← Book details Burinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 39

Sashe 22

Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida tatabbtar yashiga wanka sannan Takoma Dakin, Akan gadon taga ya zubar da kayan daya cire, tayi sauri ta dauka ta ajiye shi, sannan taduba cikin kayansa zata dauko masa wani kayan, taga kaya birjik aciki, wani wajan iya manyan kaya ne kawai, wani wajan suit wani wajan kuma qanana, rasa wanda zata dauka tayi aciki, sai ruwan ido take, idan tadau wannan saita maida ta dauko masa wani, daga karshe de ta dauko masa wando three quarter kalar Ja, sai rigar ta dauko masa baqa, ta ajiye Akan, jakar daya shigo da ita dauke zata saka masa Akan bedside drawer, Garin dauka mirfin jakar ya bude, daloli tagani aciki masu yawa, ta jinjina Kai, ita tunda take Bata taba ganin kudi hakaba, mayarwa tayi ta rufe, ta ajiye jakar sannan tafi ce zuwa falo
Saida yabata lokaci yana wanka sannan yafuto, da kayan data ajiye masa yayi tozali, baisan lokacin dayasa murmushi ba, wannan yarinyar?

Hmm
Kayan yadauka yasaka sannan yafara feshe jikinsa ta turare, turo Dakin Amal tayi tadawo, tana addu'ah aranta Allah yasa de yasaka kayan, aikuwa saitaga yasaka din
Jingina tayi da kofar Dakin ta zuba masa ido tana murmushi
Sannan tace Amma Yaya daddy wannan kayan sunyi ma kyau sosai
Tatako ahankali zuwa gabansa takamo hannun sa, hannun yabi da kallo yakasa magana, tace muje nabaka abinci, hannun su sarqe da juna suka sauka qasa sunyi kyau kamar kasacesu ka gudu
Har dining din takaishi, memakon ta zauna akujerar datake fuskantarsa, a a saita zauna akujerar gefensa, harda qara matso da kujerar, tafara zuba masa abincin, sai Kallanta yake yanda take komai nata cikin nutsuwa, gabansa ta ajiye abincin, sannan ta tsiyaya masa kunun a yar, tazuba masa ido tana kallansa
Abincin yafara ci cikin nutsuwa, yana ci acikin ransa yana masha Allah
Yanaci dazaran yadago kansa saisu hada ido itadashi, kamar wasa taji yace "meyasa bazakici abincin ba?"
Tace no banjin yunwa yanzu saide zuwa jimawa
Bakinta yake kalla yanda take motsa shi, Dan qanqani dashi
Dayawa yaci abincin, yature sauran, dasaurin ta ta janyo flate din tace haba Yaya daddy dubafa saura Dan kadan ka cinye, please daure ka qarasa kaji?

Tafadi hakan da sigar rarrashi
Jiya yi wani Abu ya tsirgo masa tun daga kansa har zuwa tafin kafarsa
Babu musu yadauki spoon din zai qarasa abincin, tayi sauri ta dora Hannunta Akan nasa tace barshi nabaka,
Debo abincin tayi ta nufi bakinsa dashi , tanaji jikinta yana taba nasa, saida ta qara matso wa jikinsa da niyya take goga masa nashanunta ajikinsa
Ahankali yabude bakinsa tazuba masa abincin, tana cewa yauuuwa, Bakinta dab danashi kamar zatai kissing dinsa
Haka ta dinga bashi yana ci, harya qare, sannan yadauki kunun ayar ya shanye duka na cup din data zuba masa, ya kalleta da wani irin yanayi atare dashi muryar ashaqe yace to naqoshi
Cikin shagwaba tace Kai Yaya Dan Allah, ba kasha wannan dinbafa, ta nuna masa Lemon kwakwar, yace "Aina koshi"
Tace a a gaskya, tsaya kaji, sau daya kawai zakasha, ta tsiyayo Lemon kwakwar takai masa bakinsa
Kadan yadansha, ta kalleshi tace Yaya daddy da dadi ko?

Jijjiga kansa yayi, alamun eh
Aikuwa tabashi yakafa Kai saida ya shanye tass
Sannan yace naqoshi
Kallanta yayi yace kamar naji Ana buga gate Dan leqa ta window
Zuciyar ta daya tatafi wajan windon
Batasan wayo yayi Mataba
Yana ganin tashinta ya kalli wandon jikinsa, kamar zaiyi kuka yace nashiga uku, meyake shirin faruwa da nine?

