← Book details Burinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 39

Sashe 4

Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau baiga fuskar dazaiyi shagwaba ko tambaya ba, Dan haka baiyi wata wata ba yasa hannun suka cinye qwan
Amma cikin ransa fadi yake qwai Dan millili haka saikace gidan yunwa
Kuma ace mutum bai Isa yayi maganaba?
*** *** ***
Gaskya abinda na fahimta gameda kalamansa shine, yana baki hakuri ne Akan wani laifi dayayi miki, sannan Kuma yana buqatar ku qulla qawance tsakanin ku
Tace to dama Ana qawa da namiji Yaya?

To shide ga abinda yace nan, meyasa kike cire niqab dinki Bayan kinbar gida?

Cikin tsoro tace Allah yaya bancire ba
To baki cireba tayaya akai yaganki har zai turo miki da wasiqa?

Ai shikkenan kiyi yanda kikeso rayuwarki ce, niyyarki ne ki amince, kokuma akasin haka
Tashi yayi yashiga ciki, gabansa yana mugun faduwa
To Wai ita Dan Allah me Yaya Shahid yake so tayi?

Itada tazo domin aqara yimata bayani Akan hausar, kuma zaiyi fishi yatafi?

Kuma yace ta amince ko karta amince
Wullar da wasiqar tayi, tabishi abaya
*** *** ***
After 3week
Salma!

Yakamata ki tashi ki hada mana break fa inaso zan fita
Juyi tayi daga cikin lallausan blanket dinsu, domin kuwa basu taba Raba wajan kwana
My dear wlh banjin karfin jikina, bazan iya tashiba, please zo
Matsowa yayi wajan ta da mamaki, kafin yayi magana ta janyo shi jikinta tana shaqar turaren daya fesa
Jikinta yaji zafi rau, da sauri yace subhanallah, wayarsa yadauka yakira family doctor dinsu, ita kuwa tana jinsa tayi luf ajikinsa
Doctor yana zuwa yaduba ta, ya tabbatar masa da cewa tana daukeda juna biyu na Tsawon sati biyu
Daddy daskarewa yayi awajan, Yama rasa da bakin dazaiyi magana
Doctor ma yalura da halin dayake ciki Dan haka yadafa kafadarsa yana murmushi yajuya yafita
Yana fita daddy yakaiwa Salma wata wawar runguma
Yasake ta yayi sujjada yagodewa Allah, yasake dawowa ya rungume ta, ita Yama Bata daria wallahi, Gaba daya ya cukwikuya babbar rigar sa
*** *** ***
Malam dama zuwa nayi in qarama godia Akan maganin daka bani, gaskya naji dadi sosai, OKASHA yana Nan yashiryu yadena shaye shaye, Babu ruwansa yanzu wlhy Abu yayi kyau sosai yanzu hakama karatu nake San turashi qasar waje
Baba hamani yace ahhh Abu yayi kyau alhaji, haka ake so ai
Shahid ne yashigo Bayan ya gaida alhaji yace baba ga mukullin shago zanje filin ball
Yace to Shahid saika dawo
Yana fita alhaji sidi yace a a Malam dama kanada yaro babba haka?

Baba hamani yace danmu biyu ne ai alhaji, Shahid ne babba Sai Amal, itada Tayi diploma, shikuma yayi NCE anan kusa damu Gumel
Alhaji sidi yace gaskya nayaba da hankalin sa sosai Malam, inaso kabani takardunsa sannan Kuma kabani dama inturashi Indonesia karatu shida Dan wajena okasha
Fara'ah ce ta bayyana afuskar baba hamani, yadinga yiwa alhaji sidi godia
Alhaji sidi yace ainine da godia Malam, okasha shi kadai na mallaka, ta Sanadin ka dakuma temakon Allah Yarona yazama cikakken mutum
Ai babu abinda zance dakai Malam Sai godia
Sannan shikuma Shahid kafada masa yazama ready, banaso su qara one week a qasar nan
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Alhaji sidi bai Bata lokaci ba wajan karbar takardun shahid yatafi dasu gida wato Kanon Dabo, inda yafara cuku cukun nema musu school shida dansa
Baba hamani yana shiga gida yafadawa samiya wannan labarin, bakinta har kunne saboda tsabar murna
Amal ce ta futo daga daki Jin umma Sai hamdala take tun dazu
Tace umma me a kayi ne yau?

Nan umma tabata labari, Amma abin mamaki maimakon tayi murna kawai saita juya daki, iyayan babu Wanda ya lura da halin datake ciki, kasancewar suna cikin farin ciki
Tana shiga daki tafada kan yar madedeciyar katifarta tadinga kuka, Yaya Shahid zai tafi karatu, to dawa akeso taci gaba da rayuwa?

