← Book details Burinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 39

Sashe 2

Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kabilun dake zaune a damagaram sun hada da hausawa, fulani, larabawa da kuma abzinawa har zuwa shekara ta 1926 birnin zinder ne babban birnin Niger
Yawancin tattalin arziqin Yankin damagaram ya dogara ne Akan noma da kiwo dakuma kasuwanci
Yankin zinder na makwabtaka da wasu jihohin nigeria, kamar jihar jigawa ta kudu, sai jihar katsina ta kudu maso yamma
Acikin gida kuwa Yankin zinder na iyaka da agadez ta Arewaci da diffa ta gabashi da maradi ta yammaci
Malam Hamani danda daga wannan Yankin yake, matarsa daya mai suna Samia, Allah ya hore masa ilimi ta fanni daban daban, har hakan yasa yaransa suma suka koyi wani Abu daga cikin ilminsa, yagaji ilmi tun daga kakanni, dagashi sai dan'uwansa ibrahima Wanda Allah yayi masa cikawa tun bai dade da aure ba
Bayan iyayensa sun rasu ne, yatattara komai nasa,yahada kan yaransa sukayi qaura suka dawo nigeria da zama
Inde magani kake nema, basai nafadaba, kasan mutanan Niger suna da wannan baiwar
Cikakken bafulatanine na damagaram
Garin jigawa, qaramar hukumar maigatari, unguwar kofar fada, acan Bayan Gari sunada gidaje sababbi, cikinsu harda wani qerarran gidan wani dansanda dayake zaune a Abuja
Anan Malam Hamani yayi yasauka
Suna zaune lafiya shida iyalansa, haka kuma Koda yaushe gidan ba'a rabashi da mutane, masu siyan magani
Cikakken Hervarlist ne, haka kuma yanada Islamic chemist
Wanda dansa yake kula dashi
Yaransa biyu rak a duniya, Shahid da kuma Amal
Malam Hamani yana San yaransa, baya kaunar abinda zai taba lafiyarsu, yanzun nan zai zari takalmin sa yaje har gida yaci ma mutunci yadawo
Sabanin matarsa Samia datake da sanyin Hali
Shahid hadadden gaye ne na karshe, fari ne tass, yanada cikar gashin gira, hancinsa Dan daidai, bakinsa mai kyau, mai karatu duk yanda zan fasalta muku Shahid bazaku ganeba, Amma zaku fahinceni idan kukai tozali da pic dinsa abangon littafi na
Yanada fara'ah ga yar'uwarsa Amal, Amma inka dauketa da wahala kaga yasaki jiki da mutum awaje
Shaquwace ta gaske atsakanin su
Sosai yanada magana, Amma fa idan yaso, rashin karfin mahaifinsu ne yasa sauran kyansa rashin futowa
Amal kyakkyawar yarinya, yar lelen yayanta tare da babanta, ba siririya bace, ba kuma me irin qibar Nan bace
A a dede misali ne, jikinta amurje yake, batada wata alamar yunwa
Allah yayi Mata sura mai kyau da daukar hankali, akwai diri ajikin Amal, hips dinta abaje yake, yayinda boobs dinta suke madaidaita a tsaye
Kowanne irin kaya tasa kyau take, farace tass, Babu alamar quraje ko tabo ajikinta
Gashin kanta kuwa dogo ne sosai, mai shegen santsi, da cika, Amal kenan
Akan kataba Amal gara kaje kaciwa Malam Hamani mutunci, yaqi jinin ataba masa ita, yana kaunarta sosai
Kwata kwata shekarun ta basu wuce 19 year's ba
*** *** ***
Tana zaune a qayataccen falon nasu, atamfa ce ajikinta Holland mai tsadar gaske, lemuka ne agabanta tana Sha tana kallan labarai
Abba ne yashigo, jama'ah suna take masa baya, saida suka rakoshi cikin falon sannan suka juya
Zama yayi tare da kallan hajia juwairah, uwargida sarautar mata, kede Koda yaushe bakya rabo da kwalliya
Murmushi tasaki Wanda da gani kasan taji dadin maganar tasa har cikin ranta
Alhaji ai Kaine sirrin
Murmushi yasaki yace Allah ko
Batare datace komai ba,tace yanzu de sannu da zuwa, yakamata muje kayi wanka ka shirya Kasa wani Abu acikinka
Lemon dake gabanta yadauka yace a a aqoshe nake , wannan kwalliyar kadai ma aini ta wadatar Dani
Alhaji kaide bakada dama wallahi, Koda yaushe cikin zolaya kake
A a to kinga laifi na dannayi wasa da iyali na?

