← Book details Burinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 39

Sashe 25

Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata qarasaba yayi saurin hade bakinsu waje daya, yanayi mata wani irin mahaukacin kiss
(idan akwai me qorafi zai iya fadamin, Kar amanta da Sharhi please inajin dadin hakan)
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Tsawon minti biyar suka dauka atsaye, yaqi sakin Bakinta, ruwa duk ya yagama jiqasu
Daqyar Amal ta tureshi Gabanta yana faduwa, wani irin yanayi takeji atare da ita wanda Bata saba Jin kamarsa ba
Kallanta yake sosai kamar yau yataba ganinta
Ahankali yace "sanyi nakeji"
Kallansa tayi, saiya Bata tausayi, daure wa tayi tayi gaba tabarshi anan,tanaso tadan ja masa aji, shikuma dayaga tayi gaba saiya biyo Bayanta
Tana dauke qafarsa yake maida Tasa
Har sukaje cikin falon, umma ce taganta tashigo da mutum Dasauri ta tashi tace a'a kice baqo mukayi, karaam Kaine atafe da wannan Daren?

Yana Dan karkarwar sanyi yace wallahi nine umma, Amma kansa aqasa yakasa hada ido ta ita, tace sannu da zuwa shigo mana, qaraso muje wajan Malam suna ciki shida Shahid
Bayanta yabi suka shige, Amal kuwa da sauri tayi cikin Dakinta, tafada kan katifar ta, tana maida numfashi, me Yaya daddy yake nufi da wannan abin dayamin?

Idanunta take juyawa alamar tunani, ahankali takai Hannunta kan Dan qaramin lips dinta tana shafawa
Acan kuwa baba mamaki yayi ta yi dayaga daddy Bayan sun gaisa ne, yace karaamullah ashe kana hanya, Muda muke ta shiri gobe zamu taho muyi muku godia, ai angama gida, sosai yayi kyau muna godia sosai wallahi, daddy da kansa yake sunkuye yace a a babu komai
"dama tace tanasan ganinku ne shine nace tazo Sai nazo mu tafi, saimu tafi gaba daya goben insha Allah "
Abba yace to Babu damuwa Allah yakaimu, Shahid kuje yaci abinci saika hadashi da Amal yaje yahuta
Shahid yace to baba, yatashi suka koma falo,suna zama Shahid yace inasu shahida?

Maganar tabawa dadd
y mamaki, shi kansa Shahid din yarasa dalilin dayasa yayi tambayar
Murmushi daddy yayi yace "suna lafiya" umma ce takawo musu abinci kadan daddy yaci yace yaqoshi, Shahid ya qwalawa Amal kira, tana futowa yace ki rakashi daki yayi wanka ya kwanta, akwai kaya aciki saiki nuna masa, ni zanje wajan baba, ahankali tace to Yaya
Dubansa tayi tace zo muje
Tashi yayi yabi Bayanta suna Zuwa, yabi Dakin da kallo, shi be taba kwana a'irin wannan Dakin ba, Amma saboda ita yau zai fara, Amma Kuma babu laifi Dakin yayi, Babu tarkace
Ruwan wanka tahada masa a toilet, zai shiga ne yadubeta yace inajin zazzabi ko zan samu magani?

Batace komai ba tafice daga Dakin, Kallanta yayi, yaga alama de har yanzu Ana fishi dashi
Toilet yashiga yafara wanka
Taje wajan umma tace umma Wai zazzabi yake ko akwai magani?

Umma tace dama yanda ruwa yadakeshi Kam ai dole
Jeki dauko adaki, kibashi yasha, Amma duk da haka kitafi da ruwa mai sanyi ki temaka masa ya goge jikinsa, zai rage zafin zazzabin
Tace to, tana dauko maganin, tatafi Dakin tana tunanin maganar umma, in temaka masa it means fa nice zanyi masa hakan ko
Itade jiki asanyaye Takoma Dakin, dauke da ruwa da magani, tana shiga yafuto daga wanka daure da towel din Shahid ajikinsa
Batare data kalleshi ba tace ga maganin nan Ina zuwa, tafice
Dawowa tayi dauke ruwa awata yar qaramar baho Sai qaramin towel ta ajiye agefensa
Kallan maganin data kawo tayi, ta ganshi dam ko tabawa be yiba
Kallansa tayi tace meyasa bakasha maganin ba?