Aguje yatashi yayi sama, yana tsoron karta juyo taga halin dayake ciki, yana zuwa Dakin yashige toilet
Amal kuwa tana waigowa zata fada masa babu kowa, taga bayanan, da mamaki tabishi Dakin sa, tana shiga Dakin taji Motsin ruwa a toilet
Bakinta ta rufe da hannunta saboda Kar dariyar datake ta futo fili, tace waya fada Maka barno gabas take, tajuya takai kwanukan abincin kitchen ta wuce daki ta shirya ta kwanta bacci
*** *** ***
Washe gari tunda tayi sallar asuba Bata koma bacci ba, Bayan tayi karatun alqur'ani da kazimi Tafita ta gyara gidan, gida yadau qamshi kamar ba gobe, kitchen ta nufa tahada musu breakfast, madara ta dama tayi musu kunun madara da kwakwa, sai fruit salad, da wainar semolina
Daki tashiga tayi wanka, tasaka Riga da sket qanana, sket din iyakarsa gwiwa, sai rigar yar qarama daga sama kana iya hango kirjinta, daga qasa kuma bata gama rufe mata cibiyarta ba, Ana ganin shafaffan cikinta
Gashin kanta tasaki ko daure shi batayiba taje falo tana jiran futowar daddy
Shiru shiru har goma ta wuce bai futo ba, Dan haka ta tashi taje Dakin, ganinsa tayi yana kwance yana bacci, tsayawa tayi tana kallan tsantsar kyau irin na daddy, cikin ranta tace ya Allah Kasa mutumin nan ya Soni kamar ba gobe
Gyaran Dakin tayi, sannan tashiga toilet ta wanke Tasa turaren wuta, tafuto, tana sakawa Dakin ma taga yayi juyi yaja fillon dake gefensa ya rungume shi
Shikuma mafarkin ta yake, gatanan tana kwance ajikinsa zata tashi yaqara rungume ta, Amma Kuma yakasa yimata magana
Qamshin turaren wutar dayaji ne ya farkar dashi, ahankali yabude idonsa, dede lokacin Amal tajuyo, idanunsu suka sarqe dana juna
Ido yazuba mata yakasa janyewa, meyasa nake Abu ne kamar wani wawa cikin kwanakin nan?

Duk a saboda ke
Murmushi tasakar masa tace Yaya daddy Ina kwana?

Yace "lafiya"
Yatashi yashige toilet din
Tana mopping Dakin yafuto daga toilet daure da towel a'iya qugunsa, duk jikinsa awaje, kallansa tayi akaro nafarko ahaka, Dasauri ta janye idanunta daga kallansa, gashi ne dayawa a kwance akirjinsa
Gabanta yana faduwa, tadau ko masa kayansa ta ajiye Akan gadon, takasa hada ido dashi, Shima ya lura da firgicin datake ciki, Dan haka ya matso kusa da ita sosai daga Bayanta, yadan rankwafa dede tsawon ta, yakai bakinsa saitin kunnanta
Cikin aji da nutsuwa yace "kingama aikin, kokuma in temaka miki?"
Maganar ce tazo mata wani iri, shi dinne zai taimaka mata?

Tab Lalle in hakane aikinta na kyau
Dasauri tace a a...

Nagode, saika futo, tayi wuf tafi ce daga Dakin
Yabita da kallan murmushi
Juyawa yayi wajan mirror ya kalli kansa yanda yake murmushin
Afili yace meyake damunane?

