← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 31

Sashe 23

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ruwansu halima shi uban gayyan yayi ta kira yana fadawa mutane muna zaune da mami ya kirata.

Nace lallai kuwa ina zama a bakin gadon.

Kayan jikinta ta fara cirewa ni kuma na dau file din da ta shigo dashi.

Ido na zaro ina kallonta da mamaki nace fareeda wa ya aikeki applying LASU wa zai barki kiyi karatu a wani garin balle lagos.

Daura towel tayi ta zauna a kusa dani tace saboda a can zanyi aure bana so in apply BUK maganan aurena ya tashi a nemi hanani saboda karatu.

Nace aure? Wa zaki aura fahad ya koma aiki lagos ne?

Tsaki taja tace ban son rashin mutunci ni dama na taba ce miki ina son fahad ne ko zan aureshi?

Nace to waye wannan kuma fareeda da sanin su abba kika cike lasu?

Ajiyan zuciya ta sauke tace su daddy basu sani ba asalima wanda nayi dan shi bai san nan apply ba sai yau zan gaya mishi.

Innalillahi ni kam waye wannan da zakiyi abu gaba gadi ba tare da kin yi shawara da kowa ba akanshi?

YAH AUWAL ne zakiyya shine wanda zan iya yin komi saboda shi.

Ban gane yah auwal ba wani yah auwal din?

Yah auwal naki mana shine zakiyya nake soyayya dashi nake fatan ya zama abokin rayuwata.

Rungumeta nayi ina tsanin farin ciki nace amma naji dadi wallahi ke da yah Auwal abin yayi wallahi.

Ni da ina ce yusra ce fa budurwarsa.

Dariya tayi tana hararana tace ba haka bane toh,yusra ce kawai ta san yana sona wai injishi kama kafa yake da ita.

Dariya nayi sai kuma na kalleta nace toh ya zamuyi da su abba kin san dai sai anci ubanki.

Kafada ta daga tace sai me in dai zan kasance da hubbyna bani da case kuma ma yace yayiwa yaya magana yace zai zo cikin satin nan ya sami su abba.

Anya fareeda ba yah auwal ne ya saki cike lagos ba.

Da sauri tace wallahi bai sani ba...

Shiru muka yi da maganan ganin fadeela ta shigo.

Tana wani fisge fisge tace wai ki fito ku tafi ta juya ta fita.

Kallon juna mukayi da fareeda ta tabe baki muka mike muka fito.

Daga gidan ma gidan hajiya muka nufa mun samu tana zaune tana kwadon zogale tuni raina ya biya amma dai na dake.

Bayan mun gaisa ne ta kira mai aikinta tace saude dauko min plate in sawa wannan kishiyar tawa zogale.

Da sauri yah rid yace wata kishiyar taki baza taci ba ita fa ba komi take ci ba atoh.

Kankance idanu tayi tace wallahi rulwanu ka fita idona sai taci ai zogale magani ne zaka zo ka min fi'ili.

Na gaya miki ni ba sunana rulwanu ba in ba zaki iya cewa ridwan ba kiyi shiru da bakinki.

Anki ayi shirun ance rulwanu rulwanu rulwanu kayi abinda zaka yi ta karasa tana zabga mishi harara.

Hade rai yayi yana ta kwafa ba kakkautawa ni kam mai zanyi banda dariya dan kullum draman su daya tana ce mishi rulwanu.

Zogalen ta zuba min tana ajiyewa gabana ya dauke yana fadin haka kawai ba za ki sa min mata amai ba.

Marairaice fuska nayi mace zanci

Kallona yayi da mamaki yace kin tabbata ba zai saki amai ba kuma ina yanzu kika gama cin masararki.

Na kara marairacewa nace ni dai zanci.

Hajiya ta cafe Allah ya miki albarka yar nan kin min maganin dan iyayi ko yaushe ka fara son nata ina ce a nan ka Dinga tijarar baka sonta.

Miko min plate din yayi yana fadin ungo kafin ta min tonan silili ni dai dariya kawai nake yi.

Ba karamin ci nayi ba dan har kari na nema hajiya sai tsiya take mishi bai kulata ba.

Kwance nake ina kallonshi yana ta hada kaya dan saura kwana 2 ya tafi ni kuma wata kasala nake ji shi yasa ban iya tashi na hada mishi ba.

Wayarshi ce tayi ringing ya dauka cike da ladabi dan daddy ne.

Ido na zuba mishi dan na ga wayar kaman na damuwa ne dan tuni ranshi ya baci ina ji yana fadin toh sai ta iso zata gaya min uban da ya aiketa.

Ajiye wayar yayi yana tsaki kallona yayi yace ki duba shegiyar yarinyan nan wai lagos state university ta cike ko gidan uwar wa zata zauna a lagos oho.

Gabana ne ya fadi dan na san yau in fareeda ta shiga hannunshi mai kwatanta sai ya shirya.

Tashi nayj zaune na dan dafa shi nace mijina calm down ba fa wani abu bane wai ita da yah auwal ne fa suje soyayya shine ta cike nan saboda kar tayi aure karatunta ya katse.
Soyayya kuma? Da auwal wani auwal? Auwal naku?

Na gyada kai ina murmushi toh shine baza su fada su bari manya su yanke hukunci ba zasu yi gaban kansu.

Nan dai na kwashe komi na fada mishi har da zuwan yaya.

