← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 31

Sashe 4

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki ya dan ja ya shafa kanshi yace ku bazu gane bane kwata kwata tun lokacin da na fara ganin yarinyan nan wallahi naji tsananta ni a lokacin ma na zata yan zuwa bikinka ne dan a lokacin bikin naka na ganta.

Ban kara ganinta ba shi yasa na manta ta toh amma mai take yi A gidan nan me hadinmu da ita??

Ibrahim ne ya kwashe zuwana gidan ya fada musu kasancewar sameer shima ku san dan gidan ne.

Sameer yace ayya gata da hankali yanzu ai ta kusan gamawa ma.

Ai gwara tayi ta gama ta bar mana gida dan wallahi haka kawai ban son ganinta bata burgeni tun bata kai haka ba kyau kaman wata aljana irinsu sai shegen fi'ili da girman kai da iyayi su ba kowa ba.

Yah ibarahim ya dan girgiza kau yace ba dai zakiyya ba yarinyan da bata taba iya hada ido da mutum magana ma bai dameta ba da wuya ka ganta a cikin mutane ni ba zan so yarinyan nan ta bar zuriyarmu ba.

Cikin kuluwa Ya Ridwan yace toh ai sai ka aureta kaje ka hadata da shema da kuwa na bar shiga gidanka har abada.

Dariya yah ibrahim da yah sameer suka yi kafin yah ibrahim yace ai dan dai na riga nayi auran ne da na aureta sai dai ga sadeeq ko da yake gaka nan ma babban gwaza kaki kayi aure ya fada hakan cike da zolaya.

Naushi ya kai mishi ya kauce yana dariya yace ah ah oga sir ba soja bane bazaka illatawa matata ni ba gwara kai babban gauro ne.

Sameer ma dariya yake yace ai ya kusa ya tashi daga gauron duk zamu fita gauron mu huta da shegen iyayinka da anyi magana kace matata to kowa ma dai zai yi matan nan.

Bar dan iska ya rasa wace zai hadani da ita sai mai idon mayun can bayan ni ina da mata first class me zanyi da kalan lalura ai ni mai iya daukan buqatuna sai shuhaira.

Rike baki yah ibrahim yayi yace oh su shuhaira manya wato har ka gama sanin zata iya daukan buqatunka ko dai har ka fara sauke mata buqatun ne.

Sameer dai dariya yake yace wallahi ni kam nayi nan bazaku kashe ni da dramanku ba ya shiga mota ya tafi.

Shi kuma yah Rid ya fuskanci ya ibrahim rannan a hade yace ai dai ka san ni ba dan iska bane tunda sanin kanka ni asali ma mace bata gabana balle in nemi inyi lalata da ita ba shuraihan.ma ganin kamun kanta da yanda take sona yasa nake sauraranta kuma na san dole za a zo a matsa min da batun aure.

Yah ibrahim yace dole mana za a matsa maka da batun aure tunda kai ba waliyi bane yanzu fa ka haura 35 ai gwara ka san me kake ciki.

Sauke ajiyan zuciya yayi yace kai dai bari kawai bro Allah kadai ya san dauriyan da nake yi shi yasa Na yanke shawaran in an kwana biyu zan sami daddy da maganan shuraihat din in shi bai fara min maganan ba.......

Nima sawwama nace da rabon ko zai yi maka shigar sauri😜

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 6 .

Tunda ya rid ya dawo ya sani a gaba sai dai in hanya bai hada mu ba yanzu zai zageni ya hada min har da rankwashi dan gwanine wajen rankwashi.

Yau lahadi na tashi da wani matsanancin ciwon ciki kasancewar ina cikin period dina ko da yamma tayi su yusra sai tafiya islamiya suka yi suka barni dan dama in har na fara period zuwa school kuma sai Allah.

Ni kadaice a gidan duk antafi islamiya su mama ma sun tafi sunan amaryan matan abokin abba.

Ina kwance a dakin mama dan in dinga jin masu shigowa duk da akwai masu aiki murkususu nake tayi ni kadai.

Sallamanshi naji a palo da kamshin turarensa sai warin tabar tuni zuciyata ta fara tashi saboda jin warin abin da natsana ga kuma ciwo .

Da sauri na tashi dan in shiga bayan gida saboda wani amai da ya taso min shi kuma dai dai nan ya shigo.

Carab ya ruko hannuna yace ke dan ubanki dan kin gan ni ne zaki tashi ki gudu wato ga dodo ko? Ni da ke waye abin gudu ke masu kalar aljanu ma ba a gudu miki ba amma har kina iya gudun ma wasu.

Toshe bakina da hancina nayi a lokaci daya ina girgiza kai ina kuma kokarin warce hannu na dan at any moment na kan iya yin aman saboda tabar da ke daya hannunshi

Ke ni kike toshewa hanci? Kut amma kin rai..... Maganan shi ce ta yanke a lokacin da na wanke mishi ciki da amai.

Kam bura uba abin da ya furta kenan ya sake ni ya wanke ni da mari kafin in dawo hayyacina ya kara min wani ya sa kafa ya kwasheni na fadi kasa

Ban iya cewa komi ba sai wayyo yayah kayi hakuri bani da lafiyane ba gudunka nake ba dan Allah kayi hakuri na hada hannayena biyu ina hawaye.

