← Book details Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 21

Sashe 12

Dabia Ko Halitta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momah ta son Ajmal kamar ranta, Amman tunda ta sami su twins sai taji ashe ƙaryar so take, twins ne masoyan ta duk da tanajin son Ajmal ɗin a karƙashi zuciyar ta sai na su twins ya nemi danne ba Ajmal, hakan be tabbata ba sai wata rana da Allah ya fara gina wata halitta da Allah yake ginama yara maza idan sunkai shekarun yi na fara girma na bambance su daga matakin yarinta zuwa na girma, matakin ne ya fara zuwa ma Ajmal ta hanyoyi daban daban ciki har da mafarki da ƙuraje da suke fito mai sai yanayi da yake tsintar kanshi a ciki na buƙatuwa kaɗan kaɗan abin sosai yake damun shi, tsautsayi yasa shi ya tare momah da maganar duk da ya kasa gaya mata duka Amman da wuri ta gano shi, tamai mummunan fassara duk da tasan dole akwai ranar ko lokaci zuwa shekarun da hakan ze bayyana agare shi, Amman sai taƙi aiki da hankali da ilimi da nutsuwa bare ta fahimtar da shi abin da ze mai amfani, sai ta ɗauki abun wani lamari daban har take ganin kamar fitina ce da ya ƙaƙabama kan shi, sai ta fara shirin nisan tashi da ƴan uwan shi mata saboda wani wawan tunanin ta na daban.

Ana haka ya fara fuskantar canji daga mahaifiyar shi tsoron haka ya hanashi kusantar ummah da zancen dan da tun a lokacin zata fahimtar da shi, tun ba a fahimta sabon salon zama da Ajmal da momah suka samu har aka fara fuskanta, Alhj Ma'aruf da ummah abin baya musu daɗi kuma sun rasa dalilin hakan, sai da Alhaji Ma'aruf ya rutsata take gayamai gatsal.

"Nifa bazan zuba ido ya in barshi cikin yara na mata ba ya haifar min da matsala, ko ka kai shi boding school ko asan abin yi ya dinga nisantan yarana, Yaro ko ina beje ba tun be tafasa ba yana neman ƙonewa? Wanan wacce iriyar fitina ce? Ina ya samo ta?" momah tayi tambaya.

" ke za'a tambaya da kika haife shi, kuma wallahi kin ban mamaki ke da zakija shi ajiki kiji damuwar shi ko ki taya shi maganin matsalar shi ko ɗara shi a hanya, dama kike cewa na kai shi makarantar kwana a hakan kina ganin shine mafita, baki damu da me ze faru ba ama ɗau wawan tunanin Ki, can shi kaɗai ze rayu? To wata makarantar bance duka ba fitinar da take ciki gara ki bar ɗanki a gida duk abin da ze ɗebo yayi a gaban ki, kuma ni ina da kyakyawan zato akan ɗana da irin tarbiyar da na bashi nasan da izinin Allah baze bani kunya ba kuma akan halal ɗin shi ze tsaya mummunan zaton ki ya tsaya iya zuciyar ki, kuma ki Dena hantarar min ɗa"

"oho nidai be dame ni ba kai ai ba haka kake ba, sai shi ne zezo a haka? Fitinar sa a ƙoƙon rai har wani matse matse fa zaka ga..."

"malama Yimin Shiru ke kika gani, lafiya ce inda mara lafiya Allah ya baki sai kin fi kowa ƙorafi ni tsonawa kina min ƙorafi a hakan yarana biyar yanzu wanne ƙorafi ne baki yi ba, ke ba'a iya miki jahilcin banza Ance ki koma makaranta ko radio ki dinga saurara Taurin kai da ra'ayin riƙau ya hanaki Kar ki takurama ɗana"ya furta Yana tafiya ze bar mata ɗakin.

Yana fita yaga Ajmal ya takure a falo gefen kujera duk abin duniya ya ishe shi yama rasa me ke mai daɗi...

"Zo nan Ajmal biyo ni muje" tasowa yayi suka tafi ɗaki ya bishi ya zaunar dashi ya fara mai bayani cikin hikima da yadda ze fahimta ba jin kunya ba ɓoye ɓoye...

"kuma Kaga inaso ka nutsu kasa tsoron Allah a cikin Ranka, riƙo da addinin ka da aiki da Ilimin ka shi ze zamar maka tsani da hanyar billewa, duk abin da kasan addini yayi hani dashi to kar ka aikata duk yadda zuciyar ka ko buƙatuwar ka taso ingizaka kuwa, nasan ka fahimci me nake nufi, har kafin Allah ya nufa matsayin ka ya kai inda ze zamar maka warwarar matsalar ka ko halitta ka da maman ka take ma kallon ƊABI'A ce da ka aro, bana so ka biye mata, Komai addinin mu yazo mana dashi be barmu haka ba, ka riƙo da azumi da ibada duk zaka sami kamewa daga barin abin da Allah baya so, kar kasa wani abu a cikin ranka bare ya dameka, ka kula da karatun ka, babu ruwan ka da shiga cikin abokanen banza da wofi Ko shiga shirgin matan da basu zama muharraman ka ba duk da nasan bazan samu haka daga gare ka ba tuni dai nake ma da haska ma hanya dan Allah karka bani kunya"

A raunane Ajmal ya ɗago ya kalli mahaifin nashi idanu taf da hawaye yace "In sha Allah Abba, kuma bazan baka kunya ba nagode da ka yadda dani har kake kyautatamin zato, azumi kuma zan riƙe shi in sha Allah, in jarabawa ce Allah y aiko min da ita ku tayani addu'ar, Allah y bani ikon cinye ta in kuma wani musibar ce Allah ya tsare ni ya bani kariya daga zuciya ta har gangar jiki na "

