← Book details Burinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 39

Sashe 3

Burinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mijin ta taje tasanarwa Ana sallama dashi, yana fita, yameqawa Malam hamani hannu, Badan yasan darajar amsa gaisuwaba da bazai meqa masa hannun ba
Suna gaisawa yace ba zama yakawoniba, Malam lado kajawa danka nura kunne karya kuskura yaqara taba yarmu
Kullum bashida burin daya wuce yadauki hannu yadaki Amal, Akan acuci maza, to yarmu Bata cutar maza saide su cuceta, kafada masa haka kawai
Malam lado yace aransa yace ikon Allah yau kuma tijarar akaina ta sauka
Afili yace masa Toshiknn, za'a kiyaye insha Allah
Baba hamani baice masa komaiba yakada binjimar sa yayi gaba
*** *** ***
11:30 am A dutse international Airport jirgin su yayi landing
Kai tsaye government house suka wuce shida jama'ar sa
Suka gaisa da governor of jigawa state, inda suka samu tarba mai kyau, sai Bayan sun huta ne, aka hadasu damanyan motoci guda uku qirar Benz, dukansu glass dinsu tinted ne, basu Bata lokaci ba suka dau hanyar maigatari
*** *** ***
Oya Bude bakin
Babu musu tabude Bakinta, yacigaba da bata abincin
Sake debowa yayi a spoon din yanufo bakinta, kawar da kanta tayi tace Yaya please naqoshi
No banyarda ba yarinya, oya Bude
Haka yadinga dura mata abinci, agogon hannun ta ta kalla mai sauqin kudi, tace Yaya lokaci yaja, karna makara islamiya, zuba mata shanyaiyun idanunsa yayi, yayi qasa da murya yace ni bazan samu abani ba kenan?

Yanda yayi maganar cikin sigar dabata saba ganiba hakan ne yasa ta kalleshi cikin sauri
Danya kawar da tunanin ta yasa Shima cikin sauri yace shikkenan to, tunda bazan samuba
Amal tace to Yayanah karka damu nida kaina zan baka dinner saikace kakoshi
Promise?

I promise Yayanah
Dahaka ta tashi cikin sauri ta zumbula qaton hijabin islamiyar ta, gabanta yana faduwa tana darurar haduwarta da Malam nura, ko yau Yaya zasu qare?

Saurin datake ne yasa tariqe niqab dinta ahannu
Tana futowa kofar gida tayi turus ganin wasu manya manyan motoci a kofar gidansu
Gawasu mutane sunci baqaqen suit kowa yasa baqin Glass alamar ba mutunci
Motar tsakiya taga sun nufi sun Bude kofar ta, aikuwa wani babban mutum yafuto
Da ita yafara tozali, ganin kallan datake musu ne yasa yace yarinya zo mana
Ahankali cikin nutsuwarta taqarasa har inda yake ta rissina tare da fadin Ina wuni?

Fuskarsa dauke da murmushi yace lafiya Lau
Nan ne gidan Malam hamani danda?

Yafadi haka yana mai Nuni da gidansu tace eh nan ne
Yace yauwa maza jekice yayi baqi
Dayake akwai kofar shiga ta waje, tanan tashiga aikuwa yana zaune yanajin radio
Tana fada masa yace tashiga gida ta dauko musu ruwa
Tana kawo musu ruwan, tagansu harya shigo dasu cikin falon, ss din suna tsaye, maigirma Abdallah ne kawai a zaune
Ruwan nazuba musu, Babu alamar qyanqyami yadauka yasha
Baba ne yace Amal jeki dauki wancan qwan kiyi addu'ar samun qaruwa ajiki ki kawomin
Ajiye jakar makarantar tayi tare da niqab din yadauki qwan Takoma gefe tafara rubutun da tawada cikin nutsuwa
Maigirma Abdallah ya kalli baba hamani da mamaki aransa yace yanzu wannan qanqanuwar yarinyar ce zatayi wannan aikin?