Wallahi banda ina gudun kasheki wallahi yau da sai na lahira ya fiki jin dadi ina ruwana da rashin lafiyarki a kyamace ya cire rigarsa ya wurga min afuska yace kuma wallahi na baki 30 mins ki wanke min rigata ki goge kuma ba a washing machine ba dan ubanki shegiya mayya ya juya ya fita.

Da kyar na Mike tsaye ai sai tsantsin aman ya kuma kayar dani wani dan marayan kuka na saka ina tausayin kaina.

Haka na lalaba na tashi na gyara wajen na cire kayana na hada da rigarshi na wanke.

Ina jin ciwon cikin nan ina komi haka na fito nayi ta yarfe rigar nan sai da na tabbatar zata iya goguwa na je na fara gogewa ina yi ina duba agogo duk na hada zufa.

Cikin sassarfa da tsoro na shiga side dinshi waya yake yi da alama da budurwarsa ce dan sai wani zuba shagwaba yake yi ko kunya baiji ba katoto da shi yana ya wani abu kaman yaro.

Tabe baki nayi in raina yayi dubu ya baci kura mishi ido nayi yana sanye da 3kwata na kamu (khaki)a jikinshi sai farar riga mai dan guntun hannu ya kama mishi jiki dan kana ganin zanen abs dinshi yanda jikinshi yake amurde.

Shi din baki ne mai kyau dogon hancin shi na masifar burgeni balle bakinshi hmmm😋

Idona kan yatsunshi suka dira dogaye dasu gwanin kyau i can't imagine hannunshi working therr magic on me wani lumshe ido nayi ina raya hakan a raina.

Innalillahi astagafurillah na fada tare da saurin zaro idona mai nake yi haka na shiga uku yaushe na fara developing dirty mind ba akan kowa ba ma sai wanda ya fi kowa tsanata a duniyan nan.

Ke naji an daka min tsawa a tsakiyar kaina sai da na zauna daga tsugunan da nake.

Uban me kika tsaya yi kuma wai ke baki san yanda na tsani ganin fuskanki bane wallahi har mafarki nake yi kuma ni tsoro kike bani ki tashi ki fitar min a daki mayya kawai mai suffan aljanu.

Tafiya nayi ina tunanin ya suffan aljannun yake ko ya taba ganine oho shi dai bashi da kalman dangantani da aljanu da mayu dan tsaki naja na shige dakinmu.

Sai magrib duk yan gidan suka dawo da masu suna da masu islamiya.

SAWWAMAN QAWWAMAN😘😎

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 7.

Ridwan zaune gaban iyayenshi maza da hajiya kakarshi kasancewar kakansu namiji ya rasu.

Gyara murya daddy yayi yace Ridwan a matsayinmu na iyayenka baza mu danne maka hakkinka ba muna so ka gaya mana ko kana da wacce kake so dan ka san mun daga maka kafa ba dan kadan ba.

Yanzu shekarunka 34 zuwa da biyar ba aure a matsayinka na lafiyayen namiji ko baka da lafiya ne bamu sani ba?

Ya dan sunkuyar da kai yana murmushi yace ni daddy lafiyata kalau asalima ina da yarinyan da nake so tana karatu ne a Europe shekaran can ta fara dama ina so in muku magana kuje a sami iyayenta duk da babanta yace sai ta gama tukun za ayi auran a cewarta.

Tunda ya fara magana duk suka kura mishi ido ba kaman hajiya da take ji kaman ta tashi ta mangareshi wai tana kasar turai kuma ma sai ta gama.

Tace kai rilwanu wai kai kam yarone da shekara ishirin ko kuwa mtsw ta ja tsaki tayi shiru dan ta san tana iya ci mishi uwa yanzu.

Abba ne yace toh nan da shekara nawa zata gama makarantan?

Kara lankwashe kafa yayi cike da kwarin guiwa ganin abba da kanshi ne ya mishi wannan tambayan yace eh toh nan da shekaru biyu dan ta sami mtsala a shekarar farko.

Abba ya gyada kai yace zuwa lokacin kuma an nada ka shugaban gauraye ko to ba zai yuwu ba ba a zuriyarmu ba.

Hajiya aka gyada kai aka ce tabbas kam ba a zuriyan nan ba rulwanu ba kai bane shugabanmu.

Daddy yace ba zamu hanaka auran zabinka ba amma kam muna da sharadi...... Ya zuba mishi ido.

Shi kam ridwan hadiye wani yawu mai kauri yayi wanda yasa adams apple dinshi yin sama da kasa yana tunanin menene kuma.

Daddy ya cigaba da cewa sharadinmu ba wani mai wuya bane wanda dama ko da ace ita yarinyan da make so din a shirye suke toh muma sai ka bi namu ra'ayin ka auri yarinyan da muka tanada maka tun da dadewa.

Wani gumi ne ya keto mishi aure kuma? Wata yarinya kuma innalillahi.

Abba yace saboda haka tunda su wadan can ba a shirye suke ba sai a fara wannan in yaso ran da suka shirya ka aurota dan ko bamu da wannan nufin baza mu zuba maka ido kana zaune ba aure ba,in ba dai ba wata ta'asar kake aikatawa ba.

Saboda haka ka shirya nan da wata uku kana da mata dan mun riga munje mun sami mahaifinta an tsai da magana suna rubuta jarabawan gama secondary za a yi bikin ku.
Chapter 4 · 0% Book details