← Book details Burinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 39

Sashe 32

Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To duk Dan da aka cika so baqin jini yake
Gaba dayansu sukasa daria
Shahida tace umma karfa yazo ki ganshi gaba daya ki rikice, kice saishi
Umma tace a a ku riqe abinku banayi
Shahid yace ai umma ba wannan maganar ce kadai zata kaimu ba, har maganar aikin nan da Abba yayimin
Tace Toshiknn, gaskya Kam gara kuje din, Allah ya kiyaye, idan babanku yadawo saina fada masa, inyaso kaima saika kirashi awaya
Yace to umma
Ta kalli shahida tace yata ki kula da kanki sosai kinji?

Shahid yayi saurin cewa umma nikuma banda ni?

Umma tace Dan Allah ku tafi Shahid
Haka suka futo harabar gidan, da kansa yabude mata gaban motar tashiga sannan yazagaya yajasu suka dau hanya
*** *** ***
Yaya daddy Dan Allah kafita daga Dakin nan, su Momy fa suna falo, karsuyi tunanin wani Abu muke
Qugunta yakama yana daga Bayanta, ya rungume ta, ya dora kansa awuyanta yace shikkenan ma kinga nahuta idan suka fahinci wani abun din, basu ne suka San yara ba
Tace to ai ansamu, Dan Allah katashi ka shirya kashiga office, Nima indomie nakesan dafawa, ita nake sha'awa
Yace no karkiyi da kanki, zan fadawa momy Sai Tasa ayi Miki
Tace Yaya daddy banajin dad
in na masu aikin, inaso ne inyi da kaina
Yace Toshiknn
Wayarsa ce tayi ringing, yana dubawa yaga Abba ne me Kiran
Yadaga wayar yace yau ka manta da fita office ne?

Babu kunya daddy yace ah...

Abba dama yau bazan fita ba
Abba yace ok to shikkenan
Amal ta kalleshi tace meyasa zakace bazaka ba, idan Kuma wani Abu yataso fa?

Yace nariga nasanar dasu yau bazan shiga ba, yarinyata tace in zauna inbata kulawa
Cikin mamaki tace wacce yarinyar kenan?

Cikinta yashafa, yace gata acikin nan
Murmushi tasaki tace to Bari inje inyi girki na
Kallanta yayi, cikin shagwaba yace please baby, kawai gaisawa zamuyi da babynah, tace Amma Kuma Yaya daddy su umma fa....

Shima kan gadon ya nuna mata yace please ko Yaya ne
Yakamata Hannunta suka yi gadon, daga nan suka Lula duniyar ma'aurata, inda Amal taji dadin abin sosai, shikuwa gogan baisan Ina kansa yakeba, Jin tasake wani irin dadi
Saida komai yalafa,tace my dear yunwa nakeji, kuma kahanani yin girki da wannan gaisuwar
Yace sorry baby na wallahi ke dince, ta daban ce, bari inje in dafa miki da kaina, aide indomie ce ko?

Tokinsamu yanzu
Yatashi yayi toilet domin wanka, Amal ta bishi da kallo Itade tasan cewa bai iya komai ba, Amma tayaya zai iya dafa wata indomie, Amma bari tazuba masa ido
Yana futowa daga wanka, yashirya yace tashi Nakai ki toilet din, kiyi wanka, kafin ki futo indomie tana jiranki
Sarai zata iyayin komai da kanta Amma saboda ya dauke tan ta miqa masa
Hannayenta, yadauke ta yakaita toilet din, sannan yafice
Yana zuwa falo Sai momy ita kadai, tana kallan labarai
Taga yayi kitchen da kansa, ta daga murya tace wani Abu kake buqata ne?

