Sashe 35
Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga masa Kai tayi, tana hawaye, ahankali yasa harshen sa yashare mata hawayen duka, sannan yahade bakinsu waje daya
Saida yayi kissing dinta sosai, sannan yadago da fuskar sa yace kin hakura?
Cikin sanyin jiki ta rungume shi, tana Ajiyar zuciya
(Ummy Abdul Nima comment dinki yatafi Dani kamar yanda BURINAH yatafi dake
Gaskya babu abinda zance da masoyan wannan novel, tsakanina daku Sai godia
Godia ta mussaman ga masoyan BURINAH na Facebook, haqiqa inajin dadin yanda kuke zuba Sharhi Akan BURINAH, but Dan Allah karkuce yayi kadan Dan nasan Hali
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Haka suka zauna tana rungume ajikinsa har tsawon wani lokaci, yana ta faman bubbuga bayanta alamar lallashi, har bacci ya dauke ta
Ahankali ya kwantar da ita Akan gadon sannan yayi kissing goshinta yafita daga dakin
Direct dakinsa ya wuce Shima, yafada kan gadonsa gamida rufe idonsa
Koda wasa bai taba tunanin soyaiyar wata yarinya zata yi masa mugun kamu kamar hakaba Bayan salma
Sai gashi zai shiga wani Hali saboda rabuwarsa da baby
Ko Yaya zai iya rayuwa Bayan Bata nan?
Bayajin yanda yake tsananin kaunarta zai iya wata biyu batare daya sakata acikin qwayar idon saba
Murmushi yasaki lokacin daya tuna da darun datayi masa na dazu, Wai ya nasan arabasu
Baby kenan Uwar rigima
Dena murmushin yayi lokacin da maganar salma tafado masa arai, yatuna lokacin dasuke wasa da fillo a falon su Momy yace
"salma kibani wannan fillon "
" gwalo tayi masa tace bazan baka ba saikayi murmushi "
" inkinga murmushi na to amarya ta nake yiwa
Ashe kuwa hakanne, gashi yanzu yanayin murmushin ga baby akoda yaushe
*** *** ***
After one week
Rana Bata qarya, inji bahaushe
Suna tsaye acikin airport din gaba dayansu
Amal na Jikin momy Sai kuka take, momy tace Amal kiyi hakuri mana, ai Zaman nadan wani lokaci ne zaki dawo kinji yata?
Cikin kuka tace momy ni banasan rabuwa dake
Jikin momy yayi mutuqar sanyi, ita kanta batasan rabuwa da yarinyar, juyawa tayi ta kalli Abba
Shima cikin ransa quna yake, Dan haka cikin sauri yakawar da kansa Dan karsu gane halin dayake ciki
Yadubi daddy yace to karaam, ai babu wata matsala ko?
Cikin dauriya yace Abba babu damuwa, insha Allah idan munje zanyi kokarin samar mata da komai
Abba yace to kace baka buqatar doctors dinma
Daddy yace Abba ai can ma sunada qwararrun likitoci, jb yahadani da wani doctor zanje wajansa mu tattauna saiya bamu qwararrun likitocin mata zasu yi Mata komai
Abba yayi Ajiyar zuciya yace Toshiknn, Allah yakaiku lafiya
Shahida ta rungume Amal ajikinta, tana sake rarrashin ta, Shahid ya matso yace duk kune kuke sake shagwaba yarinyar nan fiancee
Yadubi Amal Yace qanwata, Allah yakaiku lafiya
Hararar wasa tasakar wa Shahid din, daddy yana kallansu yana murmushi
Komawa yayi wajan jama'ar da sukayi dandazo wajan rakoshi airport
Haka yayita meqa musu hannu, suna sake musabaha sannan yajuyo yakamata hannun Amal yariqe
Sukayi sallama dakowa suka yi ciki
Babu Bata lokaci aka bada umarnin shiga jirgi, Kai tsaye inda manyan mutane suke zama acikin jirgi suka nufa, kamar govnors da sarakuna
Basufi minti goma da shiga jirgin su ya Lula zuwa Malaysia
*** *** ***
Already yariga yayi musu booking din komai na inda zasu zauna zuwa wani lokaci
