Sashe 19
Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qasafa kace, uhum wallahi bazan iya kwana a qasaba, saboda ban sababa, jikina ciwo zaimin
Tajuya masa baya tayi kwanciyar ta
Kallanta yake da mamaki, wato kenan de yanzu yarinyar nan tana nufin shine yasaba kwana aqasa ko
Zagayawa yayi ta daya gefenta yadauki fillon gefenta ya wullar aqasa, yadawo yasa hannun sa Akan fillon datake kwance, yajanye fillon, jikake qum
Yabugawa Amal kanta ajikin gadon
Da sauri ta tashi zaune tace Kai Kai Kai
Tana shafa inda ta bige, yau nashiga uku Daren Hana bacci yazo
Kallanta yake sosai, yakasa Hana qwayar idonsa kallan abinda take muradi
Cikin karfin Hali yace "ki iya bakinki"
Kuma still yakasa dauke ido akanta
Harararsa tayi afakaice, aranta tace wallahi gaskiyar Yaya Shahid
Miqewa tayi, tabude kayanta ta dauko jarkar maganin da umma ta aiko mata, takafa Kai tasha sosai
Duk abinda take yana Kallanta afakaice
Tana gama Sha tajuyo tana cewa irin wannan kallan haka ai saida neman tsari
Yace "me kikace?"
Tace a a magana nake da kaina, tahaye kan gadon ta kwanta tare da rufe ilahirin jikinta
Ajiyar zuciya yasauke,yace tashi ki kawomin abinci, dago kanta tayi ta nuna masa abincin tace gashi can acan ai
Shima yace nagani
Tana zunbura baki ta tashi takai masa abincin Takoma gado, yana ganin ta kwanta yasake cewa
Bani takarda acikin jakata
Kafin ta motsa saida tadafe kanta da Hannunta, tace Yaya daddy, Amma bacci nake fa
Kallanta yayi bece mata komai ba, ta tashi ta dauko masa, Takoma gadon zata kwanta tace akwai wani Abu kuma?
Girgiza mata Kai yayi yana Kallanta, tana ganin haka tajuya tasake addu'ah ta kwanta
Iska ya firzar daga bakinsa, shi kansa yarasa gane kansa, yarasa meyasa yake sakata wannan aikin
To Amma meyasa zata lullube jikinta?
Amal kuwa tana komawa gadon bacci ya dauke ta
Shima abincin yaja Dan dole yaci kadan, ko kula takardar data bashi be yiba
Tajera fillon daya dauko agadon yadauko blanket ya shimfida aqasa, yatakure ya kwanta anan
*** *** ***
Alerm ne yatashe su dede lokacin sallar asuba, atare suka farka, Amal ta tashi tana murtsike idonta, tare da hamma saboda baccin be ishetaba
Daddy yana farkawa yaji bayansa ya amsa, Dasauri yakai hannun sa wajan, yaji wajan yariqe, saboda kwana a'inda bai sababa
Dakyar yatashi yashiga toilet, yayi wanka tare da alwala, yana futowa itama tashiga tadauro alwala, tanata kallansa aranta tace wanka da wannan asubar kona menene oho
Yana sallah tana binsa abaya har suka idar, tana gama lazimi Takoma ta kwanta, shikuma yadauko alqur'ani yana karantawa, tana daga kan gadon ta zuba masa ido tana kallansa
Gashinan mutum har mutum Amma ba shida mutuncin kirki
Runtse idonta tayi, Takoma bacci
Shima yana gama karatun, yayi oder abinci yaci, yafita, be zame ko'Inaba Sai Chemist
Maganin ciwon jiki ya karba, yasha, yajefa sauran a aljihunsa, daga nan ya wuce yawon sa ko inda Amal take bai nemaba
Amal kuwa Sai wajan karfe goma ta farka, tayi wanka tashirya cikin atamfa dinkin Riga da zani, Wayarta ta dauka,zata kira su umma Amma Kuma batada Sim card din qasar
Dole Sai hakura tayi ta kwanta
Baidawoba Sai yamma, yana shigowa Dakin tayi masa barka da zuwa
Agajarce ya amsa da "yauwa"
Wanka yashiga, yafuto sanye da jallabiya ajikinsa
Tashi tayi Takoma wajan window tana kallan waje, harya gama shirya
Yadauko takardunsa yafara aiki
Ahankali tace Yaya daddy
Batare daya kalleta ba yace "inajinki"
Dama Dan Allah Dan kiramin anty mufy kaji
Kallanta yayi batare dayace mata komai ba yadau wayar yamiqa mata
Da murmushi afuskar ta, ta karba ta duba Wayarta tadau number takira
Tana shiga anty mufy ta daga, Amal tace anty Ina yini
Muryar wa nakeji kamar masu tafiya honeymoon?