Keyarsa ya Sosa yace a a momy Amal ce takesan indomie, shine nace bari inyi mata
Momy aranta tace ikon Allah sabon Salo, to Bari muga wannan girkin yanda zai qare
Afili tace Toshiknn, Allah yabada sa'ah
Aikuwa babu kunya yajuya yashige kitchen din
Yana zuwa yadauki tukunya, ya wanke ya dora sannan yadebo ruwa yazuba saura kadan ruwan yakai Rabin tukunyar
Yadauko noodle din guda daya babba yabude yasaka acikin ruwan, magin daya gani aciki yabudesu duka biyun yazuba, yadebo salt yazuba, sai mai
Yana rufewa kuwa tafara tafasa, ya tsaya harta dahu, yadauko flet yajuye aciki, duk ruwa yacika indomie din, gata tayi fari fat
Yadauko yafuto falon, alokacin Amal harta futo falon itama, har Gabanta yakai mata abincin yace sauko kici gashinan
Ta kalleshi ta kalli indomie din, tace to
Momy dake gefe tana kallansu
Amal aka saka hannu zuciya daya, takai indomie Bakinta, cikin sauri ta furzar, tace Yaya daddy gishiri
Wacce irin indomie ce wannan?

Ta dauke flet din tayi kitchen dashi, Shima tashi yayi yana Sosa kansa zai bita kitchen din, yakai kallansa ga momy yaga dariyar ta take ita dakai
Yana shiga kitchen din yaga ta ajiye indomie din ta dora wata, ya kalleta yanuna mata wadda ya dafa din, yace wannan din bayarwa zakiyi?

Kallan mamaki tayi masa tace, ai babu Wanda zai iyacin wannan indomie din, duk wanda yaci kuwa to mutuwa zaiyi, gishirin dayake cikinta, shine zai kasheshi
Kansa ya kawar, yayi shiru
Yana gani tadafa wata, sannan taja kujera a kitchen din tafara ci, Shima dayaga haka, saiya dauki Tasa yasa spoon aciki yadiba yakai bakinsa, ai tuni ya furzar yana yamutsa fuska, ruwa yanema yasha
Sannan yaje wajanta yasa hannu sukaci tare
Sunkusa gamawa sukajiyo karadin shahida, aikuwa dukansu sukayo falon
Shahida na ganin Amal taje da gudu ta rungume ta, daddy yace ke kalau kike kuwa?

Kiyi mata ahankali mana
Saida yafada ne sannan yajuya yaga momy da Shahid suna kallansa
Saiyayi fuska kamar ba shine yayi maganar ba yanemi waje ya zauna
Momy ce dakanta taje Tasa aka shirya musu lafiyaiyan abinci, sunaci shahida tanata tsokanar Amal
Bayan sun gama ne momy takira Abba awaya, yana zuwa suka sake gaisawa sannan yabawa Shahid opper sa, sosai yasake murna da godia
Abba yace ai babu wata matsala ko? kunada kudi cikin account?

Shahid yace eh Abba akwai 7 millions
Murmushi su na manya yayi yace ai bakwa kashe kudin ma Shahid, kuyi abinda ranku yakeso fa, zuwa gobe ma insha Allah zansa aturo muku wani kudin
Dagashi har shahida ne wannan Karon sukai masa godia, sannan Shahid yace ai mungama magana da baba ma, yace nadauketa mudawo nan din saboda aiki, saimu dinga tafiya can muyi weekend
Abba yasake murmushi yace Toshiknn Allah yabada sa'ah
Dukansu sukace amin
Saida suka wuni agarin sannan sukai haramar tafiya jigawa, inda zasuyi shirye shiryensu sudawo
*** *** ***
After 2 week's
Suna zaune afalo dukansu, daddy Sai zungurin Amal yake, yana kyafta mata ido, yana nufin ta tashi su tafi daki
Ita kuma taqi tashi, yana sake zungurin ta saita juya masa idonta, tana nuna masa su Abba
Alama yayi Mata da kansa ta tashi su tafi, haka ta sunkuyar da kanta, tadena kallan sa
Basusan Abba da momy duk suna ganin su ba
Wayar daddy ce tayi qara, yana amsawa daga daya bangaren akace yallabai yau ne zakuyi wannan meeting
Kansa yashafa yace meeting?

Kaga a daga shi zuwa next week
Yakashe wayar
Abba yace ba meeting zakayi da wasu ba?

Kansa ya Sosa yace yace Abba dama Yan majalissar jiha ne zamuyi meeting dasu
Abba yace to ai babu dadi karya alqawari, yakamata katashi katafi
Babu yanda ya iya haka yatashi jiki ba qwari yashirya yafita
Amal na rakashi itama tayi Dakinta
Momy tayi Ajiyar zuciya tace alhaji Yaron nan bayasan fita office yanzu, narasa dalili
Abba yace to tsakaninsa ne da iyalinsa
Momy tace to ai idan yafita itama yarinyar kanta zata Dan huta
Murmushi Abba yayi yace Toya za'ai, aide batada damuwar komai ko?