Wannan yanayin da nakeji ko Akan salma banji Shiba
Shiryawa yayi cikin sauri, yafuto qasa
Yauma tare suka ci abinci, kowa yana satar kallan dan'uwansa dasun hada ido kowa saiya kawar dakai
Suna gamawa Takoma kujera ta zauna, Shima daki yashiga yabaje takardu zai fara aiki, kawai kuma saiya fasa yadawo falon Shima, hannun sa ta kalla taga takardu da wannan jakar dayazo da ita
Zama yayi anesa da ita kadan, ita tana kallo shikuma yana aiki, yana cike takardu yana satar kallan ta, ita kuwa Bata sani Bama
Yaya daddy Dan Allah Dan aramin wayarka, dago kansa yayi ya kalleta, Babu musu ya miqa mata wayar, tana amsa number ta tasaka aciki takira, Kiran na shigowa Wayarta tayi saving number sa
Sannan ta dauki number momy, data Shahida da Abba, already tanada ta anty mufy
Bashi wayar tayi, tace gashinan nagode, ina zuwa, ta tashi tashige dakinta
Yana ganin shigarta yadauki wayar Tata, yaduba wayarsa yaga number ta tasaka aciki tayi kira
Sake Kiran wayar Tata yayi, yazubawa wayar ido ganin
"my d"
Yafuto barobaro Akan screen din wayar, me kenan?

My daddy?

My darling?

My dear?

Motsin ta yaji yayi sauri ya ajiye wayar ya sun kunyar dakansa kamar bashiba
Akwatin daya shigo da ita jiya yatura mata Gabanta, kallan mamaki tabishi dashi tace na menene Yaya daddy?

Kai tsaye yace kudinki ne
Tace kudi kuma?

Girgiza kansa yayi yace haqqinki ne amatsayin ki na matar gorvnor, bakida banki shiyasa nakawo Miki duka
Mamaki ne yakamata, ita Amal itace da wannan kudin?

Dagowa tayi cikin murmushi da Jin dadi tace nagode Yaya daddy
Yace bani ne nabaki ba, wannan haqqin government ne
Tace nasani but babu abinda zanyi dashi, kayi amfani dashi wajan ciyar da yara yan primary abinci duk ranar juma'ah
Kallanta yayi da tsananin mamaki, wacce irin yarinya ce wannan?

Kafin yayi magana ta nuna masa wata takarda acikin takardun gabansa tace Yaya daddy wannan ta menene?

Cikin mamakinta yace, sunayen dalibai ne dazamu tura qasar waje domin su qaro karatu
Daria tasaki tace eh gaskya ka kyauta Allah yatemaka yatayaka riqo
Yace amin, idansa akanta
Awannan Rana haka suka wuni cikin nishadi, haka tasashi a gaba taita tambayar sa abubuwa Akan mulkin su yana fada Mata
*** *** ***
After one week
Yana zaune a office dinsa, yayi Nisa cikin tunanin ta,
"Yaya daddy oyoyo, nayi missing dinka "
Maganar tace take masa yawo acikin kunnuwansa
deputynsa yazo yakawo masa wasu takardu yace ranka ya dade!

Ranka yadade!!

Ranka yadade!!!

Yafada da Dan karfi
Firgigit yayi yadawo daga duniyar tunanin daya tafi
Yace ranka yadade wannan takardun hajiya ne, angama hada komai harma anfara rabawa yaran kamar yanda tabada umarni, sauran kudin kuma suna cikin account dinta kamar yanda kace abude asaka, inyaso duk Bayan wata saita dinga turowa
Ajiyar zuciya yasauke Yakalleshi yace yanzu na wata nawa aka dauka?

Rissinawa yayi yace andau na wata shida
Na Rabin shekara kenan?

Eh ranka ya dade na Rabin shekara, daddy yace ok zaka iya tafiya
Yana fita wayar daddy tadau qara yana dubawa yaga momy ce, tace yazo gida shahida ba lafiya
Dasauri yatashi yace ganinan zuwa momy
Lokacin dayaje gidan harta samu bacci, yadubi momy yace momy Wai jikinne?

Cikin jimami tace shine daddy, shahida tacika tunani Akan Yaron nan dan'uwan Amal, nace ta rage tunani Amma taqi ji, kuma nace abbanku yayi wa mahaifinsu magana yace a a
Jinjina kansa yayi yace Allah yasawaqe insha Allah komai zaizo qarshe
Momy tace to Allah yasa
Yace bari naje gida zuwa dare zan dawo insha Allah kafin nan tafarka
Tace to daddy nah
*** *** ***
Karfe tara yashigo gidan, yana zuwa yafada kan kujerar falo yacire hularsa yayi wulli da ita, Sumar kansa ya hargitsa, Wai wannan Yaron meyake ji dashi ne zai kama yakashe masa qanwar sa?
Chapter 22 · 0% Book details