← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 31

Sashe 6

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kadan mamaki bai kasheni ba me ke damun kwakwalwan yah Rid? Abba na hango zai shiga motarsa nan na gano dalilin kulawar.

Har abban zai shiga motarsa sai ya fito ya dan kwankwasa glass din side din ya rid.

Bala'i nan naga munafurcin namiji sai ya wani nuna alamun firgita da sauri ya sake habana yayi saurin sauke glass din.

Abba ne yace ridwan mai ke faruwa ne naga zakiyya na kuka ba dai wani abu ka mata ba?

Dan sosa kanshi yayi yace abba wallahi wai ba ta da lafiya ne shine zan kaita hospital shine fa take kuka wai ita bata son allura.

Ashsha sannu zakiyya ai gwara kuje asibitin ai zama da ciwo ba dadi kuyi maza ku tafi, Allah ya sauwake ameen.

Ya ja motar muka kama hanyan hospital ina mamakin shu'umancin yah rid Allah ka fitar dani.

Mun danyi nisa kadan duk inda muka wuce ana kallonmu gefen titi yayi parking yace fitar min a mota.

Dammm gabana ya ba da nace ki fitar min a mota ko malama ki koma baya danni bazan dinga tafiya dake ana bina da kallo ba haba kowa sai ya jinjina min daukan aljana a motata.

A hankali na sauka na koma baya(abin dariya in bai dauki aljana ba ai ya zama driver din aljana🤣🤣)

A haka muka isa asibitin aka min test aka ban magani dan mugunta sai cewa yayi a min allura,duk tsoron allura na haka na daure aka min hawayene kawai yake zubo min.

Haka muka kara dawowa ina bayan mota sai da muka kusan isa gida yasa na dawo gaba.

Lokacin da muka shiga gate yana waya da sauri na fita a motar da naga hankalinshi ba ya kaina nayi cikin gida da sauri.

Ina shiga na sami su fadeela sun zo wani mugun kallo na ga tana bina da shi ni dai bance wa kowa komi ba naje na hau gadona na kwanta.

Fareeda ce tace hmm hajiya zakiyya ko aunty zakiyya zance ya jikin

Da sauki na fada a takaice.

Banko kofarmu aka yi ya shigo ya wula min ledan magunguna na yace ba dai kin mai dani sa'anki ba zanci ubanki ne.

Ya fice wani shewa naji fadeela ta sa tace ah dadinta ba isa a mana fi'ili ba duk kyaun mutum bashi da farin jini a wani wajen.

Dukkanmu bawanda ya kulata,haka ta gama hargaginta ta fice ko meye hujjanta oho.

Haka yah rid ya gama hutunshi kullum shi yake kaini makarantan boko ya kaini islamiya kuma ba ranan Allahn da ba zai ci ubana ba.

Ni kuma gyaran part dinshi da girkinsa ni nake yi haka zai lissafo min abinci kala kala kuma yace sai nayi.

Su mama sai murna suke ya sakko ya rumgumi zabinsu,su yusra ma har an canza min suna daga matan yah rid ko auntynmu.

Ni kadai na san azabtuwar da nake a hannunshi tun ma wai ba a daura mana aure an barni daga ni sai shi ba kenan.

Dan mugunta haka zai labta min under wear dinshi yace in wanke a toilet wani sa'in har da kayansa ga washing machine ga komi amma haka zai sani wanki in dauraye in ajiye a toilet din.

Da zai koma mamah tace sam sai dai ya kira daya daga cikin sojojinshi ya ajiye 407 din shi a dinga kaini school a ciki.

Sunkuyar da kai yayi yace haba mama kina son bata yarinyan nan ta cigaba da bin motan gida mana in ina nan ba sai in kai ta ba.

Ah ah sam ni ban yarda ba sojojin nan dai an baka su a wajen aikinka ka dau daya ka bata yana mata hidima kuma ka sa a bude mata acct kasa mata kudi dan ka san yanzu bambancinta da matarka kadan ne.

Haka yana ji yana gani ya mata dukkan abin da mama ta zayyano yana kudurta irin ci mata uwa da zai yi dan yayi alqawarin mutuqar aka bata mishi akanta sai ya mata ninkinsa.......

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 10.

Nan da nan na dawo big gal duk inda zani da driver na ga kudi da mama ke sani kashewa ta canza min mai da su turare.

Tuni kyauna ya kara fitowa da haskena gashina kam har wani sulbi ya kara yi.

Wajen koyan kwalliya mama ta min register tasa aka kawo min make up kit na 50,000 haba ai sai su yusra suka ce suma sai an musu register.

Tasa aka musu make up kit kuma tace su tambayi yayansu ai ba wacce ta iya sai yah sadiq suka tambaya yace zai sayawa mutum biyu na 20 20 thousand in yaso ya ibrahim ya sayawa sauran biyun haka ko akayi.

Sai kumbure kumbure suke yi wai nawa yafi girma da kaya momy tace toh ai ni amarya ce.

Fadila kam ai kaman ta hadiyeni sai habaice habaice take jefana da shi wai na zo zan mallake musu dangi da asirin mu na fulani.

In banda rashin hankali na bafulatanin kauye ina ke ina yah rid yar kauyan kayayau da ke.