" Amin ya Allah, Allah zai dafa ma kuma ze dube ka nafi ganin ƙaddarar ka ce tazo a haka, da sannu kuma zaka cinye ka ɗan dinga nisantar ƴan uwan ka mata tunda haka take so, duk yadda zan mata bayani kana gani taƙi fahimta, baga ɗaya maman ka? Wani ya ƙika da wuni wani ya so ka da kwana ko ta taɓa hantarar ka ko shiga tsakanin ka da ƙanen ka na wajen ta? "

Ajmal ne ya bashi amsa da" A'a Abba shine yasa Abin yake Damuna, har fa tana cewa wai in je can tunda ta sake min inna ɓata mata yara ita babu.... "

" A'uzubillahi bazamu ga haka ba kar ka ƙarasa kuma kar ka sake mai mai tawa, mugun yawun ta ya ƙafe acikin bakin ta ko ta to far dashi, Allah ze kare ka kullin cikin yi muku addu'a nake yi kai da ƴan uwan ka, in wajen mahaifiyar ka yama zafi kayi wajen mmn su safna nasan zaka sami sauƙi acan kaji ko, sai ka tsare kanka kar ka bada ƙofar da zargi ko rashin yadda ze shiga tsakanin ku, kaci gaba da tafiya dasu tamkar ciki ɗaya kuka fito dan uba ɗaya ya fi ƙarfin wasa, Allah ya maka Albarka ya maka maganin abin da yake damun ka"

Da "Amin" ya amsa Abban ya gama rarashin shi har suka tafi sallah tare, yana dawowa ko be je ko ɓangaren momah ba, ya tafi ɓangaren ummah.
[13/12, 7:41 am] Maman shaheed😍🥰: *ƊABI'A KO HALITTA*

Free book

Shafi Na 10

Maman shaheed (Fatima Abubakar)

"Ajmal Kaine, ya Anyi sallah ko?" ummah ta tambaye shi bayan ya shiga ɓangaren ta.

"eh ummah tare muka dawo da Abba ma"

"OK, ya dai? Ko akwai matsala ne? Nagan ka wani irin, ba dai momah bace Ko?" ta tambaya.

"eh babu komai," ya bata amsa a gajarce.

"toh Allah yasa, kadai dinga haƙuri ka ƙara akan wanda kake da shi wata rana sai labari kaji ka kiyaye hakkin Allah da dokokin shi zaka sami rayuwa mai salama mara turnuƙu aciki kaji?"

Y amsa mata da "toh ummah in sha Allah" abin da mahaifiyar shi bata iya mishi kamar shi ya halicci kanshi a haka.

"laa yaya ashe ka shigo banji ko maganar ka ba" Safiyya ce ta fito ta gan shi take tambayar shi.

Jarumta da fara'ar dole ya ƙirƙiro ya bata amsa da "eh yanzu na shigo ai"

"ke magananiya ɗebo mai abinci zaki ci kashi da surutu kamar radio" ummah ta umarce ta.

"kai ummah kin manta ba lallai yaci ba shinkafa ce fa jullof kin san... Yaya ko a zubo ma akwai cabbage Sai na yanka ma ka haɗa da shi ko ze ɗan shiga" safiya ta tambaya.

"au ai na manta, ko a zubo?" ummah t sake mai tambaya.

"a'a ku barshi kawai naga mommah tayi tuwo miyan wake kamar zefi min zanje naci Kawai" ya basu amsa.

"laa to yaya ko na ƙarɓo ma?" ta tambaya.

Ya ɗago ya kalle ta yace "hmm kin manta ko? Jeki za'a tuna miki" sum sum ta nemi waje ta zauna yasa mata dariya, ummah ma dariyar take, tana ce musu "bana son shegan taka kul ɗin ku na gaya muku"

Sosai suka tuna ranar da taje wajen momah ƙarɓo mai alala ze haɗa da kunun ummah aka korota akace baida ƙafa Ne, alalar da beci ba kenan koda yaje karɓa ta hana, sai haƙura yayi, Wai sai da ya gama zaman shi sanan zezo ya ƙarɓa.

Yanzun ma tunawa da kar ya makara tayi mai haramiyar yasa ya tashi ya tafi dan yunwa yake ji, yana zuwa ya samu tana sallah ya tafi kitchen ɗin da kansa ya sami Hassan da husaina aciki suna zubawa a cooler, Yace su Zuba mai, suka zuba mai da yawa ya karɓi kwanon zai rage, hussana na gaba tukunyar miyar, ya kama kafaɗun ta kenan dan ya matsar da ita, ashe momah ta sallame sallah Wai har ta jisu shiru tabar yaran ta da ƙato a kitchen Kamar ba ita ta haife shi ba, tana shigowa ta hango kafaɗun hassana a hannun shi, Tako kurma ihun da duk sai da suka firgita a razane suka juyo, itako idon ta ma kizo ya mata da shaiɗan da yake sake bata taimako da reremata waƙar zargi, gani tayi kamar hanun shi a kirjin hassana, dan haka ta saki ihun.

"momah lafiya?" husaina ta tambaya.

"maye ke faruwa haka? Me kake yi kenan Ajmal? Ko ba tambayar ka nake ba?"

"momah mai ko nake yi? Tuwo zasu zuba min, sun zuba yayi yawa nazo rage wa, gasu tambaye su" ya firta yana lumshe ido yana jin dama bezo ba ya kwana da yunwa dan besan me zece ba, mahaifiyar shi na son yimai sharri? Hakan baze iya fitowa daga bakin shi ba, sai tsinkayo muryar ta yayi tana tambayar su hassana.
Chapter 12 · 0% Book details