Sashe 21
Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wallahi wajan yayi mugun kyau Yaya daddy, tafadi haka tana juyawa tana kallan wajan tareda wara hannayenta
Haushi kashe daddy
Gaba dayama yarasa maganar dazai fada Mata
Yanzu fisabilillahi yarasa Ina zaije yawo Sai wajan shopping?
Meyake damun tane Wai?
Fizgar Hannunta yayi, yajata qiiii Sai tafiya suke, saida yakawo ta wajan kayan kwalliya ya tsaya yace kidau abinda kike so gobe zamu wuce Nigerian
Ga mamakinsa Saiyaga ta Bata fuska, tace nagode babu abinda nakeso mu koma kawai
Matso wa yayi dab da ita, yayi qasa da murya kamar me rada yace karki min musu anan, ki dauka mu tafi
Tana zunbura baki ta daukarwa Abba turaruka, ita kuma tadau kayan kwalliya
Shiru tayi tana nazari me momy take so?
Sai can tasaki murmushi ita kadai, tasan momy akwai son ado, kullum cikin kwalliya take, Dan haka tajuyo ta cewa daddy zamuje wani wajan
Shikuwa Kallanta yake, yaga tana Abu kamar me jinnu, inba hakaba kiyi shiru kina tunani kuma ki saki daria ke kadai?
Wani abinma de sai yara
Zagayawa ta dinga yi awajan saida suka zo wajan saida yari, ta nuna masa wata hamshaqiyar sarqar gold tace adauko mata ita, me wajan kuwa ya miqo mata ita tare da Dan kunnan ta, sai ta kuma daukan Zabe na azurfa me kyau, sai kuma wani zoben Amma shi na gold ne, ta gwada ahannun ta, sannan ta cewa daddy tsaya anan Ina zuwa
Wajan kayan maza ta nufa ta dauko masa gajerun wanduna, da three quarters, sai best masu shegen kyau da tsada
Tazo tace masa nagama mu tafi
Kallanta yayi, Shiba Wai siyaiyar ce tayi yawa ba a a kawai Yana mamakin sarqa da dankunnan datace abata ne, mezatai dashi?
Anya kuwa tasan kudinsu?
Ita kuma Amal Sarai taga kudin sarqar, dubu Dari biyar ne, tunda tasan tazo da daddy tasan cewa batada matsalar kudi
Suna komawa gida tahada musu kayansu duka, tsarabar ta kuma tasaka acikin Jakarta, zoben azurfar data siyo ta kalli aranta tace nasan wannan zoben zaiyiwa Yaya Shahid kyau
Ta daga dayan zoben gold din, tace wannan kuma nasan zaiyiwa shahida kyau, bazan Bata hannu da hannu ba, Yaya Shahid zan bawa yasaka mata da kansa, nasan shahida zatai farin ciki da haka
Washe gari suka Lula nigeria, jirgin su na sauka motoci sukazo taryansa, jama'ah kamar me, dole Sai motar datake da baqin glass suka shiga wato tinte
Government house suka tafi Kai tsaye, motocinsu na sauka shahida ta futo da gudu tahadasu ta rungume su, sai sannu dazuwa take musu
Ba yabo ba fallasa Amal ta amsa mata, saida sukaci abinci suka huta
Sannan yasamu damar ganawa dasu Abba
Amal ce tafuto Fuskarta da murmushi tace miqawa Abba tureren data siyo tace Abba gashi
Yakarba yace masha Allah nagode sosai yata
Ta dauko sarqar data siyo ta bawa momy cikin ladabi tace momy kema ga naki
Duk Akan idon daddy
Momy tace Kai Kai masha Allahu Amma Amal kince nayi kwalliya naje gidan biki kaina tsaye
Gaba dayansu sukasa daria, Abba yadubi daddy yace babana to kaga yanda akeyi
Shikam mamaki ne yahanashi magana,kawai ya sunkuyar da kansa qasa cikin kunya, kenan ita Bata siyowa nata iyayen komai ba, nasa iyayen tasiyo wa, shikuma daya kamata yayi tunanin siyo musu, Shima bai siyo ba
Haka kowa yakoma dakinsa cikin nishadi
Washe gari suka koma gidansu, inda daddy yakoma bakin aikinsa
*** *** ***
Bayan kwana biyu takira maisah zata fada Mata abinda takeji game da daddy, sai maisah tace gobe gobe ma zatazo bauchi takawo mata ziyara
Amal de kawai tajita ne, Amma Bata yarda ba, haka sukai sallama
Washe gari daddy bai kwana agida ba, misalin karfe biyu saiga Kiran maisah tace Amal nazo, na qwanqwasa gidan maigadin bai budeba, Amal cikin mamaki tace wanne gida maisah?
