← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 31

Sashe 7

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsawa yace i dont bloody care kawai in ganshi in na dawo sannan a gyara min part dinna ko jikin mutum ya fada mishi ya katse wayar.

Rike wayar nayi kawai a kunnena ina tunanin wannan masifan da nake shirin shiga Allah ka shiga tsakanina da bawankan nan.

Karan ringing din wayan dake kunnena ya ankarar dani da sauri na fita na kaiwa mama sannan na wuce dakinmu ina tunanin ta inda zan fara.

Halima kadai na samu a dakin tana kan system zama nayi a gefen gadona na zuba uban tagumi.

Halima ta dan juyo ta kalleni tace ke kuma fa irin wannan uban tagumi ki cigaba da sa abu a ranki kina yar karamarki da ke sai wata cuta ta kamaki shi yah rid ba asara ne da shi ba tunda ba sonki yake ba mu dai masoyanki za a bari da matsala.

Hmmmmm kawai nace har zata juya ta cigaba da abinda take yi dan ta san zurfin cikina in ban yi niyyar fadan abu ba duk nacin mutum sai dai ya kyaleni.

Nace kiji yah wai wani oha soup zan mishi ni kuma ban taba ba asali ma ban san miyan ba.

Jarfa meye kuma wani oha soup yah rid fa ba shi da dama tsakani da Allah muna kano ba kudu ba ina zamu san wani oha soup.

Ko miyan wani yare ne sai Allah duk shiru muka yi muna nazarin ta inda zamu fara.

Halima tace yauwa yammata Allah ya taimakemu we are in the 21 century where technology exist.

Na mata kallon tambaya kafin kwakwalwata ta tafi inda nata yaje da sauri na tashi na rungumeta.

Tace toh ta ina zamu fara sunan miyan zamu sa ko kuwa.

Nace ah ah mu fara da saka yoruba tribal soup mu gani nan muka typing sai gasu sun jero mana su ewedu soup,gbiri soup da sauransu amma ba oha soup.

Muka koma muka typing igbo soup nan fa muka fara cin karo da su banga soup atama soup vegetable soup ogbono soup sai ga oha soup ai nan muka sa ihu.

Halima ta copying yanda ake yi ni kuma na fara shirin zuwa kasuwa har na shirya na karbi list din ingrediant din nacewa Halima yana ga kina zaune ki tashi mu tafi mana.

Tace ke nifa tsoron shiga motan nan nake nace hmm ai baki kaini ba amma haka nake shiga dan banda yanda na iya dan Allah tashi muje.

Ta tashi ta karyar da wuya tayi kalan tausayi wai toh yana iya abin ma abin dariya aiko muka yi dariyarmu.

Munje kasuwa mun sai duk abinda muke buqata nan da nan halima har da yusra ma suka tayani muka hada mishi abincin da juices dinshi su ka kuma tayani muka gyara side dinshi.

Muna dawowa dakinmu suka turani bathroom wai in yi wanka bayan na fito ne ina zaune ina shafa mai.

Yusra tace yasin ni ban yarda yah rid da zakiyya basa son auran nan ba ji tun kafin ayi auran suka koma mata da miji kwana ne kawai basa yi tare amma duk wani hidimanta shine.

Haka itama duk wani hidimanshi itace yanzu ki duba sai kace wanda mijinta zai dawo an mishi girke girke an gyara gida anzo anyi wanka za a cancada ado ta karasa fadan haka cikin zolaya.

Ai ko na hade rai nace wallahi ba kwalliyan da zanyi ya samu daman ce min aljan da kyau.

Hakuri suka bani ai fir naki yin kwalliya kayana kawai na saka doguwar rigace budada dan momy tace bai kamata in dinga sa abu da zai matseni ba saboda budaden hips dina saboda maza ne a gidan kuma ba muharramaina ba

Sai ya kasance yawancin kayana open gown ne sai ko buba nayi sallahn la'asar muka fito babban palo inda muka sami mama da momy zaune suna hira.

Momy ce tace ah ah zakiyya ya ban ganki da kwalliya ba duk irin zuwa make up classes din nan da kuke yi.

Carab yusra tace wallahi momy ba yanda ba muyi da ita tayi kwaliya ba taki.

Momy tace maxa ki wuce kije kiyi kwalliya haba na mene.

Haka na koma nayi light make up duk da haka sai da nayi ziza.

Muna nan zaune a palon ya iso gaba na sai dukan tara tara yake gaishe da su mama yayi sannan muma muka gaisheshi ya amsa yana shan kamshi.

Sai ya kara min kyau bakin kwayan idonshi har wani walkiya yake yi fuskan nan tas ba ko gashi.

Hmmm shima yah rid din nan mai kyau ne fa yake zagin mutum dan dai kawai shi ba fari bane.

Hararata yayi kasa kasa ganin na kure shi da ido yayi kwafa a hankali.

Mama tace kai kuka kai da wa kak kwafa ya dan shafa kai yana murmushi yace mantuwa nake tunanin nayi.

Momy tace ayya yanzu dai kaje ka samu ka huta ai ka sha hanya kai dai da son tuki kake maimakon ka biyo flight.

Mama tace son wahala dai da son kudi kin san sojoji da mako kuwa.

Duk muka yi dariya har da shima ya tashi ya nufi side dinshi.

Yana shiga ya lumshe ido cikin jin dadin kamshin turare da na abincin da aka shirya mishi akan dining.