Shiru yayi ya ciro waya ya kira daddy ya fada mishi.

Daddy yace ba komi tabbas yaya ya kirasu yana zuwa gobe Allah yayi zabin alheri kawai

Yah rid yace ameen daddy sauran ma duk su fito da miji haka nan baza su dinga sa mana ciwon kai ba.

Daddy yace hakan za ayi zanje in samu abbanku muyi magana.

Suka yi sallama rungumeshi nayi ina miahi godiya.

Yace da na miki me baza kayi wa fareeda komi ba ina

Girgiza kai yayi yace ai na rantse sai na taba lafiyarta.

Turo baki nayi nace ni dai ah ah wallahi ko kuma in tayi maka kuka.

Yace baza ayi haka ba ki bari ko rankwashinta inyi dafe kaina nayi dan tuna zafin rankwashinsh, amma gwara rankwashin da duka.

Nace toh shikenan da ta zo kuwa sai da ta sha rankwashi ya fita ya barmu tare.

Murna muka dinga yi.

A daren ranan ne kuma aka kira sauran aka ce kowacce ta fito da miji nan da wata biyu yan banza duk murna suka yi banda fadeela dan ta rasa ta ina zata faro.

Ta duba duk cikin masu sonta ba wanda ya kai yah rid kudi ko kyau da nagarta ba kuma zai yuwu zakiyya ta fita kyau sannan ta auri mijin da yafi nata ba dole sai dai ita ta fita ko su zama daya hakan na nufin sai dai ta auri yah rid kenan😱

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 40.

FADI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU.

Washegari yayah da wasu daga cikin baffaninmu suka zo nemawa yah auwal auran fareeda.

Bayan sun gama abinda ya kawosu yah rid ya kwasosu dan suzo suga gidana tunda yayah bai taba zuwa ba asalima tun baki ba wanda ya kara zuwa.

Sosai suka yi farin cikin ganin muhallina sun san kam Allah ya ban miji daya tamkar dubu.

Sauka na musu sosai suma basu gushe ba sai da suka kara min nasihohi kan zaman aure da hakurin zaman.

Suka nunar min ba a ko da yaushe mutum ke samun abinda yake so ba inyi hakuri da duk halin da zan tsinci kaina.

Allah baya taba barin bawa mumini face sai ya jarabeshi kana fita a wani jarabawan kana shiga wani ne fatan Allah ya bamu ikon cin dukkannin jarabawan da zai jarabce mu amin.

Siyayya sosai yah rid ya musu ya hadasu da mota da driver aka ma yar dasu.

Nima cikin kayan lefena na dibi zannuwa da kayan shafe shafe na bayar akaiwa salma.

Sun tafi sun barni da tunanin wani kalar jarabawa zan fada kuma yanzu tunda na kubuta daga na kin da mijina yake min.

Jikina ranan a mace na wuni har sai da yah rid ya zata wani abu ke damuna ban boye mishi ba na gaya mishi damuwata dan haka nan naji zuciyata na tsinkewa.

Kwantar da hankali yayi sosai yace Allah baya taba dorawa bawanshi abinda ba zai iya ba dan haka ki kwantar da hankalinki ki yawaita addua Allah zai saukaka mana koma menene dan ba abinda yafi karfin addua.

Gyada mishi kai nayi kawai ina sauke ajiyan zuciya.

Lokaci daya kaman wanda aka mintsina ya tashi tare da kamo hannuna yace i almost forget zo ki gani.

Car park muka nufa wata mota na gani a dunkule an rufeta.

Hannu ya yaye rufin me zan gani wata shegiyar middle picano ce army green baki na bude ina kallon motan dan kam ya tafi da imanina.

Na dade ina sha'awar motan saboda kankantar ta ba karamin kyau motan ke min ba.

Key din ya kada min a gaban fuskata kallonshi kawai nake yi kaman doluwa dan na rasa me ke faruwa a nan din.

Hannuna ya kamo ya damka min key din a hannuna murmushi kwance a fuskarshi.

Kallonshi nake da mamaki da kuma alaman tambaya.

Gira ya daga min tare da sa hannunshi ya zagayo kuguna ya hade jikinmu waje daya ya sunkuyo da kanshi ya dora goshinshi kan nawa numfashin mu na gauraya.

Cikin rada yace precious ban taba son wata irin yanda nake sonki ba ke din wata jigone na rayuwata bana jin zan iya hada sonki da na wata ko wani abunke din daban ce kina da matsayi mai girma a zuciyata da rayuwata zan iya karar da duk wani abu da na mallaka dan in samo miki farin ciki.

Kullum cikin godewa Allah nake da iyayena da suka min gata suka aura min ke.

Kyawawan halayenki da kyautatawanki a gareni ya dasa kaunarki a raina.

Duk da irin muzguna miki da nake yi dai dai da rana daya baki fasa hidimta min ba.

A lokacin da nake cikin tsananin buqata baki duba halina ba kika kawo min dauki baki barni na shiga halaka ba niko me zan miki in biyaki.

Babu sai dai in kyautata miki gorgodo in kuma faranta miki kaman yanda kike faranta min a ko da yaushe.

Ni Ridwan na miki alkawarin da sanina ina cikin hayacina bazan taba kuntata miki ko in bata miki rai ba sai dai ko cikin rashin sani which we cant escape amma zanyi kokarin kiyaye hakan ma.
Chapter 23 · 0% Book details