Momy tace babu komai alhaji
Washe gari da daddare suna gama cin abinci suka yiwa su Momy saida safe zasu tafi Abba yace kudawo dama inasan magana daku
Dawowa sukai suka zauna Abba yace nasa ashirya min ma aikata tareda doctor's guda biyu mata, Amal zata tafi Malaysia domin renon cikinta
Saboda nan din inaga hayaniyar mutane zata dameta
So angama komai zaku iya tafiya gobe ko jibi idan ka sanar a office, idan ka rakasu saika dawo bakin aikinka
Comments
Comments
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Gaban daddy ne yayanke yafadi, wacce irin tafiya kuma yana Zaman zamansa da matarsa?

Amal ma jikinta yayi sanyi dajin furucin Abba, to Amma Yaya zatayi dole zata hakura da mijinta tabi umarninsa tunda kamar mahaifi yake awajanta, dole akwai abinda ya hango shiyasa yafadi hakan
Dan haka ta yunqura zata tashi taji caraf daddy yariqe Hannunta
Hannun nasa tabi da kallo sannan ta zauna
Daddy yace Abba mungode da hukuncin daka yanke akanmu, Amma Abba banqi takaba, saide Ina neman alfarma daya awajanka, wallahi Abba zan Bata ko wacce irin kulawa, insha Allah Babu abinda zai faru, Abba nayima alqawari, nide kar'arabamu
Abba ya kalli momy tareda ajiyar zuciya, Lalle zamani yazo qarshe, rashin Kunya qiri qiri
Sannan yace to ai babana Nima ba komai ne yasa nace hakanba, Naga ita yarinyar zata samu hutu babu hayaniyar jama'ah, sannan Kai kanka zakafi tsaida hankalinka waje daya game da aikinka
Momy tace hakane Kam, kaga daddy bakasan fita office tun daga yanzu ma da Amal ta samu ciki
To kuma idan ta haihu inajin tattaro komai naka zakayi ka zauna agida, karfa ka manta haqqin mutane ne akanka kakula dasu, nasan cewa Amal itama haqqinta na kanka but su jama'ar Gari alqawari kadauka zaka kula dasu kabawa kowa haqqinsa
Shekaran jiya ba kaje office ba, kuma babu wani dalili me karfi, sannan jiya meeting kansa zakuyi Amma Babu kunya kace a daga daddy
Haba babana, Allah fa dole zaiyima tambaya Akan hakan
Shiru su daddy sukayi, maganar momy gaskya ne, Amma tayaya suke tunanin zai iya rayuwa batare da Amal ba?

Matarda bikin qawarta za'ai makusanciya Amma yahanata Koda kwana daya ne, sai a ranar sukaje suka dawo, tayaya zasuyi wannan tunanin?

Abba ne ya katse musu tunanin da fadin to kunji wasu daga cikin dalilan dazaisa tatafi
Daddy yace hakane Abba, insha Allah zan kiyaye, wallahi kullum zan dinga fita inde Akan office ne, ni wallahi kafin ku tashi daga bacci na nafita
Gaba dayansu babu Wanda bai murmusa ba Akan maganar daddy
Abba yace to ai shikkenan, ku tashi ku tafi, Allah yayi muku albarka
Suka amsa da amin
Amal tayi hanyar Dakinta, Shima daddy yabi Bayanta, tunawa yayi da iyayensa suna wajan a zaune, Dan haka cikin Sosa qeya yadawo Shima yanufi hanyar dakinsa
*** *** ***
Washe gari da safe suna breakfast gwanin sha'awa su hudu, momy ce dakanta ta zubawa kowa, saboda batasan Amal tayi aikin komai, kowa yanacin abinci ahankali cikin nutsuwa Amma Amal hannu baka hannu qwarya takeci
Tas ta cinye nata, tadau flet tasake zuba wani
Daddy yazuba mata ido yana mata kallan mamaki, wanna wanne irin cin abinci ne?
Chapter 32 · 0% Book details