Baba hamani kamar yasan abinda yake tunani yace masa alhaji karka damu
Yaron wajanki zai haihu
Um karka damu, zai haihu da yardar Allah
Tana gama rubutun ta maiqowa baba hamani qwan
Tace baba natafi islamiya yace Amal
Tajuyo yace daura niqabin naki mana
Murmushi tasaki tace to baba
Tsayawa tayi tadaura tafice, gabanta yana faduwa saboda makarar datayi da kuma shakkar haduwarta da Malam nura
Abba yana zaune yana kallan ikon Allah, sai yaji sun birgeshi da alama mutumin akwai tarbiya agidansa
Baba hamani ya katse masa tunani da fadin to gashi alhaji
Wannan qwan guda daya ka ganshi?

Abba yace eh
Yace to afasashi asoya, abawa Yaron da matarsa sucinye
Abba yace duka su biyun qwai daya?

Baba hamani yace alhaji muna baka kana Qin karba
Inbakaso tashi jeka
Abba yace a a muna so ya karba yayi godia
Yace nawane kudin maganin?

Baba hamani yace dubu hudu, Amma nama ragi kakawo dubu biyu
Abba yace to mungode, yadauko bandir din kudi guda biyu,har dubu Dari biyu
Yace to gashi mungode
Baba hamani yadauka yacire dubu biyunsa yace jeka da kudinka mu Bama karbar cin hanci irin naku yan nigeria
Abba Abdallah yayi murmushi yace to nabawa yata Amal kyauta
Murmushi baba hamani yayi yace to Amal tana godia alhaji, za'a Bata
Daganan su maigirma Abdallah sukai godia tare da sallama suka tafi
Mrs Usman ce
BURINAH
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Ahankali take tafiya kamar yanda tasaba cikin nutsuwa, da zumbulelen hijabinta
Tana shiga harabar makarantar taga malamansu maza awaje, gabanta ne yayi mugun faduwa lokacin datayi ido biyu da Malam nura ta cikin niqabinta
Har qasa ta tsugunna ta gaidasu Amma abinda yabata mamaki shine yanda ko maganar makara babu Wanda yayi Mata acikinsu
Tana qarasawa ajin, ta zauna kusa maisah, kallan ta tayi tace Kai Amal yau kin makara dayawa, Bayan kinsan halin Malam nura bashida 'm'
Wlh Rumaisa baba ne yasani aiki
Shiyasa nayi latti, maisah tace Ayya, aikuwa aikin iyaye shine gaba Akan komai
Safna abdulrashid daya daga cikin daliban tace Amal, ashe jiya baban ku yaje har gida yayiwa Malam nura kashedi Akan kinayin acuci maza
Yuuuuu kallo yadawo kan Amal, cikin mamaki tace baba kokuma Yaya Shahid?

Ni ban fadawa kowaba Sai yayanah
Safna cikin sanjin gulma tace um aikuwa ya kyauta Dan yayi mana maganin wulaqancin Malam nura
Kafin inyi magana shugaban makarantar yashigo tare da wasu daga cikin malamai cikinsu kuwa harda Malam nura, idonsa qur akaina
Dana lura ni yake kallo saina sunkuyar da kaina
Ba'a dauki tsawon lokaci mai tsawo ba, shugaban makarantar ya shaida mana cewa kowa yaqara dagewa yayi gyaran karatun sa dakyau saboda Ana gab dayi mana bikin sauka
*** *** ***
Wai alhaji kunsha hanya, sannunku
Tafadi haka yayinda take kokarin cire masa malun malun din jikinsa
Abba yace ai hajiya tafiyar akwai Nisa, Wai ahakan ma danma ba'a Mota mukaje ba, Amma tsakanin Garin da inda muka sauka tafiyar akwai yawa, gashi hanyar tasu tana buqatar gyara
Momy juwairah tace to sannunku alhaji muje kayi wanka kahuta, kafin ya miqe yace ga wannan
Kallan hannun nasa tayi tace alhaji qwan menene wannan?

