← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 31

Sashe 16

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

He never wanted to hurt her ya san dole zata zarge shi amma ai ta san ba a musu aure dan su zubawa juna ido ba an musu aure dan ansan yana da buqatar mace kuma iyayensu sun ga ita ta dace da rayuwarshi.

Yeah ita ta dace da rayuwarshi dan kam shi yaji me yaji ko baya sonta ai zai zauna da ita ya debi gara😜shi raini ne bai so kuma ta dauko hanyan raina shi ta bar ganin taga gadon kwananshi ubanta zai ci ai ta san halinshi ai ta san baya raga mata.

Shi weak point din shi daya yanzu ba zai ce yana sonta ba amma ya daina jin tsanarta sai dai yana tsananin kishinta musamman yanzu da ya dandana zumarta yana kishin wani ya kalle mishi ita balle har ya raya wani abu a ranshi.

Mikewa yayi ya nufi dakinta a hankali ya tura kofan tana kife har lokacin tana kuka.

Sauke ajiyan zuciya yayi ya karasa shiru yayi ya rasa ta inda zai fara mata.

Ina jin shigowarshi nayi banza da shi kaman ban san d ruwanshi ba.

Am sorry da sauri na jiyo ba tare da zuciyata tayi shawara dani ba ta bada umarnin haka.

Limshe ido yayi ya daga min kai yes i am sorry i hit you i never meant to ke kika hasala ni kin sani bana son raini and ke kuma kina so ki fara abinda ba halinki.

Kwantawa nayi ina kallonshi yana magana mamaki yake ban tuban muzuru ne ko me.

Zakiyyatu mu gyara auran mu mu zauna like every other ma'aurata bana son raini ki kiyayye wannan we cant continue like this we have to iron things out ko ba ma son juna mu kiyayye juna mu zauna lafiya kinji.

Gyada mishi kai kawai nayi dan ni mamaki yake bani namiji bashi da kunya shi dai akan wannan wajen basu da dama mutsike ido suke yi.

Thanks for understanding yace tare da mikewa ya fita bai yi gigin taba ta balle ta fassara shi.

Yana fita na janyo wayata na danna kiran fareeda

Bawoni abin da ta fara fada kenan tana dauka tsaki naja nace sallaman kenan bawoni toh sai ki nemi beyeraban da zaki yiwa.

Dariya tayi tace kilode wani tsakin na kuma ja nace ban son rashin mutunci fa ke shawara nake nema.

Gyara murya tayi ta dawo serious tace toh ina jinki madam matar soja soja.

Kwashe komi nayi na gaya mata.

Ausubillah nace jin ta zabga wata uwar ashar ta dora da fadin ke banza ce wallahi kin ba da mata kin bashi a arha baki gwara kan shege ba.

Wallahi ke kam kyan ne kawai ba wayo da dabara kaman ba mace ba.

Nace naji ke dan ba ke bace wallahi wani abun u cannot resist them.

Resist them my ass ba daurewa ake ba kema din wallahi jarababbiya ce daman kadan kike jira anyway yanzu tunda ya kawo kanshi yana neman shiriya ki yarda a shirya amma mind you kar ki kara bashi a arha make him beg ki sashi ya kneeling sai ya rokeki.

Dariya nayi jin yanda take wani dagewa kaman wata uwata.

Au dariya ma na baki ko wato ga mahaukaciya toh wallahi kar ki kara tunkaroni da matsalarki.

Sorry sorry kawata wallahi tausayawa mijinki kawai nake naga yayanki ma baki bari balle wani.

Hmmm yar uwa ba zaki gane bane mazan ne abin tsoro zuma da wuta ake cinsu ga zaki ga harbi ke dai Allah ya shige mana gaba kawai.

Ameen my dear ya mutan gidan ne ya fadeela ko dan hi din nan ni in na kirata bata ma dauka.

Tsaki ta ja tace fita batunta ni ban san yaushe fadila ta canza ba ni sai nake ganin kaman an sake min yar uwa da wata mai son zuciya da hassada i really miss my old twin wannan wata ce daban.

Cikin tausayawa nace sai addua shi kawai za mu dinga mata Allah ya shiryemu baki daya.

Ameen kuyi ku dawo mun missing dinki wallahi

Bani bace ai yah rid din ne sai a slow.

No p ki saito mana shi bye tun dazu mami ta sani aiki sai mun hadu a watsapp.

Bayan na ajiye wayan ne na fada kogin tunani gaskiya nayi sake da na bari ya rid ya min shigan sauri amma ai wannan ma wani makami ne tunda gashi yana kusonto kanshi dani.

Murmushi nayi yanzu na dandana mishi zuma kuma na janye..........

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 29.

Normal zaman mu ya koma zanyi mishi duk wani abu da na saba dama ko da ya hakeni ban daina ba.

Da yamma zamu je driving lessons dinmu amma dare nayi zan sidade dakina in kulle.

Shi kam abin nan ya ishe shi wai ace kana da mata ga buqata yayi ma yawa amma ka rasa nayi shi kam yau zai maganu kuma zai aikatu.

Da yake yau weekend tunda ya fita da asuba bai dawo ba sai wajen 11am wanka yayi saboda exercise da suka sha.

Ina kwance lokacin ina karatu a wayata ya shigo dakin tashi zaune nayi ina gaisheshi.

