Sashe 13
Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan Allah kayi shiru Shahid, kadena kokarin dukan mace ko Yaya take Dan Allah
Shahid yana huci yashige daki, okasha bai taba yima sa fadaba Sai Akan wannan jarababbiyar yarinyar, tayaya zai sota?
*** *** ***
After ten day's
Zabe yarage saura kwana biyu, kullum daddy baya gida, dagani Sai mai gadi, haka nayi ta zagaye gidan yau ni kadai, naci abinci nakaiwa iliya mai gadi, acan nayi zamana mukasha firar mu
Hannu na ya dade da warkewa
Da yamma nayi wanka nasa Riga da sket dinkin Jan less sosai nayi kyau acikin less din, yakarbi fatar jikina, hips dina sun futo sosai, haka rigar ma Ana iya hango albarkatun qirjina
Kawai nishadi nakeji yau, kuma nakira Yaya Shahid bansameshiba, na zauna afalo na kunna kallo, kamar wasa nace ke bari de yau inga menene adakin nan da daddy yake shiga
Dakin natura nashiga, da photunan ta nafara tozali, tsayawa nayi Ina kallan Dakin, ko Ina photunan salma, kan gadon na kallah Naga Rigar baccinta akai, kenan nan yake zuwa yayita kallan pictures dinta, ya rungume rigar baccinta
To tayaya ma zai kulani,?
Nan take naji wani qullulun baqin ciki araina
Aigara ni rayaiye nakeso, shikuwa Akan matacciya yakasa dubani, bai damu da cina da shana ba, kamar an ajiye masa gunki
Hararar photon nayi, afili nace Allah yaji qanki de
Computer nagani agefen gadon nasan tasace, Dan haka nadauka Nakai falo, nacire dankwali na, naci damara dashi, nakwashe pictures din duka Nakai dakina, naduba ko Ina, banbar komai nataba
Tas nakwashe komai nakaishi dakina, inata fada, ni za'a renawa hankali, nan gaba Naga inda zaka dinga shiga
Computer nadauka nahau sama, Nakai masa ita dakinsa, wannan ne Karo nafarko dana shiga Dakin, komai na Dakin red ne, Dakin yayi mugun tsaruwa kamar ba Dakin namiji ba
Akan bedside drawer na ajiye computer
Kallan Dakin naci gaba dayi, anan Naga pic dinsa babba, yasaka suit, yana daria, sosai photon yayi mugun kyau
Agefen gadonsa Naga wani Dan qarami, shikuma na salma ne, afili nace, afili nace, bacci salma, Rana kana Dakin salma, tayaya za'a kalli Amal?
Photon nadauke nasauko qasa dashi, ina Tafe Ina sababi, nasan tunda nace masa idan yaci Zabe yasakeni nasan zai sakeni, tunda naji yayi shiru, Amma Kuma mutum ma ai rahma ce, duk da zai sakeni Bayan zaben ai ko gaisawa yaci ace munayi
Amma muna zaune zama kamar Zaman gaba, inata magana ta afili Shima pic din nasake kaishi dakina
Dirin motarsa naji, Dan haka nacire dankwali na daga da marar danaci, nariqeshi ahannu na
Ribbon din kaina nacire gashin kaina yabazu har Saman kafaduna
Yarfe hannu na nafarayi me ciwon inajin Bude kofar falon, Nakai kallo na gareshi
Shima din niyake kallah, shi wallahi Yama manta da yarinyar saboda harkar Zabe dayazo kusa, mekuma yasamu hannun nata?
Kallansa tayi yayi kyau sosai cikin manyan kaya farare
Ahankali tataka taje kusa dashi tana Yarfe hannun, ta miqa masa ribbon din Hannunta red color, kalar kayan jikinta
Tace Dan dauremin gashi na, hannu na ciwo yakemin
Idanunsa masu fizgar yanmata yazuba mata, Lalle ma wannan yarinyar
Yasan cewa da Allah yabashi haihuwa da wuri shida salma da tuni sun haifeta
Amma saboda yarinta shi zata renawa hankali tace masa ciwon ta kusan 1 month har yanzu bai warkeba
Kode jitake Shima Yaron ne kamar ta?