Dan haka Kai tsaye jirgin su na sauka direct gidan aka kaisu
Sosai gidan yayi masifar haduwa, daga wajansa ya qawatu da shuke shuke masu gwanin sha'awa
Bawani babban gida bane Amma yanda aka tsarashi ne kadai zaisa ya birgeka
Cikin falon komai milk and ash color ne hatta dining table din haka kalar su take
Cikin kitchen Din kuma komai green ne, dakuna ne guda biyu da aka qawata su da furnitures launin pink da baqi
Shine yayi Mata jagora har cikin gidan, ita Kam Sai Kalle Kalle take
Dubanta yayi yana cire babbar rigar jikinsa, ya ajiyeta Akan kujera yace kihuta baby, zanje in dawo
Kallansa tayi tace Amma my dear ni gaskya tsoro nakeji
Daddy yace babu abinda zai sameki baby, nuni yayi Mata da kofar falon yace dubafa akwai megadi, ki shiga kiga gidan idan akwai abinda bai miki ba saiki fadamin idan nadawo, dama ni na ganshi awaya tun kafin muzo
Cikin shagwaba tace to Amma karka dade
Yace angama baby nah, yasakai yafice daga falon
Tashi tayi ahankali tana kallan gidan, saida ta zagaya ko'ina, tanata murmushi ita kadai, gaskyar Abba dayace tana buqatar waje marar hayaniyar mutane, yanzu de duba yanda gidan nan yayi sosai, komai ya birgeta
Saide matsala daya zata zauna tsawon wani lokaci babu BURIN ranta atare da ita
Ajiyar zuciya tasauke, ta ja
nyo jakar kayansu tayi cikin daki da ita
Rigar bacci ta janyo ta ajiye Akan gadon, sannan tadaukowa daddy nasa kayan baccin
Sannan ta daura towel tashiga wanka, tana futowa ta Bude jikinta da turare
Takama gashin kanta tayi kalba qwaya daya dashi, jelar gashin tasauko agadon Bayanta
Hijabi ta nema tayi sallolin da ake binta, sannan ta cire hijabin tafuto falo
Bata dade da zamaba, daddy yadawo
Akan kujera ya zube yana cewa wash baby
Cikin daria ta dube shi tace kagaji ko Yaya daddy?
Sannu, tashi muje kayi wanka da sallah saika kwanta kahuta
Kallanta yayi cikin sauqin so yace ai nayi sallah awaje, naje nasiyo abinda zamu ci ne, sai kuma wajan doctor danaje Akan maganar ki, insha Allah gobe zai turo mana da doctors din dazasu dinga lura dake da babynmu
Daya zata dinga zuwa da safe har dare
Dayar kuma zatazo da daddare Sai Washe gari da safe idan yar'uwarta tazo saita tafi gida
Kallan mamaki tayi masa tace Yaya daddy saikace wata yar Sarki?
Hannunta yakama ya riqe sannan yace ai awajena kinfi Sarkin ma baby
Tace to naji, muje kayi wankan yanzu
Yace no Zona fara baki abinci tukun, idan na tabbatar babynmu ya qoshi sainaje nashirya Nima inzo kibani nawa
Kallansa take da tsananin mamaki, wannan wanne irin so yakewa wannan cikin?
Batace masa komai ba Takama hannun sa tana janshi, tace bazan ci komai ba, saina tabbatar kaima ka gama komai, saimuci abincin mu kwanta, Naga kagaji sosai
Binta yake da kallan luv, ashe Shima an damu dashi haka
Babu musu yatashi sukaje ciki yayi wanka, itace ta taimaka masa yashirya, sai shagwaba yake zuba mata
Falon suka dawo, suka fara cin abinci, shida kansa yadinga Bata harta qoshi
Sannan Shima yaci nasa
Dakanta ta tashi taje ta Bude fridge a kitchen, komai da komai akwai, hatta kayan fruit Ba'a bar komai ba
Ruwa da just tadauko musu tareda cup
Bayan sunsha ne,daddy yatashi da kansa yaje ya maida
Daukarta yayi cak suka koma kan doguwar kujera, tana kwance a Kirjinsa
Cikin rada yace baby kinsan me?
