← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 21

Sashe 17

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"eh na gane ta wacce nace tana da hankali, kace to an rigani lokacin bakasan ma ko iya magana da ita bazanyi ba"

"yauwa to ita, Ai an shiga maganar akace a haɗa su yaya mahadi yayi tsalle ya dire yace sam, tun muna ganin abun akan ko baida ra'ayin ta ne ashe dai da magana ne shi kwata kwata ma fa baida feelings wlh da gagarumar matsala komai baya ji bata aiki kai ko maganar ma baya so amai kwata kwata, matsalar shi ya fito yayi bayani yaƙi ya tsaya ɓoye ɓoye sai da baffa da ummu suka mai da gaske har sukace ko baida lafiya ne? Shine fa suka ɗan fuskanci wani abu"

Ajmal doguwar ajiyar zuciya yayi kafin ya firta "innalillahi wa'inna ilahiraji'un, wanan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan yunwa"

"kabari Kawai to Kaga da irin matsalar ka da tashi wacce zaka zaɓa in an baka zaɓi? Abokin a" sa'ed yayi tambayar.

"kai duk babu na zaɓi biyu ne babu ko ɗaya na ɗauka haba kai kasan yadda akeji ne da nawan Hmmm mutum ya dinga ji kamar zeyi ta'adi sai ƙarfin tsoron Allah ne ze iya dakatar da shi da kiyaye wa Hmmm duk yadda za a kwantan ta ma fa bazaka gane ba"

"abokina ka gode ma Allah Kar ka budulce mai, duk fa wanda bai gode ma Allah ba zai godema azabar sa ka sani dai ko? Kai fa ko a yanzu da karanka ya kai tsaiko kana da mafita, Ina nufin Aure da ka tsiyayar kanayi akai akai shikenan ka wuce wajen, shi fa? Gayamin ta inda zeyi ma bare ya samu salama ba sai da lafiyar ba ma? "

" Hmmm haka ne kuma da dai mitsitsin sauƙi za'ace to ni yazo in rage mai ko na juye mai ma ni ko na samu daidai to"

"kana da kai kuwa a ina ka taɓa ganin Anyi haka? To ta yaya nunamin in gani na kure haukar ka yau? Nuna min..."

"dallah kai banza ne ni na sani ne? Ina nufin da anayi Rabawa biyu zanyi na taimake shi"

"oh asan banzan Dai tsakanin ni da kai da ka gyara zancen ka yanzu, kasan fa shi inda ya samu matsala tun accident ɗin da sukayi Har ake tunanin waist ɗin sa ya taɓu kk baze ƙara aiki ba ashe da akwai gagarumar matsalar nan da sai daga baya ta bayyana dan baffa ma likitocin asibitin ya ɗora ma, Wai basu bincike shi sosai ba, kuma gaskia a lokacin lafiya lau suka sallame shi sai daga baya ashe abun ya ɗan sami matsala bayyana hakan daga baya yazo, ga yaya mahadi da miskilanci abu na damun shi sai dai ummu ta fahimta fa tamai ɓaro ɓaro sanan Zai Mata ƙarin bayani"

"kai na tausaya mai wlh wai to kai a gidan uban wa har aka zauna ana hirar irin wanan da kai kamar a gaban ka akayi komai, kai baka da kunya fa komai ka sani haka?" Ajmal yana hararar sa'ed yake tambayar shi.

"kai a harkar addini da abin da ya shafi cikin gida da iyali fa babu kunya sai mai buɗe ilimi iyaye Susan ƴa yaran su suke, musulunci fa yazo mana da komai sai dai wasu su tafi dashi yadda suke so, kai mufa ummu tun muna fara girma (balaga) take fahimta, kuma ta zaunar damu ta mana bayani kai har yadda ake wanka a wajen ummu na fara ji kafin Naji a Islamiya, kuma abakin ta muke sanin yadda wasu abubuwa masu mahimmanci da ya kamata mu sani, ire iren su nisanta da matan da bamu da alaƙa dasu da da su indai aka Mana abun da bamu yadda dashi ba muzo gida mu sanar mata ka manta auwalu da malam ɗan Lami ya fara shafa shi kullin in sun je masallaci Yamai na ɗaya Yamai na biyu kawai yazo ya buɗe mai aiki a gaban ummu bata bashi amsar abin da hakan yake nufi ba sai da ta tara mu dan tasan muma muna da buƙatar Ilimin, wlh Sai a lokacin nasan meye luwaɗi da maɗigo ta mana mugun jan kunnen da har yanzu bai bar kunuwan mu da zuƙatan mu ba tun muna yara take nuna mana babu alaƙa tsakanin macce da namiji ko namiji da namiji ko mace da mace a matakin shekarun mu dai, kai wlh matsalar ka da ahanun ummu ka faɗo Ko a matsayin ɗan riƙo da matsalar ka ko ta girmama da zaka sami sauƙin wani abun dan bazata barka haka ba, tunatarwa da shawarwari kaɗai sun isa ka gane wani abu kuma zata tayaka ririta baiwar ka, ƴan case ɗin yaya mahadin nan Kaga yadda ta tashi hankalin ta? Tafi baffa ɗaga hankali fa, kuma da ita ake komai ba zuwa asibiti yanzu har na gargajiya ake mai, yadda ta damu ko yaya mahadin bai damu haka ba, ni kuma case ɗin yada, akayi na sani gaskia gani nayi nima inada buƙatar sanin Ilimin abun dan da babu mu suke yi sai na dinga damun ta har ta ɗan mun bayani yadda bazan gane ba dan Abun bai shafeni ba sai da sisco ya ƙara buɗe min aiki na fahimta na tausaya ma yaya, dan ni Kagani yanzu a yadda nakeji bance banajin Komai game da mace ba, Amman da wanzuwar ta da rashin ta duk ɗaya, dan nasan duk bala'e lokacina baiyi ba, to bani da ma girbi mai ya haɗani da shuka? Nasan in lokacina yayi zanyi ne dan haka nake sake ɗauke kaina daga matan ma, kamar kai" sa'ed ya dasa aya.

