← Book details Burinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 39

Sashe 5

Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi ma yayanah
To muje inbaki abinci, Kisha magani
To yayanah, Sarai ta ware suka fita daga Dakin
*** *** ***
After 2 weeks
Tafiyar su Shahid ta tabbata, inda aka gama musu komai da komai shida okasha
Umma da baba da Amal ne suka rakashi har airport
Okasha yana kallansu, shiko ajikinsa, asalima Bluetooth ne akunnansa yanajin waqa
Lokacin da aka kirasu shiga jirgi Amal kuka Shahid kuka
Umma cikin ranta tanajin tsoron wannan al'amari na Shahid da Amal
Amma Allah yasa ba abinda take tunani bane
Suna shiga jirgi, Babu Bata lokaci suka Lula Indonesia, saida su Amal sukaga tashinsu sannan suma suka dau hanyar dawowa gida, suna shiga Mota ta riqe kanta da hannun ta dayake barazanar tsagewa,
Bayan sun dawo gida saida umma tayi da gaske sannan Amal tadan saki jikinta kadan, shikkenan babu Yaya Shahid, Babu meyi mata wasa, Babu me rarrashinta, Babu me tsokanar ta, sai hawaye
, Allah ya kyauta, abinda umma tace kenan taci gaba da abin gabanta, duk da itama taji ajikinta wannan Tafiyar ta Shahid
*** *** ***
Suna sauka suka hau taxi ta kaisu gidan dazasu zauna kusa yake da school, kasancewar okasha kansa awaye yake basa shan wahalar komai, darana suka sauka Dan haka suka shirya zasuje makaranta su qarasa registration daga nan kuma suje su siyo Sim card domin Kiran yan gida
Bayan sunyi wanka, okasha yashirya dawuri ya zauna yana jiran Shahid, yayi kyau cikin qananun kaya
Yana Zaman jiransa Sai gashi yafuto da yadi ajikinsa Riga da wando rigar tsawon ta har qasa, ko hula babu yace masa muje
Okasha baisan lokacin daya tuntsure da daria ba, yafara nuna shi da hannu, haba gaye, ya za'ai Kasa wannan kayan Dan Allah
Shahid dayakejin wani daci aransa saboda rabuwarsa da Amal yace okasha please tashi mu tafi Dan Allah
Okasha yace to kaga Ina zuwa, dakinsu yaje yabude jakarsa yadauko wasu arnun kaya qanana, jar Riga, baqin wando, yace gashi Kasa wannan kafin muhuta zuwa gobe muje shopping Dan Nima banzo da wasu kayaba
Shahid yace kagani babu wani kaya dazansa Malam kawai muje
Dakyar okasha yasa Shahid yasaka kayan, sannan yabashi wani agogo yasa qirar Gucci, saiga Shahid harta taje lallausar sumar kansa ta buzaye mai kama da ta yan hindi
Dasauri suka futo saboda basaso suyi latti basu tsaya ko Inaba Sai University of Indonesia
Suna shiga harabar makarantar sukaga mutane atsaitsaye wasu a zaune kowa yana harkar gabansa
Abinka da basabanba nan Shahid yadaga Kai yana ta kallan yanayin makarantar
Garam yaji yayi Karo da mutum har hakan yayi sanadiyar faduwar wayarta
Cikin sauri yace yasalam ya tsugunna yana dauko mata wayar
Jin hausa a bakinsa yasa cikin masifa da bacin rai tace Malam wannan wanne irin shirme ne?

Dagowa yayi ahankali yana qare mata kallo daga sama har qasa dama wannan yarinyar bahaushiya ce?

Aishi jiyake arniya ce, saboda dasu shigarta take kama
Wayarta yabata yace kiyi hakuri Dan Allah ban lura bane
Wayar takarba takasa cewa komai, yace kiyi hakuri
Yaji tasake yin shiru, akaro na uku yace kiyi hakuri
Kawai yajuya yatafi
Qawarta ce ta girgiza ta tace SHAHIDA me kike tunani ne?

Jamcy wallahi wannan gayen yatafi da Imani na
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Shahida me kike fada haka? daga ganin mutum?

Kobaki ganshi bane?

