← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 31

Sashe 22

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga kafada nayi nace me ko ma mishi ina dariya

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 38.

This page is dedicated to you aunt zuwairat Ene ufedo mi, uwe cene ke du kpayu mi kpayi edo omemele ku ke wu ki deyi uwe my star i so much cherish u and i adore your talent. Ufedo emi lailai

Ana yin sallan magrib ya shigo da masara lokacin muna dakin mamah.

Mama na uwar daka tana sallah dan mu mun yi cikin zumudi na tashi hannu na sa na karbi ledan hannunshi dan tuni kamshin gasashiyar masarar ta ziyarceni.

Ban bi ta kanshi ba na zauna jikina har rawa yake na bude na dau masara daya aiko da zafinta.

Fara ci nayi kaman wace ta wuni da yunwa gaba daya ido suka zuba min tun ba shi ba da ya san ba haka take abu ba.

Su yusra ma mamaki suke yi dan sun san ban wani damu da gasashen masara ba dama dama ma dafafe.

Dan ko zuwan mu hwol dasu haka zasu ta kwarainiyar gasa masara ina kallonsu amma yanzu ci nake kaman an aikoni.

Mama ce ta fito tana fadin zakiyya ai yanzu dai zaki ci abincin tunda kuka iso baki ci komi ba sai coke.

Ridwan ne ya amshe batun da fadin yauwa mama hala ke zaki sa ta ci abincin dan wunin yau gaba daya bata ci komi ba sai gasashen masara.

Mama ce ta juyo inda nake taga yanda nake cin masaran har na cinye daya ina kokarin cin na biyu tace ikon Allah dan tuni ta fara hasashen wani abun.

Dan tun shigowarsu ta zargi haka ganin irin kyau din da ta kara amma sai tayi la'akari da zaman waje daya tunda daman ita mai kyau ce.

Dan ta tabbatar sai tace to kici wani abu mana kafin masaran ko amai zai saki.

Da sauri nace eh wallahi mama dan ko tunanin abincin nayi sai naji zuciyata na tashi shi yasa ma bana bi ta kan abincin.

Masha Allah cewan mama to kuma ba kya sha'awan cin wani abun sai masara.

Shiru nayi ina tunani🤔 can nace yauwa mama sai popcorn.

Kallon juna su yusra suka yi cike da mamaki.

Shi kam dafe kanshi yayi🤦🏽‍♂ dan ganin yanzun ma ba wani abun kirki tace ba wai popcorn.

Yauwa mama da irin dry plantain din nan mama tace toh Ridwan samo mata.

Tsaki yayi yace mama ta tashi mu tafi dan na gaji na siya mata a hanya.

Gaskiya kam kuje ku huta ke zakiyya tashi ku tafi gidan gobe zan shigo ni da doctor Zainab.

Mikewa nayi ina neman gyalena nace mama waye ba lafiya.

Ba kowa zata zo ne ta muku barka da zuwa nace toh.

Sai da ya bi ya jido mun popcorn da dry plaintain muka kama hanyan gida duk a gajiye yake dan shi yake driving ya tura sojojinshi gida.

Muna isa wanka yayi nima da kyar ya dagani daga cin popcorn ya min wanka.

Kwanciya yayi yan kallon yanda nake cin popcorn din ina korawa da coke shi shan coke din ne baya so.

Bacci ya fara daukanshi na tabashi ina fadin mijina zanci plaintain kuma na barshi a parlor kazo ka rakani.

Bacci cike da idonshi ya tashi muka je muka dauko har zai kwanta nace ruwa zan sha kuma babu a fridge din dakin nan.

Nan ma ya mike yana layi dan bacci da gajiyane a tattare da shi ruwan na dauko.

Ya kalleni da lumshashen ido yace shikenan ko akwai wani abun.

Kai na girgiza tare da fadin babu jana yayi yace oya muje please ki kwanta precious dare yayi kuma duk mun gaji.

Kafada na makale nace ni bana jin bacci kai kawai ya gyada min ya kwanta.

Hira na fara mishi tun yana ansawa har yayi shiru bacci ya daukeshi.

Ni kuwa idona ya bushe kyamas ba alaman bacci sai buruntu nake kayanmu na fara jerawa a wardrobe.

Dago kai yayi jin buruntun yayi yawa ga haske da na kunna.

Precious what are you doing karfe biyu fa baki kwanta ba.

Baki na turo nace ni bana jin bacci tashi yayi ya janyoni ya kashe wutan sani yayi a jikinshi yace kwanta baccin zai zo.

Haka na dinga mutsu mutsu sai kusan uku na sami bacci.

Da asuba a daddafe nayi sallah ko doguwar addu a banyi ba na lallaba na kwanta.

Kallon yanda tana kwanciya bacci ya dauketa yayi yace atoh ba dolle ba rigima ya hanaki yin bacci jiya i wonder what is wrong with her.

Karatu ya dan taba shima ya koma gadon ya jawota jikinshi.

Basu suka farka ba sai wajen sha biyu lokacin ma wayarshi ce ta tashesu mama da dr zainab ne suka iso.

Hijab na zira na fito wajen mama kayan tea nayi kokarin kawo musu mama tace ah ah mu ai na rana muke jira yanxu kam dan mun tsufa da karyawa.

Dariya nayi na zauna na gaishesu.

Dr zainab ce ta min yan tambayoyi sannan ta bani wani kwalba naje nayi fitsari na kawo mata suka tafi.

