Sashe 19
Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari kuwa mummunan labari ya karaɗe ko ina, kafin ummah tazo da asuba ta sanar mai yana kunna radiyon wayar shi dan ta ɓoye radio da yake ji ma ashe ya kunna ta waya aiko labarin ya daki kunnen shi tunda wani irin bugawa da zuciyar shi tayi bai sake sanin inda yake ba dama kwanan momah ne tun da ta tsallake shi ta barshi kafin asuba bata sake bi ta kanshi ba sai bayan asuba da ummah ta shiga su gaisa tayi mummunan gani, hankali tashe ta kira ummah nan gida ya rikice Ajmal na masallaci wajen karatu yaga ana kiran shi duk da wayar na silent da kamar baze ɗauka ba ganin number momah sai gaban shi yayi mummunan faɗuwa yaushe rabon da moma ta kira shi? Yau yaga kiran ta yasan to babu lafiya, fita yayi ya ɗaga, tun da ya fita hankalin su sa'ed har malamin yaƙi kwanciya, shiko Ajmal bema San lokacin da ya isa gida ba.
Da gudu gudu sauri sauri aka nufi asibiti da abbah baya gane wanda yake kan shi, suna isa aka karɓe shi, a gagauce aka fara mai abin da ya dace, haka ya wuni basan waye a kanshi ba har suka kwana a haka ummah duk dauriyar ta sai da ta zubar da hawaye, su hussy d safna Ko tuni kuka ya ɗaura aure da su babu ci babu sha, Ajmal ma sai da ya zubda hawayen, momah Ma ma sai da ta zubar da hawayen musamman da ta tuna maganar su ta ƙarshe, Ina so ki dinga sassauta ma Ajmal Ina miki wasiya da hakan ki dinga mai addu'ar. Sai da sake rushewa da kuka.
Da safiyar washe gari akazo duduba Shi ya ɗan buɗe ido Amman babu magana sai kallo kuma yana ɗan gane mutane da fahimta, bayan mutane sun watse ummah da Ajmal suka matsa kusa da shi suka fara mai magana cikin taushin murya suna nuna mai iya shago kawai aka rushe su Ajmal sun sami nasarar kwashe komai na Shagon har da kuɗin shi masu kimanin naira miliyan babu dubu arɓa'in da suka gani, sai wasu miliyan biyu cif da suka gani a ajiye daban.
Momah da d su hussy mamaki suka dinga yi banda su safna da suka san da hakan.
Wata ajiyar zuciya Abbah yayi sai yaji kamar ana mai bishara da yayi magana, ya samu ya furta "Alhamdulillahi, nagode muku Allah ya saka muku da gidan Aljannah, Ajmal Allah ya maka albarka da ƴan uwanka baki ɗaya, miliyan guda babu dubu arba'in ɗinan tawa ce ita kenan kadara ta sai canjin da nake bi bashi, in unji tsoron Allah sun kawo to in basu kawo ba karku cewa kowa komai, nidai miliyan biyu nan sune iya abin da ake bina bashi na karɓa da niyar ƙara jari na miliyan uku, to Allah ya soni da rahama ban kashe ba ban sai abin da zan siya ba a ɗauka a ba Alhaji sabitu kuɗin shi amin godiya wajen shi yaso ni da arziki Allah bai nufa ba, nidai Inaji kamar ciwon nan bazai barni ba, ku riƙe juna da amana ko bayan babu raina, shamsiyya Allah ya baki ikon gane gaskia bayan wanan bani da matsala dake, ku haɗamin kan yara ku basu Tarbiya ingantaciya in kun min haka kun gama min komai, kuyi haƙuri ban barmu ku komai ba"sosai kowa na wajen yake kuka banda Abbah.
"Alhj ka daina faɗan haka cuta ba mutuwa bace zaka tashi da izinin Allah"
Tunda ya gama furucin nan ya fara ƙoƙarin mai da numfashin shi saka makon doguwar maganar da yayi, duk da yaji zuciyar shi sakayau kamar ya sauke wani nanauyan abu na bashin mutane, likita Ajmal ya tafi ya kira suka zo suka duba shi aka, mai allura jijiya sakamakon kokuwa da yake yi da numfashin shi da ƙyar ya sami bacci.
Ajmal da sa'd ne suka tafi mayar ma da Alhaji sabitu kuɗin dan cika umarnin Abbah, suna wajen shi yana ta jajanta abin da ya faru ya karɓi kuɗin ya cire dubu ɗari biyu yace ayi jinyar shi da shi Ajmal har yaƙi karɓa, Ahj sabitu Yamai faɗa Sai ya karɓa, suna shirin tafiya aka kira Ajmal akace yazo abbah na son ganin shi, atake yaji jikin shi yayi sanyi da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa ganin hakan Alhj sabitu ya fito da mota a garage yace suje ya duba jikin nashi, suna zuwa asibiti suka ga ƴan uwan su na ƙauye har da su kawun momah da yayan Abbah da gwagwansa ta Kaduna sunyi cirko cirko suna ta matsar ƙwalla, shiko kasa motsi yayi ji yayi duniyar ta tsaya mai can sai kokuwa yake da numfashin shi, da ƙyar ya iya samun damar fita daga motar, sa'ed yaba kuɗin da Alhaji ya basu dan bai sa su a aljihu ba dama ji yayi had kuɗin sun Mai nauyi.
Da ƙyar Alhj da sa'ed suka tallabo shi suna bashi haƙuri, koda kawu yazo da wani ƙanin Abbah rungume Shi sukayi suna bashi haƙuri shi dai ya gaza gane a duniya yake ko lahira? Ba kuka ba hawaye.