Cikin daria maisah tace gidanku mana, ai aguje Amal tazo tabude mata gidan suka rungume juna
Suna shiga ciki aka Bude babin fira, tare suka shiga kitchen suka hada abinci mai rai da lafiya, sannan suka koma falo sukaita firar su
Maisah tace inajinki yar damagaram, Amal tayi Ajiyar zuciya tace maisah tunanin sa nake, idan na zauna ni kadai banda aiki Sai tunanin murmushin sa, da maganar sa
Koya batamin rai Ana jimawa zan manta inyita tunanin sa
Maisah takama hannayenta tace wa kike nufi Amal?
Kai tsaye tace daddy maisah
Amma shi baya sona, Bana gabansa, maisah tunda nake dashi bantabajin yakira sunana ba, bayamin magana saide inta kama dole, nikuma a jinsa birgeni yake wallahi
Maisah tace Amal, kin kamu da mahaukacin kaunar mijinki
Zare hannayenta tayi daga cikin na maisah tace tayaya?
Tayaya hakan zata kasance maisah?
Mutumin daya tsani inyi masa magana zan kamu da soyaiyarsa?
Maisah saboda nafita waje Ana ruwan sama nayi wanka, shikkenan yakori maigadin gidan, Wai nice zan dinga budewa tunda na zabi nuna wa maza jikina
Arana saina kirashi yafi sau nawa, Amma shi Koda wasa ban taba ji yakirani ba, kullum cikin Zaman hakuri muke nida shi
Maisah ce tasake riqo hannayen Amal tace, to Amal koma de menene, kina kaunar daddy, yanzu ai yarage namu, Wajan ganin mun shawo kansa yadawo kan layi, Koda wasa kada ki nuna masa kina sansa, Dan mazan yanzu sunce suna sanka ma Yaya aka qare, bare basu nuna suna soba,
Sannan kome zakiyi masa kawai kiyi abisa ke bakisan kinyi ba
Kidinga jansa da fira yanaso ko bayaso, sauran maganar kuma kawo kunnanki kiji
Rada maisah tayi mata, tace kin gane de, ke nida nake budurwa ma nice me gwada miki wadannan dabarun?
Maisah kin tabbatar idan nayi haka zai Soni Shima?
Sosai ma kuwa Amal, ki jarraba kigani
Amal tace Toshiknn, aikuwa zan aiwatar maisah
Haka suka tafi Dakin Amal, suka barbaje kayan akwatunan ta, maisah ta dinga ware mata wasu daban, tana qara wayar mata dakai
Sannan suka futo, suka Sha firar su, dazata tafi Amal tayi dibi dibi tarasa me zata Bata, tace maisah mezan baki?
