Sashe 8
Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shine Wanda nakeso ni
Cikin tsawa wadda ita kanta Samia saida tayi mamaki saboda tasan yanda yakeson Amal
Yace karna sake Jin wannan maganar daga bakinki, nide nasan ban baki damar kula kowa ba, kuma ko waye wannan Yaron ki fada masa zanzo in sameshi
Tunda shine yake hure miki kunne
Nariga nagama magana, yaro de nabashi, Rana kuma ansa, kiyi abinda zaki iya, tashi kibani waje marar kunya kawai
Da gudu tayi daki tana kuka, nashiga uku na
Ni wallahi banasan kowa, arasa wanne irin aure za'a min saina dole, ni wallahi banasan sa, yawani zo yaqame awaje daya saikace gunki
Wallahi Bana sansa, hijabin ta take nema zata tafi gidansu maisah
Acan wajan su umma kuwa, Malam ne ya kalli umma yace Samia kinji wata sabuwa kuma ko?
Samia da Allah zai hadani da wannan Yaron datake magana akansa toda haduwarmu bazatai kyau ba Samia
Toni Wai yaushe ma Amal din har tasan kanta dazata fara kula wani bamu saniba
Amma may be yayanta ai shi yasani, tunda tare suke abinsu
Wayarsa yadauko daga aljihun sa, Babu Bata lokaci yadannawa Shahid kira
Bayan sun gaisa baba hamani yace dama inaso zan tambayeki ne, Shahid yace to baba inaji, Wai kasan yarinyar nan tana sauraran wani sham?
Shahid yace wacce yarinya?
Domin kuwa shide yasan cewa Amal bai Santa da kowa ba
Baba yace wakuwa nake nufi banda Amal
Yace gaskya baba bansanshiba, itace tafadama hakan da Bakinta?
Yace qwarai kuwa yanzu nan muka zaunar da ita nace ga yaro nan nayi Mata miji harma mun tsaida ranar auren nanda sati biyu shine takemin wani zancen banza
Gabansa ne yafadi Wai wacce Amal din?
Me baba yake nufi?
Shahid yace baba Wai Amal Amal de?
Baba yace ita mana to menene?
Kansa yadafe da hannun sa daya dayake barazanar rabewa gida biyu, idanunsa suka kada sukai jajir
Yace Amma baba Ina Santa
Wallahi Ina kaunar Amal baba
Kai Shahid me kake fada haka?
Wacce irin magana ce wannan?
Baba wallahi nabari ne in dawo in sanar daku komai Amma baba Ina kaunar Amal tun batada wayo baba
Baba Dan Allah Kar ayi auren nan
Baba hamani kashe waya yayi batare dayace komai ba, ya rafka uban tagumi
Umma tace meyafaru Malam
Baba yace Samia mun shiga uku
Karaf akunnan Amal datake kuka zata tafi gidansu rumaisa, innalillahi meyafaru baba yake maganar shiga uku?
Kasa kunne tayi domin tajiyo karshan maganar
Baba yaci gaba da cewa ashe Yaron nan yadade yana San yarinyar nan Amma yaqi fada mana, Wai jira yake saiya dawo daga makaranta yasanar damu
Umma tace Wai Shahid?
Aini Malam nadade da gane take taken sa, kawai de shiru nayi Inga ko shaquwarsu Tasa hakan
Nashiga uku Samia, idan nahana Shahid auren Amal banyiwa IBRAHIMA adalci ba
Ibrahima ahannu na yadanqamin amanar Shahid Samia
Wannan wacce irin masifa ce ne?
Jiri ne yadebi Amal, batasan ya akai ba Sai ganinta tayi aqasa jagwab ta zauna
Yaya Shahid
Tayaya?
Tayaya za'ai ace akwai aure atsakanin su
Yaya Shahid fa
Inaaaa bazai iyuba, Dasauri ta tashi tun kafin iyayen su ganta tayi waje, Bata zarce ko Inaba Sai gidansu maisah
*** *** ***
Da hannu biyu yadafe kansa dayake masa mugun ciwo, innalillahi wa inna ilaihir raju'un
Why Amal?
taku yaji akansa, yana dago Kai yayi tozali da ita, dama ita yake jira, saboda sunyi waya tace tanaso su hadu dashi awajan domin yaganta
Kamar kullum de Riga da wando ne ajikinta
Tayi bala'in kyau
Ido ta zuba masa takasa janye idanunta akansa, meyasa me shi idonshi yayi jajir haka?