Tace a a
Yace yauwa namanta ban fadamiki ba, nasa abincika min maganin wannan Yaron, agwada ko za'a dace
Fuskarta ce tabayyanar da fara'ah, tace to alhaji Allah yasa adace, tunda anyi na asbiti babu cigaba ai gara akoma na Islamic din
Lemon hannun sa ya ajiye yace hakane Kam hajiyata
Gaba dayansu sukasa daria, domin kuwa maganar Tasa, tabata daria
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Dukanta yake da dorinar datake hannun sa, tana tsugunne idanunta jajir saboda tsabar kukan datasha, bazaki fadamin dalili ba?

To ita Wai meyakeso tace masa?

Cigaba yayi da dukanta har hakan yayi sanadiyar ficewar niqab din dake Fuskarta
Ido yazuba mata, saboda shi harga Allah kawai de yana ganinta tana zuwa school dinne, Amma baitaba ganin Fuskarta ba, saboda Koda yaushe tana cikin niqab
Jikinsa ne yayi sanyi, lokacin daya dakata da dukanta
Batace masa komai ba tamiqe tana goge idanunta da niqab din hannun ta
Borin kunya ne yasashi cigaba da fada gudun kada sauran dalibai su fahimci halin daya shiga
Da dorinar hannun sa yake nunata yace kiqara yi mana acuci maza kiga irin hukuncin dazan sake yimiki
Dan iskanci yara Dan kunga kun girma shine ba'a isa afada muku kuji ba, acuci maza do kace Awannan makarantar idan mutum bazai iya kiyaye wa ba, to karya sake dawowa
Yana gama fadar haka yajuya yabar cikin ajin
Malam nura kenan
Dasauri Rumaisa tazo ta rungume ta, tana goge mata hawayen idonta
Itama idanunta sun ciko da qwalla, tace
Kiyi hakuri Amal, kinsan Malam nura baida mutunci
Cikin sheshshekar kuka nace to Rumaisa yayakeso nayi?

Gashin kaina yake so na aske kokuma so yake na Bude kaina yagani
Ki yi hakuri Amal, zomuje mu zauna
Suna zama malama tashigo suka fara daukar karatu, dayake islamiya ce ta yamma, basu wani dau lokaci ba aka tashesu
Suna tafiya ahanya Rumaisa tana qara Bata hakuri Akan abinda Malam nura yayi Mata, tace Dan Allah karki bari baba hamani yaji
Amal tace karki damu Rumaisa nayi miki alqawari
Dahaka suka rabu kowa yayi gida
Tana shiga gida da sallama tayi dakinta, umma da Shahid suna zaune a tsakar gida, dayaga zata shige daki nan da nan yafara tsokanarta kamar yanda yasaba
Amalun aiki!

Dasauri ta juyo cikin sigar shagwaba tace umma kin ganshi ko?

Kawai sai Tasa kuka, basusan dama akusa take ba
Ba umma kadai ba hatta Shahid saida jikinsa yayi sanyi, saboda yasan cewa ba wannan ne Karo nafarko dayake tsokanarta ba, tunda tariga da tasan bahaka sunan nata yake nufi ba ko kula shi batayi
Amma yau abin harda kuka
Littafin hannun sa ya ajiye yaqaraso wajan ta, har sunajin numfashin juna
Yakama hannun ta yace keda waye?