Idanunsa akanta yace ai baki bani ba
Kai ita tarasa meyasa yake mata wannan abubuwan
Maganin ta ballo guda daya tabashi ahannunsa, ta miqa masa ruwan ya karba yasha
Yadubi ruwan Gabanta yace"mezakiyi da wannan ruwan?

"
Kame Kame tafara, tace am..

Um..

Dama fa umma ce tace waika goge jikinka dashi zaka denajin zazzabin
Kallanta yake yanda duk ta rikice, yace ai bazan iyaba, saide in zaki temakamin, kaina ciwo yake kuma zazzabi nakeji, ga sanyi danakeji, har mura duk damuna take
Kallan mamaki tamasa menene abin jero wannan jinyoyi?

Ahankali ta matsa kusa dashi, kusan tayi kusa har tanajin hucin numfashinsa, tsoma towel din tayi acikin ruwan ta matse, sannan tafara goge masa jikinsa
Kallanta yake yakasa dauke idonsa akanta, ahankali yakai hannun sa kanta yacire Dan mayafin data rufe kanta dashi
Yana cirewa kuwa gashin Kanata ya sakko har Saman Fuskarta
Yasa hannu ya maida mata gashin baya
Yaci gaba da aikin Kallanta, jiki asanyaye taci gaba da goge masa Jikin, tagama goge masa ko'Ina sannan tafara goge masa Kirjinsa da duk gashi ya kwanta
Abinda ya lura dashi shine tafi goge wajan, to Kode tana so ne?

Yanata tunani harta gama ta dauke mayafin ta, da ruwan zata fice yayi sauri yariqo Hannunta
Yana riqe da hannun nata yatashi tsaye yamatso dab da ita, yakama Fuskarta da hannayensa biyu bakinsa dab da nata yace "meyasa kika tafi kika barni?"
Gabanta ne yake aikin faduwa takasa wani Motsin kirki
Idonta ne yaciko da qwallah, Bata iya dakatar da zubowarsu ba, cikin kuka tace fada kakemin
Tasa hannu zata goge hawayen,yayi saurin kawar da Hannunta yace "no yakai bakinsa kan kumatunta ya lashe hawayen tas"
Yana riqe da itan yace, "BABY please karki sake tafiya ki barni, kin Riga da kin zama wani bangare na jikina
Yakai bakinsa saitin kunnanta cikin rada ya furta I love you
Ai Amal najin haka batasan lokacin data qwace tayi Dakinta ba, tana zuwa ta rufe kofar harda kullewa
Tafara Tsallen murna, kan gadon tafada Sai birgima take tana murna
Nan take tadau waya ta kira maisah, anan take cewa gobe tazo gida da safe zasuyi magana
Maisah da batasan da zuwan Amal dinba tace lafiya kuwa?

Amal tace kede kawai kizo, dahaka sukai sallama
Shikuwa daddy da murmushi yabita da kallo, sai shine ya kawar da bahon, sannan yabude jakar Shahid yaduba wata jallabiya yakasa
Sai adakin baba Shahid yakwana, yayinda masoyan biyu suka Kasa rintsa wa kowa yana tunanin dan'uwansa
*** *** ***
Washe gari Yaya Shahid ne yayi musu komai, yayi wanka, suka shirya, har daki umma takai musu abinci, suna gamaci Shahid yake danyi masa fira haka jefi jefi duk da bawani sabawa sukai ba
Amal kuwa bacci tasha me dadin gaske, saida Gari yayi haska sosai sannan ta tashi tayi wanka, ta kira maisah, sannan tafice wajan umma taci abinci, umma tana hankalce da ita Bata nemi abincin dazata kaiwa mijinta ba, kenan da ba'a Kai musu haka zaiyi ta zama, Kai wannan Yaro yana hakuri
Maisah ce tashigo gidan tana ganin Amal suka rungume juna, Bayan sun gaisa da umma sukai ciki, Amal tabata labarin abinda yakawo ta gida, maisah taita mamaki tace yanzu Wai Dan Allah yana gidan nan?