Zama tayi akusa dashi
Shide yakafeta da ido, yana kallan ta, ransa amutuqar bace, da bayanin da baba hamani yayi masa
Zama tayi dab dashi
Tace barka da hutawa
Ataqaice yace yawwa barka
Dafatan ka ganeni nice mukai waya jiya
Dan Allah inaso kafadamin sunan ka
Still agajarce yace Mata "shahid"
Fara'ah ce ta wanzu afuskar ta, ashe ma sunansu daya
Cikin murmushi tace ashe ma sunanmu daya
Ni sunana shahida
Dafatan ka amince da soyaiya ta
Wallahi tun ranar farko dana fara ganinka naji ka kwanta min
Wallahi Shahid idan bansameka ba ko zan iya....
Dakata Dan Allah baiwar Allah
Kawai shikkenan daga ganina kin zauna Sai zubamin surutu kike
Dan Allah ki kalleki
Da ido tabi jikinta da kallo tanaso tagano aibun daya gani agareta
Kinga ni banda ra'ayin aure mace haka, ban tsane Kiba, kawai Bana ra'ayin ki ne, bakiminba
Hannayensa yahada waje biyu
Yace Dan Allah naroqeki kifita daga rayuwa ta
Yana gama fadar haka, yajuya yabarta awajan, me shahida zatai banda kuka
Wallahi idan Bata sameshi ba mutuwa zatai
*** *** ***
Maisah nashiga uku na, auren dole baba zaimin
Bangane ba, mekike nufi ne Amal?
Cikin kuka tace wallahi da gaske nake maisah, nanda sati biyu za'a daura min aure
To dawa?
Waida wani, nifa sau daya nataba ganinsa, kawai shine baba ya karbi kayan saka ranar su
Ashe Yaya Shahid sona yake maisah
Ashe ba cikinmu daya ba
Ta qarasa maganar cikin kuka
Yaya Shahid de Amal, Yaya akai kika sani?
Wallahi da kunne na naji su baba suna maganar
Kuma ni wallahi babu Wanda nakeso inba Yaya sham ba
Amma Kuma Da'a auramin wannan mutumin gara sau dubu in auri Yaya Shahid dina
Ajiyar zuciya maisah tasaki, tace Amal, shiyasafa kwanaki nake tambayrki cewa Anya kuwa Yaya Shahid iyayen ku daya?
Kikacemin eh
Amal abinda zan fada Miki shine kiyiwa iyayenki biyaiya, bakida kamarsu aduniyar nan
Amal baba yayi miki komai, ke kanki kinsan cewa yana sanki, bayasan bacin ranki, meyasa ba zakiyi masa biyaiya ba?
Amal baba bazai ba dake inda za'a cutar dakeba, kiyi hakuri
Rungume rumaisa tayi tana ci gaba da kuka, maisah tana bubbuga bayanta alamar rarrashi
*** *** ***
Da daddare tasha maganin ciwon Kai, ta kwanta, idonta biyu, tayi shiru tana tunanin rayuwar ta yanda take neman juyewa
Umma ce tashigo ta miqo mata waya, tace gashi zakiyi magana da yayanki
Tana Bata wayar tajuya ta fita
Da sallama ta daga wayar, Yayanah
Kawai saita da kuka, Shahid da zuciyarsa ta kusa karyewa yace menene kuma abin kuka?
Ko Dan baki samu sham dinki ba?
Nifa Yaya bahak.....
A a Amal, bakiji magana ta ba, inda kinji bazakimin hakaba, cikin kuka tace Dan Allah yayanah kayafemin
Kamar wasa taji, alamar yana kuka
Dasauri tace Yaya kuka kake?
Cikin shashshekar kuka yace Amal Yaya zanyi da soyaiyarki?
