu tare zamu bar gidan nan" jumana ta furta tana turo baki.

"ke asiri kike son tona ma kanki? Kar ki ƙara maimaitawa, Aure fa ba abin wasa bane, kiyi haƙuri baby da sannu komai ze zama tarihi in sha Allah," ta furta tana shafa mata baya, alamar rarashi.

Sosai haleema tafi jumana Wayo sakamakon suna da banbancin reno, ita haleema a tsayayye gida ta taso kuma na masu ƙaramin ƙarfi kuma ta taso cikin yayu da ƙanne, ita ko jumana a gaban mahaifin da da mahaifiyar ta a sangarce da gata ta taso duk da mahaifiyar ta na ƙoƙarin seta ta da ganin tayi mata tarbiyar tsayayya da ɗanka ze iya rayuwa a duk halin da ya tsinci kanshi, dadyn ta ne yake shagwaɓa ta, dalilin da yasa hakan duk ya ja mata shiga wani taskun rayuwar bayan barin mahaifan ta duniya riƙon ta ya koma hanun mum/hajiya, ƙawayen ta kuma su kira da da hajiyan shagali...

"yanzu dai meye matsalar gaya min, Wai ma kinyi breakfast kin ba mijin Ki?" haly ta wurgo mata tambaya.

Amsa mata tayi da "breakfast Kuma? Tab! Mutum da bama yaso mu haɗu, ke Nifa kowa ta kanshi yake tun jiya da kuka garƙamemu gida ɗaya, bance mai ba be ce min ba, ke ni badan badan ba ma mu ta zama a hakan"

"kai wai kina nufin ko gaisa wa ba kuyi ba, Naji ajiya shi ya kamata ya fara nemann ki da be nemeki ba be kamata ki neme shi ba yau kuma ke ya kamata ki gaishe shi ki bashi abin da zeci ko da bazeci ba kin fita, dan akwai abokin shi Sameer da Ko sa'ed Ne suna da kirki wallah ya nuna min kayan tea da su indomei Har da su ƙwai da ya kawo dan ni na adana miki ma a kitchen da hannu na kinƙi nutsuwa ne jiya Sam har na tafi bamuyi maganar ba" Halima ta faɗa.

"to ai ni dai...."

Haleem ta katse ta "ke me? Ni fa baby in da bamu sami matsala da ke ba yanzu ne zamu samu, saboda ina gano miki ƴanci da kika samu ke kuma baki gano ma kanki, and Ko babu komai nan gidan d kike ɗaukan mijin ki kamar maƙiyin ki yafi zama da hajjaju, ki faɗi tsakani da Allah?"

" umm eh nima na sani, but..... "

" but what? Ki fara mu'amalantan shi kafin ki yanke mai hukunci, kin san dai babu yadda za'ayi ya zama wicked Kamar wanan mamar taki....."sai kuma haleema ta dafe goshi.

" eh da hakan ze kasance zanfi farin ciki, Amman fa ba'a gane maci tuwo Sai miya ya ƙare, taya zan fahimce shi ya rufe duk ƙofar da zan gane hakan? Halee"

"baki so bane Ai da kin samu, ni wlh da inada yadda zanyi da nasa ya dawo dake hayyacin ki Ko ta hanyar......" sai Halee ta yi shiru ta kasa ƙarasa wa.

"ƙarasa ko ta hanyar ya min fyaɗe ko shine abin da kike son cewa? To wai dan Kinga ina yawan ce miki ina Jina cikin wani yanayi na buƙatuwar..... " haleema bata Bari ta ƙarasa ba ta rufe mata baki.

" ya isa ba haka nake nufi ba mubar zancen kafin ki fara min kuka, yanzu tashi muje kitchen mijinki yaci girgin Ki kai ko baze ci ba ai baze ce ba a bashi ba" har jumana zatayi gardama Halee ta girgiza mata kai, ta kamo ta badan ranta naso ba, ta nufi kitchen da ita.

09064271655
[08/12, 7:51 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*

Free book....

Shafi Na 6

Maman shaheed (Fatima Abubakar)

_ANGO DA AMARYA_
Jumana da Haleema suna fitowa, lokacin da yayi daidai da shigowar Sameer da Ajmal Yake buɗe mai ƙofar falo.

Sameer da sallama ya shigo, haleema ta amsa, jumana da Ajmal kuwa kowa wani saƙo yake ji atare da shi kamar masu tsararbar aljannu, kowa ya kasa kallon ɗan uwan shi, sai da haleema ta wargaza shirun nasu da fara gaishe da Sameer, da fara'a ya amsa ya ƙarasa shigowa falon yana kallon jumana yana mata murmushi, can yace "Amarya barka dai da fatan a tashi lafiya?"

Wani kallo Halee ta mata sai taji ƙarfin amsa mai yazo mata "lafiya lau ya gida y gajiyan ku?"

Wani kallo Ajmal ya mata kallon da besan yayi ba jin sautin zazaƙar muryar ta da kuma tambayar gajiyar su Sameer, it means ma ta ƙarɓi Auren har da ban gajiya take ma wasu?

Karaf idanun su ya gauraye dana juna ita da Ajmal wani ƙyalli suka gani ya fito daga idon ta ya faɗa nashi itama haka ta gani da sauri ta sunkuyar da kai tace "ina kwana? Ajmal kasa amsawa yayi sai wata kasala da ta saukar mai, kawai ya kama hannu Sameer yace," Muje ko? "

Sameer Ne ya Amsa ma jumana, da" a ai babu gajiya Amarya, gashi zan ɗan aran miki angon Amman ba jimawa zamuyi ba zan dawo dashi har gida"

"uhumm" kawai ta iya cewa kanta a ƙasa tana wasa da yatsu ta da suka sha lalle ɗan uban su.

Haleema ce ta iya magana "OK to sai kun dawo dan Amarya girki zata ma Angon ta for the first time, Kar ƴa jima dai" tasa dariya tana kamo hanun jumana sukayi kitchen.

Ajmal gaba yayi dan baida lokacin sauraron abunan, Sameer Ne ƴa Iya mayar mata "OK, lalai ko dole yaci girkin nan, Ango na godiya, bari muje da saura dan ya dawo on time" Sameer Y bishi waje Yana mai mitar y Dena abun da yake yi.

_Sameer & Ajmal_

"Dr Nifa banda niya Kawai aimin abin da ya dace, dan babu wani abu da zan iya yima yari.........."
Chapter 6 · 0% Book details