← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 21

Sashe 10

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama ta shiga kanta a ƙasa wanda mugun ƙarfin hali kawai take yi "Assalamu Alaikum, yauwa dama Suhail ɗin ne ya ƙaraso yana jiranka a falo" ta tsinci kanta da haɗe mai a dalilin zuwan nata da ta kasa haɗa ido dashi, tun shigowar ta.

"OK, Ganinan, kika ce yayan kine ko?" shima ba tare d ya kalle ta ba yana latsa wayar shi dan kawar da abin da yake ziyartar shi tun shigowar ta da jin ƙamshin turaren ta mai sanyin ƙamshi na mata ba maza ba.

Da sauri ta ɗago ta kalle shi har ta sami damar ganin me yake yi da ganin ɗakin tsaf ba kamar ɗakin suhail ba d yake baza kaya in a sata ta gyara mai, sam be iya kintsa Komai ba kuma shima ɗakin da ƙamshin shi mai daɗi, sai tayi saurin cewa "A'a ƙanina ne dai nace ma"

"OK" ya sake cewa, sai ya miƙe, sai tayi saurin juyawa da niyar Barin ɗakin tajiyo muryar Shi Yana cewa "Dafatan dai ba irin tsagerun yaran nan bane dan ni ba komai zan iya ɗauka ba abarni Naji da abin da yake Damuna ma"

Tana shirin fita duk da maganar ta mata wani iri Amman sai tace "In sha Allah baza ka sami haka daga Abeed ba" sai tayi sauri ta fice, sai ta bar shi da tunanin toh shi suna biyu ne dashi? Ance Abeed Ance suhail? Neman ta yayi ya rasa kawai sai y fita ya ita dan yaji dai dame yazo.

Bayan jumana ta fito sai, tace ma Ajmal "broh Gashi nan fitowa y su mum? Hope Dai babu wani issue nagan ka..."bata gama firta abin d zata furta ba, taga Ajmal y fito sai ta miƙe dan kawo ma Abeed abin sha.

Shiko suhail tun fitowar Ajmal yake kallon shi, shi kuma Ajmal ɗin kallo ɗaya Yamai y ɗauke Kai, suhail ko hamdala yayi da murnar ganin irin mijin nunama sa'a har maƙiya da jumana ta samu a ƙoƙarin cutar da ita da aka mata mugunta aka bata, Ajmal ba mumuna bane gaye ne Iya gaye baida makusa Ko kaɗan Sai dai d ake cewa dan adam tara yake be cika goma ba, Amman da gani za'a sami abin d akeso daga Ajmal, dan sun ma dace da junan su sosai, sai yaji zaben da aka mata ma da sannu ya zamar mata Alkhairi, duk d besan y shi ya karɓi Auren yayar tashi da kullin ake nuna basu da alaƙa ba shi kuma yasan duk duniya bashi da ƴar uwa ko ɗan Uwa Najini sai ita.

Sallamar da Ajmal Yamai yana miƙo mai hannu ne ya tsayar mai da duk tunanin da yake.

"ya gida?" Ajmal y tambaya.

"lpy lau y kuke taro y tashi lafiya? To Allah ya sanya Alkhairi y baku dawamamen zaman lafiya y baku kariya daga dukkan sharrin mutum da Aljan da..." sai Jumana tamai wani kallo tana mai nuni da kar ya furta abin d yake shirin furtawa akan hajiyar su, sosai y fahimce ta, dan baya so y bar mata tabo a gaban mijin ta duk d yasan yau da gobe doke ze fahimci mahaifiyar shi muguwa ce mai baƙin nufi akan jumana.

Ajiye mai abin sha tayi dan tasan ma bazeci abinci ba gashi ma basu d wasu abubuwa sosai a gidan, godiya ya mata, tace "nice da godiya Abeed Son" karon farko Ajmal yaga yalwatacen murmushi akan fuskar ta da ta tafi da imanin shi gaba ɗaya yama rasa a wacce duniyar yake da masoyan gaske ne su ɗin d komai ze iya faruwa.

"Hmmm kema? Kin ɗana ko? Zaki tunamin abin da ya wuce ko? Hmmm ki bari naki ko nace naku son ɗin yana hanya ke da wanda Allah ya fimu sanin dalilin da yasa aka haɗaku a ƙarkashin inuwa ɗaya wacce muke muku fatan ta zamar muku Alkhairi abin alfaharin ku in sha Allah "
Kusan a tare Ajmal da jumana suka kalli juna jin suhail na neman sakin layi, Wai son ɗin su, har yaushe akayi daren da gari ze waye? Shiko suhail kan shi tsaye yayi furucin dan baida kwana kwana kuma ba da wata manufa ya faɗa ba har cikkn ran shi, suko idanun su ne ya gauraya da na juna wani sihirtacen saƙo ya ziyarci illahirin jikin su ba tare da shawarar junan su ba.

Ajmal ne yayi gyaran murya y fara tambayar Abeed y karatu? dan ɗauke waccan maganar.

"Alhamdulillahi karatu muna can nesa daku muna tayi yanzu ma a hanyar komawa muke kamar fulanin tashi"

"yauwa dan yayan mu har aunty na JUMANATU dan Allah Kar ka ɗauki abin da zan faɗa maka a matsayin iyayi ko wani Sana be Ko kaji Kamar ban kai ba,a hankali zaka fahimci dalilina nayin hakan"

"OK, inajin ka faɗi duk abin d yake ranka" ba yabo dai babu fallasa, sai suhail yayi tunani ko dan basu saba bane.