Babu alamar wayewa awajansa
Kinga jamcy idan bazaki soshiba, kada ki qara kusheshi agabana, tana fadar haka tayi gaba
*** *** ***
Hello ummatah, na'am Shahid din umma
Yaya kukaje?

Kafin tabashi amsa Amal ta fizge wayar tayi daki cikin murna da zumudi tace yayanaaaah!

Baisan lokacin daya lumshe idonsa ba, Amal din Yayanta
Yaya yakaga Garin, Yaya tunda katafi nake kuka wallahi har kaina saida yayi ciwo
Haba yammatan Yaya karkisa yayanki yakasa yafewa kansa a dalilin rashin lafiyarki, ki kwantar da hankalin ki babyn Yaya, shekara biyu zanyi in dawo kinji
Allah yaya da gaske, serious Amal, ai kinsan an jonamin da result dina ne na n.c.e, Dan haka Shahid bazai dadeba zai dawo wajan...

Kafin yaqarasa tace wayyo yayanah, Allah yakawo ka lafiya, harna fara qirgawa azuciyata
Karki manta de da alqawarin dakika daukarwa yayanki
Yaya karka damu, bari nakaiwa umma wayar muahh tasakar masa kiss tawayar
Mutuwar kwance ce kawai Shahid baiyiba
Bayan sun gaisa da umma da baba ne yayi musu sallama
*** *** ***
After 6 months
Karatun su Shahid yayi Nisa sosai, sun hadu da wani dan nigeria guda maisuna nazir, suna kiransa da nazy
Sosai suke mu'amularsu, Babu ruwansu da kowa, su ukun nan de Koda yaushe haka zaka gansu, haduwa Shahid da nazy da okasha shine dalilin gogewarsa
Yaqara wani kyau na tashin hankali, har yakasance duk inda yashiga saiya tafi da imanin yanmmata, sau dayawan lokaci haka kawai yana zaune zakaga yanmata sunzo sunce masa su nasan yin pictures dashi
Haka zai tsaya suyi
Sosai Shahid yagoge yaqara wayewa
Dayayi pictures zai watsa shi a media
Jama'ah kuwa kamar babu gobe, yanda suke tururuwar yimasa magana, musanman yanmata
Abangaren shahida kuwa tun tana daukar al'amarin da wasa, sai gashi abin yafara damun ta, har hakan yana nema yashafi karatun ta, inda ta yanke wa kanta hukuncin zata dinga bibiyarsa hartasan shi din waye, daga baya kuma ta labarta masa abinda take ji game dashi
*** *** ***
Tana zaune Akan gado, Shima yana kwance yadora kansa Akan cinyarta, yana shafa cikinta, sumar kansa take shafawa ahankali, my dear baka gajiya da shafa cikin nan, kaide Koda yaushe ka zauna Kanata aikin shafawa
Salma kenan, bakisan yanda na matsu Inga dana danaki bane, salma Ina fatan Inga munci gaba da rayuwa nida ke har abada tare da abinda zamu Haifa
Zuba masa ido tayi, yanda yake magana cikin, ashe akwai ranar dazata ganta daddy yana zuba mata kalamai haka
Batasan lokacin data qara rungume Shiba
Tace su hajia suna farin ciki da zuwan wannan babyn, kowama haka, nide fatana inhaifeshi lafiya,
Karki damu salma, insha Allah lafiya kalau zaki Haifa mana babyn mu
Tace karaam kayimin alqawarin zakaci gaba da sona har abada, idan namutu zaka riqe mana babynmu dakyau
Yayi mamakin kalamanta, yace salma karki sake irin wannan maganar please
Tace Toshiknn my dear nadena, haka taci gaba da shafa kansa har bacci ya dauke shi, ido ta zuba masa, itade tana kaunar mijinta, tana fata su kasance tare har qarshan rayuwar su
Cikinta ta shafa Wanda take kusa da haifarsa, tace Allah yakawo ka lafiya baby na,da Murmushi sosai asaman Fuskarta
*** *** ***
Samia bani shayi,
Daukar butar shayin tayi, tace Malam yaude Naga alama shayin nan yanayi ma dadi
Aidole Samia
Bakiga yau rawaninmu ba irin na kullum bane?