Batasan lokacin datasa daria ba tace a a anty duba lafiyar Yaya daddy mukazo, mufy tace haka de kukace, kawai kuce kun tafi soyaiyarku
Amal ce ta kawar zan can da fadin anty ya junior?
Yana Nan lafiya Amal, inji de babu abinda Dan rigimar nan yake miki ko?
A a anty babu komai, Toshiknn ku kula da kanku bye bye, to anty bye
Tana kashe wayar memakon tabashi saitasa number umma suka gaisa itada baba, sannan takira maisah
Maisah tace Amal wannan layin fa, tace kede bari layin Yaya daddy ne, maisah tace inyee kice komai yazama normal anriga da anwuce wajan?
Ajiyar zuciya ta sauke tace kede bari qawata saina dawo kawai, maisah tace Toshiknn Amal, suna sallama saita kira Shahid, yana dagawa tace Yayanah yakake yagida?
Takardar hannun sa ya ajiye, tsam yatashi yanufeta, batare da yayi Mata magana ba, yamiqa mata hannun sa
Hannun nasa tabi da kallo, alama yayi da kansa ma'ana tabashi wayarsa, idanunta cikin nasa, tabashi wayar
Yana karba yakashe wayar yace "ba kudin banza gareniba dazaki dinga mutane shashakai dashi"
Lalle ma Yaya Shahid dinne shashasha?
Tafadi haka aranta
Daukar Wayarta tayi afili tace yaqi taho shashashar wayata, ni Ina sanki, haka yanmata da qannan wasu suna rububinki
Kallanta yayi, yazo dab da ita yace maimaita abinda kikace
Cikin takaici da bacin rai itama tace cewa nayi qannan wasu na rububinki
Yace ita wayar Taki?
Tace nifa bada Kai nake ba, fuskar sa yakawo dab da Tata, ya nunata da yatsa yace idan kika kuskura kika sake kiramin wannan Yaron acikin wayata saina zaneki
Hannunsa takama zata janye takasa
Nikam yayanah ba yaro bane
Cikin bacin rai yace ok, to waye Yaron?
Kinsan de inda salma na nan toda tuni na haifeki ko?
Haushi ne yakamata, Jin sunan daya ambata cikin faduwar gaba da bacin rai tace Dan Allah Nika matsa
"bazan matsa ba, kisanar Dani waye yaro?
"
Abinda yace kenan
Kokarin matsawa tafarayi, shiko ko gizau be yiba, tana yunqurawa zata tashi ya damqi hannun ta yafizgota dab dashi har sunajin hucin numfashin juna
Idanu suka zubawa juna,nadan wani lokaci, itace tafara janye idanunta acikin nasa
Ta qwace jikinta, Shima yasake ruqota, da karbi ta fizge jikinta, Garin yaruqo hannun tane, saita zame, hannun sa bai sauka ako'inaba Sai Akan nashanunta, yanda yayi niyyar kaiwa Hannunta kyakykyawar damqa aka samu akasi haka yayi musu, wani irin laushi yaji
Atare suka zaro idanunsu
Cikin sauri yasaketa tare dayin baya
Itama Dasauri Takoma kan gadon tare da juya baya, Shima wajan takardunsa ya koma, shiru Dakin yayi, kamar ba yanzu ne suke hayaniyaba
Daddy shiru, Amal shiru
Cikin ransa yace shikkenan najawa kaina raini awajan yarinyar nan, da wanne ido zan kalleta?
Itama anata bangaren cewa take nashiga uku, abinda bai taba faruwa daniba, nida Bayan Yaya Shahid babu Wanda nake hada jiki dashi
Amma Yaya daddy....