"Dan Allah yaya dan Annabin shi wanda yafi kowa d komai, dan Allah ka riƙe min Amanar Jumana, ka tausaya Mata ka hana ta maraicin mahaifiyar ta da mahaifin ta, kai taimake mu ka zamar mata gata na nunama sa'a ko duk wani maƙiyi, in ka mana haka ka mana komai kuma nasan kana da rabo mai girma a wajen Allah in sha Allah, jumana ma ina baka tabbacin zaka sameta yadda kake so bata da matsala Amman zaman ku ze tabbatar maka da hakan dan nasan mai biyayya ce in sha Allah bazara baka ciwon kai ba sai da dalili, shine dalilina na zuwa gidan nan dama b komai ba dan ni da ku sake ganina sai abin da hali yayi"

karon farko AJMAAL ya saki murmushi da be shirya mai ba, yace " karka damu a tayamu da addu'a, Wai kai ba ka kusa gama karatun ba? In ka gama kuma ai gida zaka komo"

"Hmmm yaya karatun mun kusa gamawa ina final year ɗina Ne Amman dawowar ce akwai abin d zan ɗanyi ne acan" y firta d alamun Kamar Yana jin zafin furucin da yake yi.

"OK, to Allah ya sanya Alkhairi da Albarka a karatun, Amman kar ka damu khairan in sha Allah"

"yauwa nagode sosai, Yaya jumana dan Allah ni b faɗa zan miki ba dan ƙani nake a wajen ki duk da in gaskiya tazo ko ɗa na iya ma mahaifan shi tuni, to nasan baki da matsala ki cire komai a zuciyar ki ki fuskanci rayuwar ki zabuwa da nake miki fatan tafi ta baya da kikayi da sannu zakiga Alkhairi hakan dan Allah baya haɗa ma biyu indai kayi imani da sannu zakici jarabawa, fatan Alkhairi nake miki a koda yaushe"

"to suhail nagode in Sha Allah, Allah y taimaka ya baka kariya ya tsare maka gabanka da bayan ka, Allah y zama gatan ka acan, ɗan Allah ka dinga kira na, ka Dena canja layi..." Jumana taji ya katse ta.

"canja layi kamawa take yi, za dai ki dinga jina in buƙatar Hakan ta faru, kar ki damu da kowa a yanzu sai mijin ki dan Allah" Suhail y firta Mata.

"OK in sha Allah" ta amsa mai.

"yauwa, toh ni yaya zan tafi fatan Alkhairi, sai gani na biyu, nagode sosai" suhail y miƙe, jumana ma ta miƙe idon ta na shirin fitar da ƙwalla, suhail d Ajmal duk sun gani Amman suka ɗauke kai.

Har waje suka raka shi wajen motar shi, ganin ta saki kukan da take da adanawa sai Ajmal yama suhail Allah y kiyaye hanya ya tafi y barsu, ita kuma ta ƙara ƙarfin kukan ta.

Har suhail ze shiga mota sai kawai ya dawo ya kamo hanun junama yana rarashin ta Har ya mata side hug Yana ce Mata "kiyi haƙuri ki fuskanci Auren ki mum bazata taɓa canjawa ba daga yadda muka santa tana nan da mugun nufin ta ba akan ki da bata san zafin haihuwar ki ba har ni da na fito daga tsatson ta, tun jiya muke rikici da ita akan me zanzo bikin ki ashe munafurta ta tayi tace yau ne bikin ki ni kuma dama schedule ɗin Komai ya same ni shine na bijire ma umarnin na taho a jiya, kuma yau zan bar garin yadda take nisanta kanta da ni, zanyi nisa d itan tunda kin bar gidan Allah y ƴan ta ki, zakuma ta nemeni a lokacin da bazata samu ganina ba dan sai ganina ya mata wahala... " be gama furucin shi ba yaji jumana tasa mai hannu a baki tana toshewa alamar yayi shiru,yayin da take ta fama da kukan takaici.

Hanun ta ya cire yaci gaba da furta" ai gara in gaya miki ne dan ki sani ko anjini shiru, abin da ta kasa min ne yanzu kika min, mum bata san ta bani Aron kunuwanta na zayyane Mata damuwa ta ba ita a lissafi irin nata kuɗi sune kawai damuwa ta, bata san ta Jani a jikin ta ba Naji ɗumin jikin ta irin na ɗa da mahaifiyar shi, na manta yaushe ne ta haɗa ni da jikin ta taji bugun zuciya ta Naji nata ba, bare tasan abun da nake so ko bana so, ita dai dole kawai ai mata biyayya da duk abin da tace koda hakan ya saɓa ma koyarwar addini, kece sheda, duk wani abu ke zaki faɗa gaskiya ko litatafai aka baki sai kin cika da labarai marasa daɗi na mum na mumuna nufaƙarta akanki to Yanzu Har ni ma ban tsallake ba, bata so n dawo Kano inna gama karatu, to ko zanyi yadda tace, Amman bazata yi farin ciki da hakan sai..."

Ji yayi jumana ta jijiga shi cikin karfin halin dawo da shi hayyacin shi, tana ce mai" uwa fa uwace suhail Kar ka bari ɓacin rai yasa ka dinga faɗan kowacce magana, nasan bata kyauta ba in da sabo ai mun saba, ni dai bana so kayi abin da baze mana daɗi bane na hukuncin da kake shirin yanke ma kanka, dan Allah karka yi abun da ze jefa mu cikin..."
Chapter 10 · 0% Book details