To saboda murnar saukar yata Amal ne
Ki duba fa kiga duk wannan kyautukan natane, haba Samia wannan ai abin alfahri ne, umma tace gaskiya ne, danma yayanta baya nan, aida saiyafi kowa murna
Baba yace gaskiyar ki Samia, zaiyi murna
Acan daki kuwa
Amal ce da Qawarta maisah
Sunata firar yanda saukar su ta kasance
Maisah tace Wai Dan Allah meyasa bazaki bawa Malam nura dama yafuto ba?

A a maisah, baimin ba, koba haka Bama ni yayanah yahanani kula kowa har Sai yadawo gida
Zaimin miji da kansa
Nikuwa Amal in tambayeki, Dan Allah yaya kuke da Yaya Shahid?

Kamarya maisah, wannan wacce irin tambaya ce?

Uwarmu daya ubanmu daya
Kuma kinsan de yanada ikon yin komai akaina
Maisah ta girgiza Kai alamar gamsuwa tace shikkenan, kice da Yaya sham din za'a yi, nace qwarai kuwa Amal ta shamsuddin ce
*** *** **
After 3 months
3:00 am daidai
Taji bayanta yasara, mata, dama tunda Watan haihuwar ta yakama takejin gabanta yana faduwa
Ahankali tasauko daga kan gadon saboda bataso ta Tadashi daga bacci, tana saukowa qasa, marar ta tayi wata iriyar murdawa, da karfi tasaki ihun wahala
Hakan ne ya farkar dashi daga baccin dayake
Dasauri yasauko daga gadon, yanufeta, salma sannu
Meyake damunki?

Inane yake miki ciwo?

Daddy bayana, marata
Gaba daya ya diririce yarasa mai zaiyi, jallabiyarsa yadauka fara qal da ita yasaka, yadauketa, baijira komai ba yana sakata amota yafigi motar Sai hospital
Kafin suje hospital din, Tafita ahayyacinta, suna Zuwa aka karbeta Sai labour room, anan yasamu damar Kiran iyayansa yasanar dasu
Afijajan momy juwairah tazo itada Abba
Daddy banda Santiri babu abinda yake yi, idanunsa sun kada sunyi jajir
Yarasa me yake masa dadi
Suna nan a tsaye har akayi Kiran sallar farko
Gab da asuba, likitan yafuto, atare suka miqe suna tambayrsa doctor tasauka lafiya?

Abba yace me aka samu doctor?

Shiru yayi yana kallansu, momy tace doctor Yaya Dai, kayi magana mana
Hajia saide kuyi hakuri, munyi iya kokarin mu domin muga mun ceto rayuwar ta, but hakan bai iyuba
Allah yayi Mata rasuwa, tare da abinda yake cikinta
Abba yace innalillahi wa inna ilaihir raju'un
Yayinda momy juwairah tayi jagwab ta zauna aqasa
Qarar faduwa sukaji, suna dubawa sukaga daddy yayanke jiki yafadi qasa asume
(please Dan Allah fans kuyi hakuri, nayi tafiya ne wlhy, shiyasa bansamu dama nayi posting da wuri ba, Amma insha Allah zaku dinga jina da wuri kamar Koda yaushe)
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Yana zaune a harabar school din, littafi ne ahannunsa yana dubawa
Hankalinsa kacokam yana kan karatunsa
Daga nesa kadan dashi nazy ne okasha, suna fira kadan kadan da lemuka agefensu
Tun daga nesa ta qwara masa ido tana kallansa, tarasa Yaya zatayi da soyaiyar wannan gayen
Ahankali take tafiya tayi kyau sosai cikin Riga da wando pink color tayi rolling da farin mayafi
Sallama tayi masa tare da zama, dago idanunsa yayi yazuba mata Su, a'ina yasan wannan face dinne?

Oh wadda yayarwa da waya, yafadi haka aransa
Amsa mata sallamar yayi, ya maida hankalin sa Akan littafi
Shiru ne yabiyo baya,shi yana karatunsa ita kuwa bil haqqi ta zuba masa ido tana kallan sa
Gaye duba can
Okasha yakai kallansa inda nazy yake nuna masa
Yace to Anya lafiya kuwa irin wannan kallo datake masa?
Chapter 5 · 0% Book details