← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 31

Sashe 9

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gadan gadan ya nufeta har ya sa hannu zai shako wuyanta sai ya fasa yayi wani shegen murmushi.

You what alhamdulillah na godewa Allah da ban debi sauran turawa na kai gidana ba.

Wallahi ban kasance mazinaci ba na sani Allah ba zai hadani da mazinaciya ba.

Ba abinda zan miki kije Allah kika yiwa laifi bani ba dan dai da da aurena na kamaki haka wallahil azim ba abinda zai hanani bindigeku.

Ki manta kin taba sanin wani Ridwan a rayuwar,ina nan ina kokarin Ganin na mallakeki ashe ke kina nan kina mallakawa wasu jikinki toh ba dani ba.

Ya juyo ya fita ya barta kaman an dasata a wajen.

Kwananshi biyu a garin ya kamo hanya ya dawo direct wajen aiki ya wuce.

Shi kam sha'anin mata ya tsorata shi shuraihat kenan da ba wani kyaun kirki ne da ita ba tana bin maza.

Ina ga wancan aljanar yarinya na tabbata ko bata bisu ba su zasu bita.

Da kuwa na ci ubansu ya fada a fili.

Shi yanzu ya zai ne ma lokaci kara tafiya yake buqatata kara qaruwa yake.

Shuraihat din da nake tunanin zan aura ko bata tare ba zan dinga sauke buqatata akanta ga yanda ya kasance.

Wata zuciyar tace mishi ba ga mata an aura maka ba.

No no no no haba ta ina zan fara tunkarar aljanar nan da buqatata salon ta rainani.

Hade giranshi yayi yana tunanin mafita.

Fans sai ku sama mishi mafita😝😜

SAWWAMA QAWWAMA

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 15.

Yau kam na tashi zuciyata wasai saboda na riki al Qur'ani da sallahn dare harkokina kawai nake yi har wata yar kiba nayi.

Yau su yusra ne suka zo min yini aiko munsha hira sai sakalcinmu muke yi.

Mu dafa wannan mu kwaba wancan mu jika wancan mu dai sha'anin mu kawai muke yi ba mai kwaban mu.

Fareeda ce tana kwaba iloka tace kai gidan kai akwai dadi anya nima ba auran nan zanyi ba.

Duk muka sa dariya Halima tace kayi son ranka ba mai hanaka in ka dama ka kwana da yunwa ba ruwan wani.

Mussaman ma in mijin matafiyi ne irin su yah rid,ai ba karamin haushin hanamu tayaki kwana da yah rid da momy suka yi ba ta fadi hakan tana kallona.

Farida tace toh ai sanin halinmu in mun hadu ya sa aka hanamu.

Yusra tace yau kuma sai mun fanshe ba muka sa dariya ni dai binsu kawai nake da ido ina murmushi dan wani dadi nake ji ina tare da yan uwana.

Karan bude gate da shigowan motoci muka ji dukkanmu zaro ido muka yi a tare muka furta Allah yasa ba yah Rid bane..

Da gudu muka nufi window din palo ai kuwa shine da sojoji sun kai takwas.

Da sauri muka fara tattare palon muna jera pillows din kujerun sai dibi dibi muke yi.

Murda kofan da akayi aka shigo ne ya samu tsayawa da abinda muke yi.

Duk munyi cirko cirko da kaganmu ka ga rashin gaskiya.

Kallon mu yayi daya bayan daya ya hade rai ya kalli yusra yace ku dan ubanku bana ce kar kuzo min gida ba uwar kuka zo yi??

Duk muka yi tsuru tsuru dan ubanku ba da ku nake yi ba ya daka mana wani uban tsawa.

Da sauri Halima tace mamah ce fa tace muzo mu duba zakiyya ya take.

Da kuka zo kunga an yanyankata? Shegu munafukai kawai.

Ke kuma.mayya uwar me kika gaya musu ya juyo kaina yana tambayata.

Cikin in ina da rawar murya kaina na kasa nace ba komi.

Yace atoh dan ni dai iya sanina ba abinda na miki a gidan nan in ma suna tunanin yanka ki nake yi.

Ni ba a zo dubani ko ba da aka hadani da aljana sai ke yahi kwafa ya wuce daki.

Muna cikin sauke ajiyan zuciya ya kwala min kira abin dariya duk sai muka firgice.

Da sauri na isa dakinshi ina adduan Allah yasa ba wani abu ya gani ba dai dai ba dan ko da safen nan na karkade dakin.

Ina shiga ya wurga min harara kasa kasa naji yace mayya kawai gyaran murya yayi yace malama abinci zaki dafa min yanzu.

Sannan ki dafa na kimanin mutun goma kuma dan tare nake da mutane.

Nace toh har na tashi zan fita yace zo nan na sallameki ne rankwashi ya kafa min me shegen zafi.

Yace nace miki na gama ne ko na gaya miki abincin da zaki dafa min.

Nayi shiru idona na kawo ruwa.

Yarinya ai baki yi hawaye ba tunda kika sake kika auri Ridwan.

Ni tuwon alkama zaki min su kuma sauran sakwara kina jina SAKWARA nace ya fadi haka yana zare ido shi kanshi ya san ya hada ni da aiki.

Nace toh sannan ya sallameni na fita a kitchen na sami su farida suna tattare shirmenmu.

Ni wallahi har na manta wai sunzo da sauri suka karaso wurina.

Halima ce ta cire hannuna dake bisa kaina dan har lokacin ina dafe da inda ya rankwasheni.