Doguwar ajiyar zuciya Ajmal ya sauke kafin ya iya cewa "gaskiya ummu ta daban ce, ni ban Sammi wanan gatan ba, wani abu sai dai Naji daga Abba ummah kuma nasan nauyi na take ji da zan samu wani abu daga gareta sai dai Naji a karatu, gaskia ummu uwace".
[18/12, 11:58 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*

Shafi Na 14

Na maman shaheed (Fatima Abubakar)

"kunyi dacen uwa Kunga da yanzu auwalu ya sami matsala da bata nuna muku itace abokiyar shawarar ku ta farko ba kafin wani, dan ku duk maza ne ma baku da mace dole ta jaku ajiki, ni ai tuni aka tsigeni tun zuwan su twins, wani sauƙin ma daga wajen su nake samu"Ajmal ya faɗa zuciyar sa fal rauni.

"hmm kai kam inda aka samu matsalar kenan, toh kai sai ka bama kanka kariya tunda Abba yana iya ƙoƙarin shi, ummah kuma kunya da kara ce take sa taƙi gaya maka wani abu, Amma dole inda Kaga fuska nan zaka dinga kai kukan ka da neman shawara, da tun farko ka nuna mata uwace da zata shiga sha'anin ka sosai har ta jaka ajiki fiye da yanzu duk da ma dai yanzu ai baka da matsalar komai da ita"

"a Alhamdulillahi inace inada matsala da ita na mata ƙarya dan ita take min abin da momah ma bata min, kuma babu abin da bata sani ba na halitta ta dan abakin Abba ta fara ji da taga tsangwamar tayi yawa da momah take min, kuma tamin nasiha baban abin da yafi kwantar min da hankali koda zata ga su safna a kusa dani muna karatu ko wani abu bata taɓa zargina ko kyara ta ba bare ƙoƙarin rabamu da take ba, ba kamar momah ba "

" toh ka gani yaddace ta yadda da kai ne, kai kuma nasan baka da matsala da yaran ta suma kuma ta nuna musu kai jinin su ne "

" sosai kai dai Allah yasa mu dace, ni yanzu so nake na kammala karatu nan na faɗa harkar kasuwanci da gaske"

"haba mutumina ko Auren ake shirin fuskanta dan samo mafita...."sa'ed ya faɗa yana dariya.

" banza kawai ana ta kai wake ta kaya nawa nake, dallah ni kar ka iskata ni go gefe malam ni Abbah nake son rage ma ɗawainiya kasan run da ya sami karayar arzikin nan sai a hankali gashi har ya haifar mai da hawanjini dan ni fitar da yayi yau ma har yanzu hankalina bai kwanta ba da sai da azahar zan je na same shi Amman yanzu kawai zanzo na shirya na tafi"

"wanka zaka yi kace?"

"eh shi zanyi?"

"wanne wanka daga ciki" sa'ed ya faɗa yana gimtse dariyar shi.

Wani kallo Ajmal Yamai ya mai daƙuwa yace "wankan ubanka mara mutunci Ni zakama iskanci Ko?"

Sa'ed ne ya tallabo kafaɗun shi yana bubugawa yana cewa "sorry mai da wuƙar wasa ne, kasan sai na ɗana zanji daɗi jekayi Kafin nima naje gida na dawo"

"dallah matsa Kawai ai wani lokacin mutumin banza ne kamar sisco rikiɗewa akeyi ka koma ɗan ka'is..."

Daga nan suka fita tare Ajmal ya tafi ɗakin shi yayi wanka, sa'ed kuma ya fice.

"Ku dawo?" ummah ta tambayi su Safiyya.

"eh ummah wlh ummah bakiji ba Kamar mu tafi tare, Amman dan Allah kima Abba magana ko zai haƙura momah ta dawo har kuka mukayi da zamu rabu" Safiyya ta firta, hassana kuwa ma ta rasa bakin magana.

"Tom In sha Allah zan sake mai magana, Abin ai bai ma kowa daɗi ba, yanzu kuje ku ɗibi abinci kuci ku huta ko?"

Sai suka tafi ɗakin su safna, duk jikin su a sanyaye.

Bayan Ajmal ya gama shiryawa ya shigo wajen ummah, yake ce mata ze wuce da ƙyar ya zauna yaci abinci sanan ya wuce su hussy suna mai Allah ya kiyaye hanya.

Lafiya Ajmal ya isa kasuwa, har sun ɗanyi hira da Abba, yana ta hassashen Abba kamar bayajin daɗi Har ya tambaye shi yace mai kawai ɓacin ran mahaifiyar shi ne bai sake shi ba, haka dole ya haƙura ya kawar da kai badan ya gama yadda ba.

Wajajen la'asar suka dawo gida sakamakon jikin abban da ya rasa gane mai, daga baya hawanjinin shi ya tashi dole sukayi asibiti da shi cikin gaggawa, aka bashi gado aka samai ruwa, ashe jinin ne ya hau sai da ƙyar ya sami bacci, hankalin Ajmal yafi na kowa tashi.

Ajmal ne ya kwana a wajen shi sa'ed da abokanen su Ajmal duk sunzo sun duba shi har ƴan school ɗin su, abokanen abbah ma na kasuwa duk sunzo.
Chapter 17 · 0% Book details