Da yamma ta kaiwa mama test ina da cikin sati 5 murna kaman za tayi yaya...

Ba shiri ta kira ridwan tace yazo albishir ta mishi tare da bashi maganin da dr zainab ta prescribing wa zakiyyan.

Ina kwance bayan na gama cin masara bacci ya daukeni.

Banji shigowanshi ba sai kisses da naji yana showering dina da shi ido na bude ina kallonshi.

Murmushi yayi ya tashi tsaye tare da daga collar din riganshi sama yayi doro yana wani bubbudewa.

Tashi nayi zaune ina kallonshi da mamaki.

Gira ya daga min yace kin gane ko.

Ido na zaro ganin abinda yake yi.

Ya dan ja dogon hancinshi yace yawwa kina ji ni din fa ba na wasa bane na dage na zake dantse tare da baje kwanji nayi noma.

Noma kuma yayi albarka tunda tsirina har ya tsiro a gonata halak malak.

Gira na daga na zuba mishi ido da baki da hanci dan ban gane inda maganar tasa ta dosa ba duk da na san yana cewa ni gonarsa ce to me yake nufi.

Ganin ban fahimceshi ba yasa ya daukeni yana zagaye parlon dani yana fadin precious we are pregnant we are going to be a parent.

Toshe kunne nayi jin yanda yake ihu at the top of his voice ajiyeni yayi ya riko hannuna yana rawa dani irin na turawa.

Ni dai ido na zuba mishi wai ina da ciki ni zakiyya ce ke dauke da ciki kuma wai yah rid shine uban dan Allah buwaye gagara misali wa ya taba zata?🤔

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 39.

AISHA KANYA INA KIKE TARE DA YAYUNA MAMAN SADIQ DA MAMAN MANAL BAN MANTAKI BA HASSANA DANLARABAWA KUNA RAINA ANA MUGUN TARE😘.

Kulawa na mussaman nake samu a wajen wannan zuriyar kowa nan nan yake dani su yusra mamakina suke yanda na shawo kan yah rid a cikin dan kankanin lokaci wai in gaya musu sirrin nace abin sirri ne.

A gaban kowa yah rid nuna min soyayya da kulawa yake wani sa'in har kunya nake ji.

Ranan da muka je gidan daddy motsi kadan zanyi zaice precious ya dai me kike so.

Sai da mami ta gaji tace ridwan yaushe son mace ya mai da kai mara kunya.

Murmushi yayi yana shafa kai yace mami ai ita dince ba lafiya ne ya isheta ba shi yasa.

Dariya tayi tace lallai kuwa manya za a zama uba ai ba zaman lafiya.

Shima dariyar yayi ya kwalawa fadeela kira dan fareeda taje yin online registration na post utme dinta dan bata yi tare da su fadeela ba ko meye dalili oho.

Zuwa tayi tana wani karairaye sai wani yatsina fuska take ni abin har mamaki yake bani dan dai ba haka fadeela take ba da.

Na san ita din mai son kai kanta ce kuma tana da dan rashin kunya amma yanzu abin yayi yawa.

Mussaman a gareni ta mai dani makiyarta ta gaske ban san dalilinta ba su yusra sunce bakin cikin kyau na take.

Abin bai ta'azara ba sai da aka fara maganan auran mu da yah rid ta kara kafa min kahon zuka maganan arziki baya hada mu sai dai harara da tsaki in ko ta min magana toh baka ce ta gaya min.

Kudi ya ciro a gaban aljuhunshi ya mika mata fuskar nan amurtuke dan shi bai son raini yaga alama kuma yarinyan na tashen balagan tsuntsaye yace kije ki siyowa precious masara na ga akwai mai gashi a farkon anguwan nan.

Karba tayi tana tura baki ta daukko gyalenta ta yafa ta fita.

Mami tace Allah ya shiryi fadeela ni dai ban san inda ta dauko mugun halin nan ba,saboda wannan halin ita da yar uwata ba wani shiri suke ba fa.

Kwafa yah rid yayi yace barni da ita ai tara ta nake randa zata shiga hannuna zata gane bata da wayo.

Muna nan zaune ta shigo da dafafen masara yana karba yaga dafafe

Dan ubanki dafafe nace ki siyo?

Yah ai baka fada min wanda zan siyo ba.

Ke kuma kin fi karfin ki tambaya ko toh maza ki mayr ki karbo gasashe.

A fusace ta fita ranta fal tsanan zakiyya wallahi sai ta dau mataki akanta.

Tana fita fareeda ta shigo ihu ta saka ta fado jikina tana murna.

Da hanzari yah rid ya tshi ya dagata yan masifa ke baki da hankalina sai kin ji mata ciwo.

Ido ta zaro tare da rufe bakinta mami tace su hankaline da su Allah dai ya shirya.

Gyada kai fareeda tayi tana dariya ta hade hannunta waje daya tace sorry kawata na missing dinki ne zo muje daki ta miko min hannu na kama ina dariya.

Muna shiga ta daka min duka tace shegiyas naga mutumin yayi ladab

Sosa bayana nayi nace shine zaki zage ki daka min duka ke da yah rid na juya kaman zan fita ta rikoni ke rufa min asiri kar kisa a lillisani a ce zan barar da ciki dan naga rawar kan da yake yi kenan.

Dariya nayi nace a ina kika ji ina da ciki su halima magulmata.
Chapter 22 · 0% Book details