Yace shine abinda muka Sha wannan baqar wahalar akansa
Yace suci shida matarsa, da iznin Allah za'a samu abinda ake so, momy ta dinga juya qwan tace ikon Allah
To Bari gobe Sai akai musu, daga mata hannu yayi yace haba hajiya, kirasu yanzu kisa masu aiki su dafa suci su tafi
Nizan shiga ciki in watsa ruwa in kwanta
Babu abinda zan musu ayanxu alhaji Sai Bayan munje nayiwa mijina hidima tukunna
Da murmushi ya kalleta, itade akoda yaushe cikin kula dashi take, Bata nuna gajiyar ta Akan hakan, Koda yaushe tana cikin kwalliya da kalamai masu dadi ga mijinta
*** *** ***
Amal gashi inji Malam nura yace nabaki, takardar hannun ta na kalla nadafe kirjina da hannun na, tace nashiga uku maisah ko takardar korata ne daga makaranta?

Nashiga mezan cewa baba
Nafadi haka idonta na cikowa da qwallah
Takardar ta fizge zata Bude ta karanta, maisah ta dakatar da ita da fadin a a karki Bude a gabana idan kinje gida kin nutsu saiki karanta idan munsake haduwa saiki ban labari, Amma ki kwantar da hankalin ki, insha Allah Babu matsala
Ajiyar zuciya nasauke nace to maisah, nagode qawata ta Gari
Hararata tayi tace ni muje, baquwar haure kawai, qilama zuwa kikai ki zautar mana damalami
Ku dama yan agadaz dinnan haka kuke, da anganku shikkenan nutsuwar bawa tatafi
To yar qasa, munji, kuma babu inda zamu, kullum Ina fada miki damagaram kina kaini agadaz
Tace edin can zan kaiki, Gaba nayi nace kanki akeji
Takusa qarasawa gidansu kawai sai ganin mutum tayi agabanta, subhanallah
Haba Yaya sham, wallahi kaban tsoro
To yakike so inyi tauraruwata?

Koda yaushe bamuda ikon yin magana agida saide aboye?

Kinga Amal wallahi nagaji, sanki yana neman zautar Dani, kibani dama inturo iyayena gidanku ayi magana
Yaya sham, kasan de banda ikon yin hakan ayanxu ko?

Meyasa Amal?

Yafadi hakan kamar zaiyi kuka
Tace saboda yayanah yahanani sauraron kowa, sannan Yaya sham yanzu Ina tulawa bamuyi saukaba, tayaya kake tunanin zanje wa da baba wannan maganar?

Kallanta yayi da mamaki yace Amal Anya kuwa kina sona kamar yanda nake sonki?

Yaya sham trust me wallahi I really love you
Amma kabani dama zuwa Bayan saukarmu, insha Allah zan gabatar dakai awajan baba, nasan cewa baba yana sona, zaiso abinda nakeso
Yauwa kokefa, to yanzu Sai yaushe?

Very soon zamu hadu karka damu kaji Yaya sham din Amal
Murmushi yasaki Dan yaji dadin sunan sosai
Yace shikkenan bye bye
Dahaka suka rabu
*** *** ***
Salma banaso, please kibani fillo nah
Gwalo tayi masa tace ow nahanashi kazo ka qwace, in kacika mai karfi, kokuma duk wannan dantsan kawai na adone?

Kallanta yayi, shide yasan idan yace karfi zai sa mata to da tuni ya qwace
Fillon ta sake dauka ta wulla masa, Shima yadauka yarama, sunata nishadi abin su, ta jefo masa Shima yarama, tace ko yanzu de nasa kadan motsa bakinka, haba mutum ya zauna shiru haka
Kallanta yake da tsadaddan murmushinsa mai kashe mata gabban jiki, yace aikuwa mai ganin surutu na, sai sabuwar amaryata
Nan da nan ta dauki fillon ta jefeshi dashi tace Allah a a, baka isaba
Yana kokarin ramawa, momy ta futo da filet ahannunta
Nan da nan suka nutsu gaba dayansu
Salma ta sauka qasa cikin sauri tace momy barka da futowa
Ba yabo ba fallasa ta amsa da "yauwa"
Shima ya gaida ta,ta meqo musu filet din tace gashinan kuci
Daddy ne yakarbi filet din, ganin wainar yar kadan ce yasa shi maiqawa salma
Tome zaici meze Bata anan?

Salma tayi bissmilla tafara ci
Kallansa tayi babu alamar wasa afuskarta tace Kai karaam bazakaci bane?
Chapter 3 · 0% Book details