Innalillahi karde zancan su umma da gasken ne
Cikin kuka nace nashiga uku yaya
Yace Amal, Babu yanda zanyi, dole in hakura dake
Tunda baba yariga yayanke hukunci
baba yayimin komai Amal, BURINAH inso abinda yake so Koda kuwa ba shine ra'ayina ba
Yaya kayafemin kula Yaya sham danayi
Insha Allah bazan sakeba Yaya nayi laifi
Amma Yaya wallahi banasan wannan mutumin
Banasan sa Yaya
Please Yaya kadawo baba yayi mana aure
Hawayen idonsa yagoge yace bazai iyuba Amal, bazai iyuba, karmu maida mahaifinmu mutumin banza
Wayar sa yakashe yana goge hawaye
Kamar wasa okasha yaji kuka, yana juyawa yaga Shahid yana goge hawaye
Subhanallah, Shahid meyake faruwa?
Kamar jira yake a tambayeshi nan yaci gaba da kuka haiqan, yana cewa shikkenan narasata okasha
Okasha narasa Amal, yarinyar nan da soyaiyarta na rayu acikin zuciya ta
Jikin okasha yayi sanyi,ya janyo shi jikinsa yana rarrashinsa
*** *** ***
Ungo wannan karbi Kisha, umma menene wannan din?
Bansaniba yarme tsinannan surutu
Bata qara maganaba takarbi maganin ta shanye
Umma zanje gidansu rumaisa, bazaki ba, kije nan gidan hauwa'u tana neman ki
Babu yanda ta iya haka zura hijabin ta tatafi, tunda bikin nan ya matso ake dirka mata wannan magungunan, tarasa na menene
Ko duk Dan wannan gunkin sukeyi oho
Tana zuwa gidan anty hauwan ma, magani tahada mata tasha, wani kuma tabata su aleda Wai tanasha kullum idan ankaita bauchin
Koba bauchi ba
Zasuga bauchi
*** *** ***
Alhaji kaide kadage Akan auren nan, wallahi kuwa hajia, aure kamar anyi angama insha Allah
Yatsina fuska tayi, tayi shiru batare data qara cewa komai ba
Ina agogon nan nawa?
Wai agogon daka siyo a Qatar kaida president?
Eh shi bani shi,
Tana kawo masa yasaka, yagyara Zaman babbar rigar sa, ya kalleta yace Toni ke kin zauna ko yau bazan samu afesa min turaren ba?
Batace komai ba ta tashi tana cika tana batsewa, tafesa masa, yace yauwa kokefa
Angama saka akwatunan acikin motar?
Eh angama alhaji
Tosh mu muntafi saimun dawo, shi daddy yacemin yana jiran
Jabir, jirgin su zai sauka nanda 20 minutes
So zasu biyo mu daga baya
To alhaji Allah yakaiku lafiya, Allah yatsare Amin hajia
Yana fita suka shiga motoci shida tawagar yan daurin aure, basu zarce ko Inaba Sai jigawa state
*** *** ***
Jb, Babu inda zani, Akan wannan qanqanuwar yarinyar zanje indebowa kaina gajia, wallahi bazaniba
Jirgin ku yasauka da niyya nace masa Kai nake jira
Haba daddy, Abba nefa, meyasa zakai masa qarya?
To Jb ya zanyi?
Wai kasan yarinyar dayake shirin aura min ne?
Yaushe ma Salman ta rasu?
Yarinyar fa batafi shahida ba, haba me zan tsinta ajikin ta?
Daria Jb yasaka
Yace a a fa daddy karka zo kana qaramar murya daga baya
Kai yarinyar fa nakasashiya ce, wallahi batada lafiya, liqamin ita ake so ayi
Kafin Jabir yayi magana wayar daddy tadau qara
Gabansa ne yafadi dayaga sunan Abba baro baro ajikin screen din wayar
Ahankali ya amsa, acan kuwa Abba yanata Fama da jama'ah Ana jiran ango yazo a daura aure tunda yace zasuzo daga baya
Abba yace Ina kuka tsaya ne, har yanzu shiru babu ku
Sumar kansa yashafa yace Abba Mota ce ta lalace mana ahanya
A a Mota ta lalace muku bazaku tsaida wata ku taho ba, yanzu Yaya kukeso ayi?