Acikin gidan nanfa tunda nazo kudi nawa na kaina ban taba riqe wa ba, baya bani, maisah tace keni kin isheni da mitar mijinki, tsakanin ku, lokacin dazaku fara love bawanda yasani
Daria Amal Tasa, cikin ranta tana darurar aikata shawarar da maisah ta Bata
Saida ta raka maisah gar gate, sannan tadawo gidan ta zauna afalo, tana tunani, Wai ita keson daddy, mutumin dabawani kulata yakeba banda ganganci irin na zuciyar ta
Tashi tayi, tashige daki tafara hada kayanta tana gyarawa, afili tace daga yau zan fara kawo canji awajanka daddy
Nagaji da wannan rayuwar
Tunda kayi gangancin dana soka wallahi kaima saika Soni
Zakasan ka shigo hannun yar mutanan Niger
Tana ta magana afili tana shirya kayan acikin wardrobe
(Sharhi please)
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Bayan tagama jera kayan, ta tsaya ta kalli Dakin, nan tacire Dan kwalin kanta tayi wulli dashi, tafara gyara Dakin, tashiga toilet ta wanke ko'ina
Sannan tasaka turaren wuta me shegen qamshi adakin, tadauko kayan data siyawa daddy a Germany tatafi dasu dakinsa
Cikin wardrobe dinsa ta Bude tasaka masa aciki, sannan tahau gyara Dakin
Gadon tafara gyarawa tayi shara tayi mopping, taje toilet din nanma ta wanke shi ta gyara tsaf, hatta turarukan dasuke kan mirror saida ta sauya musu tsari, sannan tasaka wani turaren wutar mai qamshi daban
Nan da nan Dakin yayi hankali, kitchen taje ta gyara ko'ina, sannan tadawo falo nanma ta gyara, Gaba daya gidan qamshi ne ke tashi, daban daban
Saida tagama gyara ko'ina sannan tashiga kitchen tahada kunun Aya dayaji kayan qamshi, tadauko kwakwa da madara tahada Lemon kwakwa, tayi shinkafa fara dataji Karas aciki, sai kuma miyar ja da naman kaji
Takai komai dining ta jerasu, sannan tashiga dakinta tayi wanka, tana futowa daga wanka Ana Kiran sallar magrib, tayi sallah, sannan taje gaban madubi tafara tsarawa kanta kwalliya
Gashin kanta ta taje tayi fakin, ta Bude kayan data gama shirya wa dazu, wanda maisah ta ware mata, ta janyo wata Riga da wando tasaka, ta kalli kanta a madubi, tace Ina Bata yiba, tacire ta, tadauko wata Riga ja, iyakarta gwiwa, taduba takalmanta ta dauko wani baqi me shegen tsini tasaka, ta bude jikinta da humra
Sannan tafuto falon ta zauna tana kallo
Aranta tace yanzu duk wannan shirin idan bai zoba Yaya zanyi?
Yatashi a banza kenan fa ko?
Wayarta ta duba gaba daya batada number sa, afili tace kinyi sakaci kinyi sakaci Amal, ya Allah Kasa yadawo gida yau
Har wajan karfe tara shiru Bai zoba
Nanfa hankalin ta yafara tashi, ta tashi tsaye tana zagaye cikin falon da Wayarta ahannunta
Tara da kwata nayi, taji alamun shigowa gidan, saurarawa tayi, saikuma taji alamun rufe gate
Ta window ta leqa, ta ganshi tare da wasu mutane, da alama magana suke, saida suka gama tattaun
awa sannan taga dayan yabude musu gate din sun fice, shikuma ya juyo yanufo cikin gidan da yar qaramar jaka ahannunsa
Gabanta ne yake faduwa, me zatayi yanzu?
Karfa yamata kwarjini, cikin ranta tace Amal daure daure Amal kada komai ya lalace
Matsawa tayi Dasauri tabar wajan, Takoma tsakiyar falon tana zagayawa alamun tanada damuwa
Yana turo kansa cikin falon wani irin qamshi yadaki hancinsa, baisan lokacin daya lumshe idonsa ba
Tana dago kanta ta ganshi tasaki murmushi tatafi Dagudu ta rungume shi, tana cewa Yaya daddy oyoyo, nayi missing dinka
Tana riqe dashi tadago kanta ta kalleshi tace tsoro nakeji ni kadai tun jiya bangankaba, inata jiranka
Kasa magana yayi, Gaba daya ta cika shi da mamaki, saide wata irin nannauyar Ajiyar zuciya dayake saukewa
Itama Sarai taga yanayin daya shiga, Dan haka takama hannun sa ta riqe tace muje kayi wanka Kaci abinci
Kamar dolo haka yake binta, saida takai shi har dakinsa, sannan ta karbi jakar hannun sa ta ajiye
Babbar rigar sa takama zata fara cirewa tace masa, daga hannun mana Yaya daddy
Shide kawai binta yake da kallo, me yarinyar nan take shirya wa?
Tana cire masa rigar ta nuna masa toilet tace to bissmillah ko
Tajuya tafi ce daga Dakin
Bayanta yabi da kallo yanda hips dinta yake juyawa acikin rigar
Tana rufe masa kofar ta jingina da Jikin kofar Gabanta yana faduwa, Amal Ina kika samo wannan qwarin gwiwa?