Comments dinku yana qaramin qwarin gwiwa
Please share
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Alama yayi Mata da kansa alamun ta matsa, zuba masa ido tayi ga ribbon ahannun ta, qara kawar da Kansa yayi alamun ta bashi waje, fuskar nan babu alamun wasa, tuni yayi Mata kwarjini, taja gefe guda tabashi waje
Da kallo tabishi harya haura sama,ko juyowa baiyi yasake Kallanta ba, haushi yasa tayi jifa da ribbon din Hannunta
Idanu ta zaro afili tace photunan matarsa
Ai aguje tayi dakinta, tare da kulle wa
Tafada kan gadon tana maida munfashi
Yana shiga dakinsa, yacire babbar rigarsa ya kwanta kan gadon yayi shiru yana kallan sama, daga baya yashiga toilet yayi wanka, jallabiya yasaka yasauko qasa
Dining ya kalla wayam Babu komai, wannan yarinyar Bata iya komai ba Sai shirme, antashi an aura masa wadda ko girki Bata iyaba
Juyawa yayi yashiga Dakin salma, tsayawa yayi yana kallan Dakin ganin komai yasauya
Acan Dakin Amal kuwa ta labe ajikin kofar Dakin, tana jiran sammaci, taji ya bude Dakin salma
Cikin bacin rai afili yace wannan yarinyar!!
Futowa yayi yazo Dakin ta, yatura yaji kofa gam arufe, qwanqwasawa yayi, tana jinsa tafara matsawa dabaya ahankali, sake qwanqwasawa yayi, tadaga murya tace Yaya daddy wasa nake saida safe
Kallan kofar Dakin yayi kamar ita yake kalla, tasan meta aikata ai dole ta rufe daki
Dakinsa yakoma, Idanunsa suka sauka Akan computer sa, kenan harnan tashigo, Lalle zai gamu da yarinyar nan
Computer yadauka yafara dube dube, wayarsa tadau qara dauka yayi tare da fadin jb ya akayi
Kai kuma shikkenan daga aure shiru ake jinka, wato kasamu sweet 18 ko
Girgiza kansa yayi ransa abace kamar jabeer din yana ganinsa, yace idan kasamu time kazo, katahomin da abinci a restaurant, yakashe wayar
Jb ya kalli wayar da mamaki
Shima anasa bangaren rufe computer yayi ya kwanta yafada duniyar tunani
Nikuwa kan gado nafada nasaki daria, afili nace hauka nake zan bude ka dakeni
Wayata na dauka nakira maisah, Bayan mun gaisa tacemin Ina oga, da fatan de komai lafiya?
Nace wacce lafiya maisah, nifa kinga Bama magana har yanzu, maisah zan iya cemiki tunda nazo gidan nan maganar arziqi Bata taba hadani dashiba,
Ajiyar zuciya maisah tayi, tace Anya Amal kina yiwa mijinki biyaiya kuwa?
Maisah wacce biyaiya sakinafa zaiyi
Subhanallah me kike fada haka Amal?
Shidinne da bakinsa yace zai sakeki?
To ai nafada masa idan yaci Zabe yasakeni na auri Yaya Shahid
Yasalam, Amal kanki daya kuwa?
Mijinki kike cewa yasake ki Amal?
Shin idan yasakeki kina tunanin baba zaiyi farin ciki da hakan ne?
Ke kanki idan yasakeki yamayar dake qaramar bazawara, ba Shahid kadai ba, a'idon kowama ke bazawara ce ba budurwa ba
Amal ki dawo hankalin ki, ki riqe aurenki dakyau, kede kifita haqqinsa, shi idan yasauke haqqinsa kansa, idan bai sauke ba yayiwa kansa
Nasan yanzu irin Dan Jan hankalin nan ma namata bakya yi Amal
Jikinane yayi sanyi dajin kalaman maisah, cikin sanyi jiki nace maisah wallahi inayi
Dazu ma haka nabashi ribbon nace masa hannu na yanamin ciwo ya daure min kaina, Amma shine ko arziqin magana bansamu ba, qarshe ma alama yayimin dakansa inmatsa tun kafin ya gabjeni
Maisah batasan lokacin datasa daria ba, tace Lalle Amal, to ai haushin dakika bashi ma kadai zaisa yakasa kulaki bare yayi miki magana, koni nan nasan ciwonki ya warke Amal, bare shi
Haka ake Jan hankalin?