Yusra tace hala ya rankwasheki? Hawayena ne suka basu ansa.

Lallashina suka yi sannan na basu labarin yanda muka yi.

Kut yah kasheki yake so yayi ya tsufar dake da wuri wadancan kartin yake so ya saki yi musu girki da dare ya mukurkusheki da rana ya saki bauta tab.
Cewar yusra

Hararenta nayi nace ya mukurkushe wa?

Dukkansu suka dauka laaaaaahhhh haba biri yayi kama da mutum.

Ni dai ban ce musu komi na fara aikina su ma suka hannu nan da nan muka gama sakwaran ma na leda muka tuka suka tayani muka gyara gidan tsaf.

Dakina muka shiga muka zube a gado farida ce ta dan dago tace zakiyya kin san me duk abin da yah Rid yake miki kina da laifi.

Tashi nayi zaune ina kallonta da mamaki laifin me kuwa?

Tace good tana mikewa zaune suma sauran suka mike dan sun san halinta akwai lecture

Laifinki shine baki dauki shawara ko daya da muka baki ba na tabbata kin cigaba da yawo a cikin hijabi kaman yanda kika saba.

Ina ji su auntu shema da aunty rabi suka baki shawarwari bana jin kinyi amfani da ko daya.

Ke bari kiji so nake ki fighting abu biyu ki kwato yancinki a cikin gidan nan su abba basu muku aure danku rabu wata rana ba.

So kiyi kokarin dai daita gidan auranki.

Numfashi na sauke na ce me zan fighting hajiya farida murmushi tayi tana karkada ido.

Halima ta daka mata duka tace shegiya uwar mata zata fara manyancen.

Hmmm so nake ki fighting TSORO da KUNYA bance ki zama mara kunya ba kunya ai ado ne akwai inda zai miki amfani amma ba yanzu ba.

Na san ba yanda za ayi tashi daya ki cire tsoron yahRid a ranki nuna mishi kawai zaki yi ba tsoron amma bai san yana nan cike pal a ranki ba.

Kunya kuma ajiyeshi zaki yi ki daina yawo da hijabi ko manyan kaya a gidanki ga dinkuna an miki fitinannu ga uban english wears da aunty rabi ta jibga miki.

Rikitashi da halittun da Allah ya miki yake kushewa show him what he is missing out ki dinga fishar hankalinshi ki kuma dinga nunawa kaman ba danshi kika yi ba kina yi ne on ur own.

Daura towel dai dai cinya ki fito wanka ki nufi kitchen a guje kaman kin daura abu kina tsoron kar ya kone in kin tabbatar yana palo.

Saka riga mai budadden kirji kije bashi ruwa ko wani abu..........

Haka suka hadu suka ta ban shawara suka sassaka ni groups na whatsapp.

Suna shirin tafiya ya leko dakin ya korashi wai sun cika mishi kunne da hayaniya shi hutu yazo ba jin hayaniyarsu ba.

Ajiyan zuciya na sauke tare da kudurta niyyan zanyi amfani da shawarwarin da suka bani in gani.

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 16

Bayan tafiyansu farida yah Rid ya kirani ya fada min ga nan sojoji ya kawo biyu zasuyi gadin gate in zan fita zan fita da biyu sannan biyu masu tsabtace compound din gidan da zuwa aika.

Shi duk a tashi hikimar in ya kewayeni da yaranshi bazan bi maza ba ya manta yaran nashi maza ne yazo ya cika gida da maza a hikimarsa ta hana yaduwar zina bai san in mazinaciyarce ba a cikin yaranshi ma sai ta ci amanarsa.

Washegari da safe bayan na gama gyare gyare na da girke girke dan yace har suma ni zan dinga musu girki dan bakin mugunta.

Na fito wanka ina daure da towel ya banko kofar ya shigo naga alaman rashin sallama a inda nake al adarsa ce dan baya sona da zaman lafiya balle ya nema min.

Dan kura min ido yayi sai kuma ya kau da kai yana hadiye yawu😜 na gane hakan ne ganin yanda Adams apple dinshi ke sama yana kasa.

Dakewa yayi ya min magana cikin sarkewan murya duk yanda ya so ya kaurara murya abin ya faskara muryarshi sai da ta nuna halin da yake ciki.

Ki shirya zamuje cikin gida abinda ya furta kenan yayi hanyan waje karo na farko kenan da ya min magana ba da tsawa muna mu biyun mu.

Da gangan nayi kaman santsin tiles zai ka dani na dan sake towel dina yayi kasa na tallafe rabin nonona suka bayyana

Wayyo shine abinda na furta a kidime, da sauri ya juyo a lokacin na dafe dressing mirror gesture din da nayi ya sa towel din kaina kuncewa gashina ya zubo ya rufe idona.

Rintse ido yayi tare da dan kama gabanshi saboda yanda yaji ya harba tashi daya.

Cikin sassarfa ya bar dakin tun kafin zuciyarshi ta sashi aikata abinda zai zo yaji kunya.

Bai taba tunanin yarinyan ta mallaki diri haka ba dan shi yawancin lokuta a cikin zumbula zumbulan riguna yake ganinta ga shegen sa hijab.

Shegiyar yarinya ga kyan fuska ga na jiki a fili ya furta ALJANA kawai wallahi bazan bari ta rikita min lisafi ba.

Duk laifinane da ban knocking kofan ba kafin in shiga da ban ga abinda zai dameni ba.
Chapter 9 · 0% Book details