I wouldn't mind a hug ya fadi haka yana tsareni da ido murmushi nayi na dan yamutsa fuskan wasa nace nah till you take a bath u sting na karasa ina rufe baki.

Kallon kanshi yayi yana murmushi ganin yanda zufa ya wankeshi shikenan ai tunda sai an min wulakanci bari in je inyi wankan.

Dariya nayi sosai ganin yanda yake abu kalan tausayi shima murmushi yayi ya tashi ya fita yana jin dadin ya sata farin ciki.

Komawa nayi na kwanta tare da rufe ido Allah ka bani ikon daidaito matsalarmu kar ka sa in ba da kai da wuri dan sonshi da tausayinshi na tasiri a kaina.

Mikewa nayi dan inje in fitar mishi da breakfask palo na kai na jera mishi kafin na koma kitchen din ina dudduba abinda bamu da shi in gaya mishi.

Store din na gyara dan naga ya danyi kura kamshin turarenshi ne ya sanar dani zuwan shi.

Yana tsaye a tsakiyan kicin din yayi wanka yasa blue jeans da farin riga ya zube hannunshi a aljuhu.

Aiki kike haka nace uhmm breakfast din na palo muje in serving dinka.

No dont mind cigaba da aikinki in kin gama ki shirya muje kiga gari.

Cikin murna nace toh yah murmushi yayi ya juya ya fita ni har mamaki nake ashe yana da yawan murmushi .

Da sauri na karasa aikin nace na kimtsa palon na dawo na samu har ya gama yana kishingide.

Yah Ridwan na gama dago kai yayi ya kalleni lokaci guda kuma ya hade rai.

Wai me yasa ku mata kuke da problem ne wai yanzu a haka zaki fita.

You guys think in kun yi aure kun sami daman yin yanda kuka so saboda ba kwa gaban iyaye.

Which ba haka bane wasu abubuwa ne suka kara hawa kanka dole ku dinga kara kiyayewa.

Sunkuyar da kai nayi ina murza hannuna nace yah toh ai gown din is loose bai kamani ba kuma gyalen da girma.

Yace you see what i am telling u wai gyalen da girma zamanin zaman ki a gida ban taba ganin kin fita ba hijab ba sai yanzu ko toh wallahi in kin san in kin shiga school irin dressing din da zaki dinga yi kenan then forget about that.

Da sauri nace ah ah yah na daina na juya da sauri naje na dauko hijab wai kuma dan rashin kunya sai ya kankantar da murya yana wani kashe ido how about that hug.

Ido na waro yayi dariya kasa kasa ya hade jikinmu waje daya tare da hada goshinmu ganin yana kokarin hada bakinmu yasa na zare jikina a hankali nayi waje murmushi yayi yana shafa kanshi kafin ya biyo bayana

Gidan abokananshi muka je yana nuna musu ni wai matarshi abin dariya daga nan muka fita a barrack din yace min sai in mun dawo zamu gidan oganshi.

Parks parks muka je ya zagaya dani roller costa ya sa muka hau ai da na sauka kaman zan yi amai abinka da bafulatana shi kam sai dariya yake haka ya rikoni zuwa mota.

Daga nan shopping muka je sannan mu ka wuce gidan oganshi babban mutum ne dan yana da manyan yara yarbawa ne.

Karba matarshi tayi min sosai nan muka ci abinci da zamu tafi 50k ya bani matarshi ta bani turarruka da kayan bacci

Sai bayan magrib muka tafi gida.

Da muka isa maimakon mu shiga sai yayi parking ya kulle motan kawai.

Kallonshi nayi da alamun tambaya ya wani sake jiki Yana min wani irin kallo kau da kai nayi gefe kawai.

Kirjina na dukan tara tara sa hannu yayi ya janyoni jikinshi yana shinshinani kokarin kwace jikina nake amma ba dama hijab dina ya zare yana bin wuyana da light kisses har ya hauro bakina.

Kokarin kwacewa nake amma na kasa sai ma kokarin kwantar da sit dina da yake yi ganin haka ai na fashe mishi da kuka.

Sakeni yayi ya koma da baya ya jingina tare da rufe idonshi.

Kuka na cigaba da yi ba tare da ya bude ido ba ya unlocking kofan yace min ki shiga ciki.

Ganin ya zaro taba yasa na fice da sauri na bude gidan na shiga ina mamakin yanda bana jin warinta a tare dashi ni har mantawa nake yana shanta.

Shi kam sai da ya busa son ranshi ya tafi masallaci sallan isha.

Bai shigo gidan ba har sai da na fara bacci naji mutum na shafani yana cusa kanshi cikin rigata.

Har na fara dauke wuta nayi saurin dawo hankali na na fara tureshi ina kuka.

Mirginawa gefe yayi ya kwanta rub da ciki kukan na cigaba da yi.

Murya a cushe yace menene kuma ba na kyaleki ba?

Nace toh ni ka fita zanyi bacci.

Juyowa yayi yana fuskantana yace kiyi baccinki ba abinda zan miki i cant force myself on you da zan iya da tuni nayi sai dai kiji tsoron Allah kar ki cutar dani

A hankali ya tashi ya fita yana layi sai naji kaman in bishi wasu hawaye masu suka zubo min.
Chapter 16 · 0% Book details