Halima tace wai ke fadila meye matsalarki ne meye naki dan ta auri yah rid iyayenmu sun ga dacewan hakane amma duk in bi dagawa mutane hankali.

Dalla banza mara kishin dan uwa tsakani da Allah in auran hadi ake so ayi da wa yafi dacewa a hada yaya gani ga farida amma a rasa da wanda aka yi tunanin hada shi da ita sai BARE yar karo.

Farida tace ah ah ni kam ba ruwana da yah rid ba iyawa zanyi da shi ba macece wacce ta kai mace ma ya rid na wulakantata balle ni.

Ji banza ke din ba mace bace duk wani halitta na ya' mace kina da shi toh meye ya rage yanzu dan Allah wannan facakar da take ti da kudi da ba daya daga cikinmu ce take yi ba.

Ohoooo sai yanzu na gane inda kika dosa fadeela cewar halima amma kin bani kunya kice hassada ce kawai kike yiwa zakiyya sai yanzu na gane tun farko me yasa kike jin haushin zakiyya ashe bakin cikin kyan da Allah yayi mata kike yi yanzu kuma da Allah ya bata namiji daya tamkar dubu nan ma baki kyaleta ba kina mata bakin ciki.

Wallahi kin bani mamaki da kunya ai iyayenmu sun san da ke suka ga zakiyyar ce tafi dacewa da su ba zakiyya zaki zo kiyiwa tijara ba iyayenmu zaki je ki sama ki gaya musu abinda ya dace dan su suka hada ba zakiyya ba yanda yah Ridwan yake ikrarin bai sonta itama ai ba soshi take ba ita da take da asset din da namijin aure sai ta zaba ko da kuwa shugaban kasa ne balle wani yah rid.

Mtsw taja tsaki ta fita ganin duk cikin yan uwanta ma ba wanda ya goya mata baya.

Farida ta juyo inda nake kwance ina kuka tace ke kuma mara aikin yi ki zauna kawai kina zubar da hawayanki a banza indai kika ce wannan halin naki zaki cigaba da yi fadila ta samu daman rainaki kenan koshi ya rid kamata yayi ki nuna mishi kema fa macece.

Yusra tace wallahi kuwa shi yana wani ikrarin bai son mace me kyau ba ayi auran bane yarinya ajiye kunyanki da sanyinki zaki yi ci mishi uwa sannan ki dauka ki mayar.

Kwashewa suka yi da dariya dukkansu halima tace wallahi yusra gaskiya ta fada tun yaushe zata saito shi kan hanya shi ba namiji bane lafiyayye sai dai inshi dutse ne.

Duk shegen girman kan nan zai ajiyeshi sai yanda kika yi da shi tayi kwafa tace Allah maza ba karamin bani haushi suke ba.

Farida tace wallahi kuwa raini ne dasu mussaman gamu teenagers ganinmu suke yara shatab wanda basu san komi ba.

Yusra tace nan ko in muka sa su a daki sai yanda muka yi dasu. Shewa suka yi suka tafa nace Allah ya shiryeku amin suka amsa da karfi.

Karatun jarabawa muke sosai bama samun zama tun safe in muka tafi school sai hudu da sauri muke shiryawa zuwa islamiya saboda hadda muke shida kuma mun wuce wajen kwalliya sai takwas kuma.

Duk zirga zirgan da muke yi ni a motar yah rid ake kaini su kuma a motar gida in tajin haushi su da yawa suna hirarsu ko ban samu su baki ba ai da dadi kana cikin mutane.

In na yi musu korafi sai su ce min ai ni matar manya ce wane su hada hanya da matar soja.

Ko a makaranta wani respect ake bani daga dalibai har malamai ganin me uniform ke dawainiya dani.

Su kam har sun fara dana sanin shiga make uo classes din da suka yi suka ce dama sun bari sai anyi final exams tunda su ba amare bane.

Momy da mamah suka ce basu isa ba ai gulmar da yasa suka ce sai sun shiga toh sai sun karasa.

Ana saura sati mu fara jarabawa mama tace min ya rid zai dawo tuni naji kaman in gudu wani abin mamaki kuma da al amarina sai na tsinci kaina da son ganin shi.

Lallai bani da hankali ganinshi na dai dai da gani bacin raina dan tabbas na san watan cin ubana ya kama.

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 11.

Ranan da zai dawo wayan mama ya kira yace ta bani dan bai taba kirana ba asalima bai da number na.

Cikin faduwar gaba na amshi wayan mama ta fita.

Sallama nayi cikin sanyina amin kawai yace sannan yace ke kina jina na san kin sami labarin zan dawo yau toh ki fara shiryawa kanki dan kam tabbas kin san ba zan miki da sauki yanda kika sa aka rabani da farin ciki da kwanciyar hankalina toh kema haka zan miki koma fiye da haka.

Tuni hawaye suka cika min ido ina kokarin mai da su.

Kina ji ko nace uhmmm yace good yanzu ina so kiyi min fried noodles,salad sai tuwon alkama da oha soup sai zobo and any other home made drink ki min shirme wallahi ki gani.

Da sauri cikin rawar murya nace yah ban iya oha soup din ba.
Chapter 6 · 0% Book details