Da taimaƙon sa'ed suka ƙarasa Har baƙin ɗakin da abbah yake ciki, sai gani sukayi likita ya fito yana basu haƙuri koda ya dafa Ajmal yana mai gaisuwa kasa magana yayi, yana shiga su safna da su hussy suka taso idanun su a kumbure suka zo da gudu suka rungume yayan nasu duk su huɗu, momah na kallon su babu umm babu um um, kuka kawai sukeyi Amman shi bama yajin kukan nasu wani yawo kansa yake masa, da ƙyar ya rumtse idon shi ko zai dawo hayacin shi, wasu zafafan hawaye suka subo mai da kowa sai da ya tausaya mai, kawu yace "kayi haƙuri tunda hawayen sun zuba zaka ji sauƙi, sai haƙuri Alhaji sa'i yayi kwana sun ƙara munyi asarar mutumin kirki mai bin kowa da Alkhairi"
Kalmar da Ajmal yake so yaji kowa ya kasa furta mai kenan sai yanzu ya tabbatar ya rasa mahaifi kenan na har Abada?
Wasu zafafan hawayen ne suka sake zubo mai karo na biyu, jin yaƙi motsi yaƙi buɗe Ido yaƙi Cewa komai su hassy suka jijiga shi suna kiran sunan shi, "yaya? Yaya kayi magana dan Allah" kawai suka ga ya silalale a ƙasa ya tafi luuu kamar babu rai a jikin shi.
Da gudu momah da ummah da su kawu suka yo kanshi, suna taɓa Shi sujaji babu rai ajikin shi ɗakin ya sake kacamewa hussy ma tunda ta ƙwala wani ƙara ta zube a wajen hassy ma ta rufa mata baya duk suka zube, akayi haihuwar guzuma ƴa kwance Uwa kwance.
[20/12, 3:47 pm] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*
Shafi Na 15
Na maman shaheed (Fatima Abubakar)
Kowa da abin da yake saƙawa, Ajmal dama tuni an bashi gado shima bayan doguwar suman da yayi, su Hassana kuma dama indai ɗaya ta kwanta ɗayar ma sai ta rufa mata baya haka suke, sun riga Ajmal ma samun kansu, dan sun dawo hayyacin su tuni, ko suka farfaɗo da sunan yayan nasu suka dawo hayyacin su, sai da suka ganshi a kwance a gado d aka kaisu ɗakin sanan suka ɗan sami nutsuwar basu rasa yayan su ba kamar yadda suka rasa Abbah.
Shima Ajmal bayan ya farfaɗo har an sa mai drip Amman yana dawowa hayyacin shi yace a cire mai zeje wajen Abbah shi ne, aka dinga lalaɓa shi ana nuna mai ya rasu ya yayi haƙuri basu kaɗai ne sukayi rashin Abba ba har da al'ummah da dama dan an rasa mutumin kirki.
Nan Ajmal ya sake tabbatar da ba mafarki yake ba da gaske Abbah ya koma ga mahalicin shi, sosai yaji hankalin shi ya tashi cikin ranshi har ɗan saɓo yayi yana cewa da ma Momah ce ta rasu ba Abba ba tsabar yadda yake samun nutsuwa da fahimta daga wajen Abbah.
Duk yadda aka so a lalaɓa shi yaƙi haƙura dole aka cire mai ruwan da Befi rabi ne ya shiga jikin shi ba dan babu wanda yake son gani sai Abbah dan ya mai addu'a.
Lokacin ƴan uwan Abbah da Aminan Abbah suna can Anyi sallama ana shirin tafiya da gawar Abbah dan ayi mata sutura, momah tayi kuka kamar ranta zai fita, ummah kuwa kamar ita kaɗai akama rasuwa, su hussy kuwa da ƙyar aka janye su daga jikin gawar Abbah.
Sa`eed kuwa na tare da Ajmal yana ta bashi baki shima yaci kukan ƙarfin hali ne kawai yasa ya ke daurewa dan ya ƙarfafi gwiwar abokin nashi, ko da suka ga Ajmal ya shigo da sauri sukayi kanshi ummah ce ta riga momah kamo shi tana tambayar jikin shi da kuma ya akayi ya taso dan sa'edd suka bari a wajen shi, sai momah ta tsaya ta haƙura, sosai ummah ta rarashe shi ta bashi haƙuri ta nuna mai da su dangana su bishi da addu'a kukan baida fa'ida duk da dai kukan yin kan shi yake ba da izinin maiyi yake zubowa ba, Ajmal ya jima kan gawar Abbah yana mai addu'a kafin yayi wata doguwar ajiyar zuciyar da kowa sai da ya tsorata a zaton su kar wani abu ya faru da shi sanan suka ga yayi shiru sai ya fara share hawayen shi, ya fita ya sami su baffa aka gama komai aka tanadi motar da za'a ɗauki Abbah ta asibitin zuwa gida da Alhaji ya sa aka bayar.
Da ƙyar su safna suka bari aka fita da gawar, akasa a mota lokacin idon Ajmal ya bushe Sai wani tuƙuƙi da yake ji a ƙasan zuciyar shi kawai.
Su ummah da momah ma aka sama musu mota da su saffiya da wasu maƙotan su guda biyu mata, suka nufi gida.
Suna isa gida aka wanke Abbah aka salla ce shi ana ta mai addu'a unguwa ta ɗinke da mutane har dangin shi na nesa duk sunzo maza da mata da suka sami zuwa, Ajmal baya doguwar magana, ga abin sadaka da aka kawo aka shiga dashi gidan.
Ummah n sashin ta momah ma na sashin ta, su safna kuwa suna ɗakin Abbah gani suke kamar zai dawo, ana ta Rarashin su, anan suka zauna da baƙin da suka zazo har daga ƙyauye Har da ƙawayen su na makaranta.