Ki tashi tsaye ki gyara rayuwar aurenki Amal
Kidinga yimasa abinci, ya siyo abinci yakawo Amma saide kiyi kuci keda mai gadi
Shi ko oho
nace maisah idan nayi ma bazai ciba, tace kintaba yi ne yaqi ci?
Nayi shiru, tace yakamata de ki gyara, Dan gyaran Dakin nan, dayi masa magana ko bayaso, nide BURINAH shine inganki keda daddy Kuna shimfida soyaiya, kunyi bala'in dacewa da junanku Amal
Ina daria nace maisah soyaiya...
Nide nagode Sai anjima
Ina kashe wayar, nafada duniyar tunani, maganganun maisah gaskiya ne, saide wannan mutumin kome nayi Bana tunanin zai Kalle ni, amatsayin mace, tunda tunanin matarsa bazai barshi ba, Amma Kuma aita mutu, yanzu nice matarsa, gaskya de dole insake taku
Yana kwance adakinsa, jb yashigo, ya ajiye masa take away yace na shigo inata sallama babu kowa agidan ne?
"tana nan"
Abinda yace kenan
Jb yace to meke faruwa yau din, baka samu abinda zaka ci agidan ba?
Ajiyar zuciya yasauke, yatashi daga kwanciyar dayayi, yace jb idan nakama yarinyar nan Sai jikinta yagaya mata
Subhanallah daddy meke faruwa ne?
Tashiga Dakin salma takwashe min pictures dinta gaba daya, tashigo dakina tadaukemin Wanda suke nan
Yaushe nafara wasa yarinyar nan jb?
Ajiyar zuciya jb yasaki, cikin ransa yace alhmdlh Zaman lafiya yakusa fara wanzuwa
Afili kuwa yace haba daddy kayi mana kasan fa yarinya ce
Nikuwa nasan yarinya ce jb
Dazu fa....
Saikuma yayi shiru, yaci gaba da fadin ni ban iya ko dafa shayi ba, kullum Bata bani abinci, narasa aure akamin kokuma Reno aka bani, kawai jb Bayan Zabe zan saki yarinyar nan
Dasauri jb yace Lalle daddy bakada hankali, karma kafara
Nagaji da Zaman Dakin Dan haka na futo falo domin infara gyarawa kamar yanda maisah tabani shawara, nagama shara Ina mopping naji takunsu, ina daga Kai mukai ido hudu dashi, ai aguje nayar da moper nayi daki jikake garam narufo kofar
Me jb zaiyi inba daria ba, wannan gida akwai drama
*** *** ***
Washe gari Ina zaune afalo iliya mai gadi yazo yace Ana sallama Dani awaje, Dan qaramin hijabi na saka iyakarsa qirjina, ina futowa harabar gidan Naga wasu mutane su biyu, har rissinawa sukayi suka gaidani, nide nacika da mamaki, sukace ranki yadade anbamu umarni ne azo ayi Miki voters card
Araina nace ikon Allah
Nace to bissmillah, kujera iliya yadauko akayimin abuna, Babu Bata lokaci aka yi aka ciromin abina, dazasu tafi nace ku tsaya, nashiga ciki Dasauri nadauko musu ruwa da lemuka nace gashi kwasha ahanya banbaku ruwaba har zaku tafi, fuskar su dauke da fara'ah sukamin godia suka tafi
Suna fita daya yadubi dayan yace gaskya maigida yayi sa'ah, kaduba kaga yar qarama da ita Amma Babu girman Kai babu komai harda bamu abinsha, dayan yace eh gaskya wannan dole yaboyeta, kwanaki naji wasu samari suna cewa ba'a taba ganin matar daya sake aura ba
Kaikuwa me wannan dalleliyar matar Ina zai bari aganta?