Innalillahi
Runtse idonta tayi, kamar mai bacci, Awannan Rana har dare yayi suka kwanta basu sake yarda sun hada idoba
Hakane yayita kasancewa atsakanin su har tsawon sati daya, yau da dare yayi, cikin sauri yadauki wayarsa yahau kan gado ya kwanta
Amal tana ganinsa batace komai ba, saida tazo kwanciya, ta tsaya akansa tace Yaya daddy zan kwanta, qasan Dakin ya nuna mata, yace ga wajenan, nahanaki kwanciya ne?
Kallan qasan Dakin tayi, taja fillo tadau bargo tayi shinfida ta kwanta, Dan ita Kam tadena musu dashi, Kar abinda yafi na rannan yasake faruwa
Yana Kallanta, harta yi bacci sannan Shima yayi bacci
Da asuba Bayan sunyi sallah da Gari yayi haske yatashi zai koma gado ya kwanta, yaga Amal tana mammatsa Hannunta, alamun ciwo yake mata
Maganin daya siyo rannan yatashi yadauko ya wulla mata, yahaye gadon yamiqe
Maganin ta kalla, ta kalleshi, shi ko tausayin ta ma bazai jiba?
Kodan yata iya tunda itace tafara
Maganin tasha ta kwanta, sai wajan shadaya nasafe suka farka, shine yarigata tashi, yashirya cikin qananun kaya, baqin wando baqar Riga mai adon ja agaban rigar, saikuma takalmi baqi Shima
Sumar sa tasha gyara, yayi kyau na qarshe
Amal tana ganinsa zai fice aranta tace wallahi nadena Zaman gadi, Dan haka tace, Yaya daddy Nima zani
Kallanta yayi, sannan yace ba Kiyi wanka ba, baki shirya ba tayaya zan tsaya ki batamin lokaci?
Cikin shagwabar da ita kanta tayi mamakin kanta, tace Yaya daddy yanzu fa zan shirya
Kafada yadaga, yanufi kayansa yana fesa turare
Cikin sauri ta dauki towel, ko kayan jikinta Bata cire ba ta nufi toilet
Kallanta yayi, yace minti goma
Dasauri tace to
Tashige toilet din
Zama yayi a bakin gadon Dakin yana kallan wayarsa
Ajima ya kalli agogo ajima yasake kallah
Amal naciki tana Cuda jikinta, ko rabi Bata yiba, taji yace "minti shida"
Sauri taqara Sawa, tagama Cuda jikinta kenan taji yace "minti tara"
Batayi wata wataba, ta sheqa ruwan taja towel tadaura tafuto
Gaba daya iyakar towel din Rabin cinyarta
Yanajin Bude kofar toilet ya kalli wajan
Idanunsa ne suka sauka Akan santala santalan fararen cinyoyinta, yazuba musu wani irin Mayan kallo, yakasa dauke idonsa akansu
Ita kuwa batasan ma yanayiba, tana sauri ta shirya karya tafi yabarta
Agabansa tayi komai, tashirya cikin doguwar Riga, tayi Rolling, tajuyo tace masa nagama
Dago kansa yayi ya kalleta, sannan yatashi yayi gaba
Yaya daddy
Takirashi
Yajuyo be ce mata komai ba
Tace meyasami idonka yayi ja?
Kai tsaye yace Mata ciwo yake
Da kallan mamaki tabishi, ciwon ido alokaci daya haka?
Allah kenan me iko
Suna fita basu zarce ko'Inaba Sai wajan shan iska, Amal anata waige ta kalli nan ta kalli can
Wato kenan shi yawon sa yake fita yabarta a hotel a kulle
Wallahi ta dena yarda yafita, yabarta
Suna shiga wajan, sai yan tsirarun mutane awajan, kowa yana harkar gabansa
Wajan zama yanema yazauna, itama haka ta zauna agefensa, tana kallansa tana murmushi
Kallan qarin bayani yayi Mata
Babu wata alamar tsoro atare da ita, tace "kayan sunyi ma kyau Yaya daddy, idan muka koma nigeria kadinga saka qananun kaya"
Eh Lalle Sai yau yasake tabbatar da yarintar wannan yarinyar, in banda yarinta tayaya yana matsayin babban mutum a'idon jama'ah kuma governor zai dau qananun kaya yasaka?
Shiyasa fa wasu ayyukan daya kamata ace itace zatayi baya kulata yabata, Dan yasan cewa lokaci daya zata lalata komai
Ai saide yasa suit kokuma manyan kaya,Dan haka ya share ta kawai
Tasake cewa kaji?