Tace ni Yaya ba komai,
Tsareta yayi da idanunsa, cikin rashin wasa yace nace miki keda waye?

Kyaleshi tayi tashige falonsu
Shima binta yayi da kallo, tare da take mata baya
Zama yayi Akan kujera ya shareta, ganin ya shareta ne yasa tataso ahankali tafada jikinsa tasaki kuka
Yanajin ta ya shareta
Saita yaga kukan nata sosai takeyinsa alamar tana tare da damuwa hakan ne yabashi damar rungume ta ajikinsa
Umma tana daga waje tana kallansu batace komai ba kawai de ta girgiza kanta
"keda waye?

"
Abinda yace kenan
Cikin hawaye tabashi labarin Malam nura
Dasauri Yakama hijab dinta yacire aikuwa farar fatarta ce ta nuna shedar dukan datasha
Da mamaki yace shi nuran ne yayi miki wannan dukan?

Karaf akunnan baba hamani
Dagatawa yayi da shigowa falon
Cikin kuka Tace wallahi Yaya shine, Wai nayi acuci maza, ni wallahi Yaya bansan acuci mazaba
Kinga yi shiru, zan sameshi anjima har gidan iyayensa zanje
Yanzu bari inje indora miki ruwan dumi ki gasa jikinki ko?

Hawayen idonta ta goge tace yawwa Yaya to jeka
Kallanta taga yanayi tace mene?

Da ido yayi Mata Nuni da ita, Dan haka cikin sauri ta dagashi tana daria, Shima fita yayi, yafara neman tukunya
Umma cikin ranta tace haka de kuka iya, dagakai harshi
Shi yaji andaketa kokulani baiyi ba yafita
Kaikuma Kaine mai dafa mata ruwan wanka
Lokacin datayi aure aisai kubita gidan mijin kuci gaba dayi mata bauta
Da gaske yake wanke tukunyar, yaje fanfo yana tara ruwa, dagokan dazaiyi yaga tana masa daria
Kallan sa ya maida kan umma yace umma kiga yanda take min daria
Allah zan jiqaki
Lalle Yaya matarka ta huta da wanke wanke taci gaba da dariyar ta, aikuwa ruwan yatara a kofi ya watsa mata
Lalala Yaya shine ka jiqani
Aikuwa tana futowa ta dauki tiyo tatara, ta setashi nan da nan ya jiqe
Tiyon ya qwace ahannunta, tana kokarin karba shikuma yadaga kan tiyon sama aikuwa Sai saukar ruwan Sukaji akansu
*** *** ***
Cikin sauri yake tafiya,yaci baqar suit daka ganshi kaga cikakken S.S daya daga cikin security din gidan ne, yana zuwa falon ya tardasu a zaune Abba da momy juwairah
Rissinawa yayi yace yallabai angama binciken komai, komai da komai yana cikin wannan takardar
Takardar ya karba yabude, what!

Jigawa fa nagani
Ai yayi Nisa dayawa
Shide aqame yake baice komai ba
Glass din idonsa yacire yace zaka iya tafiya
Cikin sauri yajuya yafita
Momy juwairah tace yanzu de alhaji Muda muke nema aiko birnin sin ne maje
Yace hakane, Toshiknn zansa aje a karbo
Cikin sauri tace a a alhaji, Wai Yaya mun samu dama zakayi sakaci da ita, kawai kaje da kanka kokuma ni inje
Yace haba, taya zan barki kije, Babu damuwa insha Allah gobe zansa ashirya mana tafiya Sai muje, saide fatan Allah yasa adace
Tace amin
*** *** ***
Sallama yake kwadawa a kofar gidan
Salamu Alaikum!!

Daga ciki matar gidan tace Kai wannan wacce irin sallama ce haka Kamar Wanda yazo gidan makafi
Daga ciki tadaga murya tace Ana zuwa
Shima daga nesan yace basai kinzo ba, kituromin uban nura
Ha'ba ta riqe tace to uban nura kuma, wannan kuwa waye?
Chapter 2 · 0% Book details