Amal tace wallahi yana ciki maisah ai ingaya miki dayaji bala'i dakansa yafada
Maisah tace meya fada qawata?

Tace yana ciki
Aikuwa suka sa daria, maisah tace kice shikkenan de yanzu an wuce wajan, ke wallahi garama da kika taho
Daria nasa nace eh wallahi
Wayarta ce tadau, qara tana dubawa taga shamsu ne, cikin haushi tace nikam nashiga uku nah, Amal tunda mutumin nan yarasaki shikkenan yadawo kaina, yakade min hankali wallahi
Amal tace wakenan?

Maisah tace Yaya sham mana
Amal tace alhamdullahi, wallahi wannan Abu yayi, maisah ki aure shi Dan Allah
Kallan mamaki tabi Amal dashi tace Amal kanki daya kuwa, tsohon saurayin kinefa, a a bazan iyaba, Amal tace to menene?

Tsohon mijinane?

Kokuma a kanmu aka fara?

Kinga ni yanzu Yaya daddy nakeso, Babu sham acikin zuciyata
Kiyi tunani maisah, BURINAH Inga kinyi aure kema, Dan haka nide indan tanine karki damu, Allah yasa mudace gaba daya, maisah cikin sanyin jiki tace zanyi tunani insha Allah
Amal tace yauwa qawata kokefa
Sun dade suna fira sannan sukai sallama maisah tatafi gida
Shahid ne yazo yacewa Amal taje ta kwashe kayan dasukaci abinci, ta tashi tatafi Dakin Shima yayi wajan baba
Tana zuwa Dakin ta ganshi a zaune yana amsa waya, saida tabari yagama sannan tace Yaya daddy Ina kwana?

Kallanta yayi yace haka ake gaisar da miji?

Itama tace Tome zance?

Yace tsaya in nuna miki
Tashi yayi yaje ta Bayanta ya tsaya, ahankali yasa hannayensa Akan hips dinta, yasunkuyo da kansa dede wuyanta cikin muryar rada yace "baby Ina kwana?"
Kasa amsawa tayi, tayi shiru tana Jin wani iri ajikinta
Acan falo kuwa umma ce tace bari kiga naje da kaina na kwashe kayan dasu Shahid suka bari nasan wannan sakalalliyar yarinyar tanacan ta qunshe adaki
Dakin dasu Amal suke ciki ta nufo, tana zuwa bakin kofar idonta yayi Mata kyakykyawan gani, ayanda taga yasunkuyo da kansa dede wuyanta babu Wanda zaice ba kissing dinta yakeba, shikuma gaisuwace yake miqawa
Allah yaso sunbawa kofar baya, da anyi abin kunya
Dasauri ta juya, Tasa hannu ta dafe kirjinta, yanzu yaran nan banda rashin kunya agidan surukai?

Lalle Allah yakawo mu wani irin zamani
Juyawa tayi taje Dakin baba tace Malam yakamata mu tafi kada muyi dare tunda yau zamu dawo, baba ne Yadubi Shahid yace jeka kirasu mudau hanya ko?

Shahid yace to baba
Saida yayi sallama sannan yashiga yashiga Dakin lokacin har Amal ta fice
Basu Bata lokaci ba suka futo
Dazasu shiga motar ne sukaga daddy yasaka wannan hular
Nan da nan kuwa kamarsa ta buya, baba yace karaamullah saboda mutane ko?

Kansa aqasa yace eh baba, key din yabawa Shahid yace gashi kakaimu Shahid
Suka shiga motar, suka tafi, shida Shahid agaba, Amal da baba da umma abaya
Sunyi Nisa ahanya Amal ta katse musu shirun ta hanyar cewa baba ingayama Yaya Shahid yakusa aure, saboda nayi masa mata
Baba yace yaushe kukai maganar keda dan'uwan naki bamu saniba?

Toma wacce me sa'ar ce wannan?
Chapter 25 · 0% Book details