Kafin zuwa magrib zazzabi mai zafi yarufeta
*** *** ***
Yauwa hajia maimuna kawai kowanne kikawo dozin daidai mugansu, eh namaza dozin daya na matan ma haka, tunda bamusan me za'a Haifa ba
Abba yayi sakare yana kallanta da mamaki
Tana ajiye wayar datake tajuyo tace alhaji barka da dawowa
Wai hajiya, mezakiyi da kayan yara ne naji kina cewa akawo miki dozin dozin
A a haba alhaji, ya zakace me zamuyi da kayan yara
Ai gara mufara tarawa tun yanzu,
Abba yace wai kina nufin cikin sati biyun za'a fara yiwa siyaiya?

A a to alhaji so kake Sai an haifeshi sannan mufara siya
Dariya yasaki y
ace gaskya wannan jika naki zaiga gata
Tace ai alhaji kaide kawai Allah yakawo shi lafiya
Abba yace amin hajiya
Daga daki ta futo taci Riga da wando, kayan sun kama mata jikinta sosai, kasancewar batada jiki sosai Sai kayan sukai mata Das ajikin ta, tayi fakin gashin kanta dayasha gyara, tana zuwa tafada Jikin momy juwairah, cikin shagwaba tace momy Dan Allah kifada masa kinji
Hajiya tajuya tace to alhaji kaji, Wai yar lelen nawa tace adan daga mata kafa zuwa next week saita koma hutu
Abba yace hajiya yarinyar nan kina sangartata dayawa, mezatayi inta zauna agidan?

Banasan sakarci ta tattara yanata yanata Takoma school jibi, already sun fara lecture, daga kanta tayi daga Jikin momy juwairah tace Allah Abba basa farawa da wuri, yace banasan Jin komai, tunma kafin daddy yasamu labari ki shirya kibi flight din dazai tashi jibi, banda yawo da qawaye babu abinda kika iya, Dan haka karna sakejin maganar cewa Wai bazaki school ba
*** *** ***
Yana dawowa daga filin ball, wanka yashiga, yaje masallaci sallah, sai Bayan an idar ne ya hadu da baba hamani, baba hamani bai Bata lokaci ba wajan fada masa yanda sukai da alhajin dayazo dazu, yace to baba Allah yasa hakane yafi alkhairi, daga haka bai qaracewa komai ba, suna shiga gida yayi cikin dakinsa, yarasa me yake masa dadi, Anya kuwa zai iya rayuwa batare da Amal ba?

Yarinyar daya reni qaunarta acikin zuciyar sa tun batasan kanta ba, Rana daya kwatsam ace yaje yayi wata rayuwa batare da ita ba?

Anya yayiwa zuciyar sa adalci kuwa?

Zumbur yamiqe tsaye yayi dakinta, gara yaje yaga halin datake ciki, duk da yar tsamar dasuke da ita Akan wasiqar Malam nura
Yana zuwa kofar Dakin yace in shigo?

Yaji shiru yasake fada second time, still yaji shiru, Dan haka yasa kansa ciki
Yana shiga kuwa yaganta akwance, Dasauri ya qarasa gareta, yace qanwata
Dakyar ta Bude lumsassun idanunta ta kallashi, hakan datayi shiya haddasa masa shiga cikin wani Hali
Matsawa yayi ya zauna a gefe daya daga kan katifar Tata yace ki tashi zamuyi magana
Tana tashi data ganshi Sai maganar ummah ta Fado mata arai, aikuwa batayi wata wata ba ta fada jikinsa tasaki wani kasalallan kuka
Yasalam!

Abinda yafada aransa kenan, wannan yarinyar karta hauka tashi
Bayanta yake bubbugawa alamar rarrashi, tayi luf acikin kirjinsa, idanunsa a lumshe, yace kiyi shiru mana
Koso kike Nima kisani kuka?

Bata iya maganaba illa girgiza Kai datayi
Yace meyasa kika shigo daki ke kadai kikabar umma afalo?

Cikin sigar shagwaba tace Yaya Wai tafiya zakai nanda sati daya?

Yaya please karka tafi kabarni, dago da kanta yayi still tana kwance ajikinsa
Suka qurawa juna ido
Kenan taji maganar tafiyarsa shiyasa itama tashiga wannan halin
Ahankali yabude kyakkyawan lips dinsa, ya matso da bakinsa daidai nata, tamkar zai hade bakinsu waje daya
Cikin kasala yace bakyaso intafi?

Lumshe idonta tayi ta Bude alamar hakane
Yace to kiyi hakuri kinji qanwata, insha Allah duk inda naje zaki kasance anan dina
Yafadi haka yana yi Mata nuni da kirjinsa gefen da zuciyar sa take
Amal BURINAH akoda yaushe shine inkasan ce tare dake, infaranta miki, insaki walwala
Amal
Tace na'am Yaya
Yace kiyimin alqawarin har in dawo bazaki saurari kowaba, har yanzu ke yarinya ce, baki Kai matsayin dazakiyi soyaiya ba
Dakaina zan nema miki mijin daya dace dake kinji?

Jikinta ne yayi sanyi Jin kalaman sa, dayaji tana kula Yaya sham to inajin da saiya daketa
Yaya nayima alqawari babu Wanda zan saurara, Nima BURINAH shine in yima abinda ranka yakeso
Kinyi alqawari?
Chapter 4 · 0% Book details