Wanka yayi ya zauna yana cin abincin yana mamakin yanda miyar ta dau zaki bayan tace ba ta iya ba.

Shegiyar yarinya ba laifi akwai tsabta da iya girki ko dan wannan ma zai aureta tana gyara mishi gida da yi mishi girki.

In ya auro shuraihat kuma sai ya baje kolin soyayyarsa da ita aljana kuma ta zama maid dinsu dan ya tabbata shuraiha ko coffee bata iya dafawa ba.

Ni kam bayan nayi sallan magrib ne ina zaune ina lazimi yah musty ya shigo yace inje yah rid na kirana.

Tuni jikina ya fara zikiri adduan dai da na saba ita na kama a bakina na nufi side din ina nanata la'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntum minal zalimin............

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 12.

HAMEEDAN HAMMA BAN IYA SUNANKI NA GAYU BA😜 WANNAN SHAFIN NAKI NE KE KADAI KINA KOKARI KINA FARKAR DA MATA ALLAH YA BAR KAUNA DA FAHIMTAN JUNA TSAKANINKI DA HAMMANKI AMEEN.

***** ****** ******

Sallama nayi a hankali na tura kofar kaman wata mara gaskiya.

Tsaye na sameshi a tsakiyan palon hannunshi da cikin aljuhu dayan kuma rike da sigari.

Damnm gabana ya fadi jin warin abin da nafi tsana dauke tsayawa nayi a bakin kofan ina dan dauke numfashi amma duk da haka ina jin warin.

Ke dan ubanki nan zaki tsaya ko ni kike nufin inzo inda kike?

Da sauri na karasa na rufe hancina cikin dabara da hijab din jikina naje na zube a gabanshi nace barka da yamma yah.

Bai amsa ba sai cewa yayi uban me kike toshewa hanci?

Da sauri nace ba komi.

Ya kalleni kaman bai yarda ba sai yace toh bude hancin ko inci ubanki.

Da sauri na sauke hannuna Allah ya taimakeni zuka daya ya karayi wa tabanya kashe a ash tray.

Sannan ya kalleni yace shegiya ke bakya kallon kanki a mirror ne?

Nace ina kallo......

Toh meye na kara wani kwalliya banda shegen kyaun da kike da shi yarinya kaman aljana, Allah daga yau na kara ganin shegen fuskankin nan kaman na mayu da kwalliya sai na watsawa fuskar acid.

Uban me kike kallona da mayun idonkin nan kaman magnet haka dazu kika wani tsareni da shegun idanunki sai na kwakulesu ya fada yana rankwashi na.

Na dafe kaina ina zubar da kwalla kuma uban me kike yi da kudi naga kina cire kudi ba kakkautawa.

Tsuru tsuru nayi na rasa me zance.

Ba dake nake ba?

Mama ce fa take sani ina cirewa ina sayan kayan kwalliya.

Kayan kwalliyan ne aka cire mishi more than hundred thousands?

Nace ah ah an min register din make up classes an kuma sai min make up kit da kuma su cosmetic din amfanina.

Kan uba wai ke nake zuwa nemanwa kudin ne da za a barnatar min da kudi a banza,wallahi sai kij biyani a sannu.

Gabana ya fadi ni dame zan biyashi kaji shi sai wani ta da jijiyoyin wuya yake dama mama tace soja akwai mako.

Kuma gobe da safe ki min kunun gyada da kosai.

Dan zaro ido nayi nace yah.....

Pap ya buge min baki yace ni kike zarowa ido kaman zaki hadiyeni da shegun idanunkin nan.

Nace ah ah fa yah gobe muna da school kuma da sassafe muke tafiya bama dawo sai 4 ga islamiya.

Oho i dont bloody care gobe ni dai inga break fast kuma lunch kawai zan daga miki kafa amma dinner kam ba abin da ya dameni da gajiyanki ke da dare ma sinasir zanci.

Na bude baki zan yi magana yace kut wai ke yaushe na dawo sa'anki ne ina magana kina yi lallai kina so inci ubanki.

Wallahi kar ki bace min da shegen fuskan nan naki kaman na aljanu a nan ki ga in ban babbalaki ba.

Da gudu na bar dakin,a daren na wanke wake na ajiye ana sallan asuba na hau aikin break fast dinshi.

Allah ya taimakeni na gama da wuri har na shirya yusra tace wannan ai daukan hakkine ki gayawa mama wallahi.

Nace barshi shi da Allahn shi yanzu in na gayawa mama sai wani abin ya billo kyalleshi ni kam.

Haka da muka dawo sallah kawai muka yi na jika shinkafa na gayawa momy ta bada akai markade kafin in dawo tace zakiyya irin wannan wahala ki bari yaci abinci da kowa yake ci mana haba in ba zai ci wannan ba ki bari ladi ta mishi kafin ki dawo nace momy ba komi.

Ko da ya dawo momy tace mishi yace in bar wahalan da nake yi haka ga karatu ga dawainiyarsa.

Momy wallahi ba yanda ban yi da ita ta bari ba wai ah ah ita dai in barta wai lada ai take samu gwara ta saba tun yanzu.

Momy ta rike baki tace oh yaran zamani ita zakiyyan ma da ake ganin kunyan ta kenan.

Muna dawowa make up school na shiga ina tausayin kaina ban gama girkin ba sai past nine.
Chapter 7 · 0% Book details