Kanta ta girgiza masa batare datayi maganaba
Yace lokacin da mukaje Germany natuna, kowa baya kula dan'uwansa
Sai yanzu ne Naga babban gangancin dana tafka wajan rashin kula dake
Dagowa tayi da kanta tana kallansa ta rufe masa baki da Hannunta
Cikin daria tace Dan Allah kabari
Karkasa natuno halinka nada daria tayimin yawa
Kallanta yake yana zuba mata murmushi yace menene halin nawa nada?
Kwaikwayon maganar sa tayi tace "idan kin gama zamu fita"
Sannan tasake cewa "karki batamin lokaci minti goma nabaki"
Daddy baisan lokacin da yasa daria ba
Yace kai baby banda sharri fa
Hararar wasa ta sakar masa tace bawani sharri
Haka sukai ta tuno abubuwan dasuka faru dasu abaya suna daria
Daga qarshe suka kira yan nigeria kowa da kowa suka gaisa sannan sukayi cikin daki suka kwanta
*** *** ***
Amma gaskya Shahid babu abinda zance dakai saide nace Allah ubangiji yayi muku albarka gaba dayanku
Shahid yace amin baba
Qwallah ce ta cika idon baba hamani afili yace Allah yaji qanka ibrahima, Allah yamaka rahma
Shahid yace baba kayi shiru haka mana, umma dake gefe tace a a Shahid wannan abun farin ciki ai yafi karfin ayi shiru
Wayarta ta dauka ta kira layin dasu Amal suka kirasu dashi, tana shiga wayar na hannun daddy
Shine yafara dagawa saida suka gaisa sannan yabawa Amal wayar
Suna gaisuwa umma tace Amal din baba, yayanki fa yabiya mana umara nida shi da babanku dakuma shahida, ankusa gama komai cikin wani satin zamu tafi
Cikin farin ciki Amal tace wayyo Allah umma tah
Umma Dan Allah idan kunje nide haqorin makka nakeso, da turaren wuta irin na larabawa mai qamshi, da abaya
Umma ce ta dakatar da ita tace to shashasha, kede kullum bazaki girma ba, memakon kice abaki Shahid din ki sake yimasa godia kokuma abaki babanku kiyi masa murna a a Sai kika hau lissafi
Cikin shagwaba tace Kai umma to Naga Yaya Shahid din yayanane
Umma tace keni Sai anjima
Wayar umma ta kashe tabar Amal da waya a kunne
Daddy dayakejin duk abinda suke fada, baisan lokacin da yasa daria ba yace me haqorin makkah, a a kaga hajiya Amal
Fillon dake gefenta ta dauka tafara jifansa dashi
Yana kaucewa, haka sukai tayi dashi suna zagaye cikin falon
*** *** ***
Atamfa ce ajikinta light blue Sai adon pink da baqi ajikin atamfar
Sosai dinkin ya karbi jikinta
Farar fatar ta tafuto Shar aciki
Fuskarta tasha makeup, tasaka pink din Jan baki a yan qananan lips dinta
Daurin datayi akanta ne yabawa gashin kanta damar zubowa agadon Bayanta
Yana tsaye cikin ash din suit, tana daura masa agogo qirar Gucci
Fuskarta babu alamar farin ciki
Takalmin sa ta dauko qirar Italy ta tsugunna Takama kafarsa ta Zura masa takalmin
Temako daya yayi Mata shine daga mata kafarsa
Sumar kansa ta taje masa, sai sheqi take, sannan tashiga fesa masa turare
Tana gamawa ta ajiye turaren tayi hanyar falo idanun ta nazubar da hawayen data Kasa riqewa
Cikin sauri ya fuzgota jikinsa
Babu Bata lokaci ya rungume ta tsam ajikinsa
Hawaye ne suka sakko asaman kyakkyawar fuskar sa, yayi sauri ya goge karta gani yasake kashe mata jiki
Kuka take sosai, harda sheshsheka, cikin sanyin murya yace kiyi hakuri baby
Insha Allah bazan wuce wata daya ba zanzo naganki tareda babynmu kinji?